Part seven

66 5 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 13 to 14
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
  *MASARAUTAR GADANGA*
Babbar masarauta ce da ake ji da ita a fadin kasar nan suna da tarin dukiya  masarauta ce mai fada aji a fadin kasar nan,  masarauta ce mai ci kakken tarihi taci sunan *Gadanga* ne sakamakon wani sarki Abdullahi da yayi mulki a lokacin aka adda besu da yake yake aita kawo masa hari.  Sarki Abdullahi" yana da wani 'da yarima Aliyu da ake wa kirari da gadanga kusar yaki... Ganin irin harin da ake kawo masu ne da kashe masu mutane da ake ne yasa ali gadanga  shirya wani yaki ba tare da sanin kowa ba daga shi sae wasu na kusa dashi Sai mayaka ko sarki bai sanda haka ba.  Rana tsaka suka kaima makiya farmaki.. Yaki ne akayisa ka mutu ko na mutu Ali gadan ga yataka rawar gani a wnn yaki inda suka samu damar cin nasara akan makiya kuma suka kwaso sauran dake da rai suka maida su bayi.  Sanda masarauta tasamu lvr wnn  kowa yy farin  cikin wnn yanci da Ali ya kwato a wnn lokaci ne Sarki Abdullahi ya nada dan sa a matsayin sarki.     Daga nan ali yacigaba da gudanar da sarauta... Ali ya gudanar da sarauta cikin aminci da jarumtaka dan kowa shakkar farmaki yake kaimasa dan mutum ne jarumin sarki mai jinkan talakawa.. Suna son sa sosae kuma sunajin dadin mulkinsa yana share masu hawaye daga nan mai mulki ko mulki yake nema sae ya biyo ta hanyar sarki gadanga masarata ce mai cike da karfin iko ga mulki dan har gwamnati dasu take damawa.. Wann shine asalin sunan gadanga da masaratar tasamo.....
Sarki Abdurrahman shine sarki na biyar bayan gadanga... Ya gaje tane a wajen mahaifinsa  Gaddafi.  ... Bayan rasuwar sa aka nada sa a matsayin sarki sae aka hada sa Aure da diyar waziri Maryam DADA kasancewar bashida aure ita kuma tana matukar sonsa sbd miskilancin sa da yanda yake ji da sarauta tana so taga taxama sarauniya tana mulki.. Shikam yayi biyayya ne kawae ga manyan sa badan yana son Dada ba... A haka aka daura aurensa da Dada  bayan yan watanni aka nada sa a matsayin sarkin *Gadanga* sarki Abdulrahman yana gudanar da tsarin sarauta yanda ya kamata duk yanda aka so ya kara aure kinyi yayi danshi baya son yawan aure auren nan miskiline kamar me yace idan yasamu wacce ta masa zai aura..   Dada kam hakan ya mata dadi dan tafi so tayi mulki daga ita sae yayanta . Saedae me tunda taxo gidan har shekarar ta biyar bata taba ko batan wata ba kuma ta kula sarki mutum ne maison haihuwa dan magana bata cika damunsa ba...
Kwatsam sai gata tasamu ciki kowa murna yake a masarautar saeda sanda ta tashi haihuwa saeta haifi mace kuma babu rai. Hankalin ta ya dada tashi sosae.   Sau biyu tana haihuwa kuma dan babu rai ana ukkun ne ta haifi diyar ta mace "Zaliha*  a wnn lokacin ne sarki yayi wata tafiya zuwa Egypt🇪🇬  zan iya cewa anan ne ya fara jin soyayyar ya mace a karon farko da ya kalleta bayan sunyi siyayya sun shiga mota knn wasu motoci suka fara parkerwa body guard be sukazo suka bude wata motar wacce ta gaji da haduwa... Saedae wacce ta fito daga motar tafi motar haduwa.. Kyakkyawar budurwace cikin shiga ta alfarma da kaganta kaga jinin larabawa cikin takun kasai ta tashiga wajen.. Sarki yace wa hadimansa a daka ta har sae ta fito snn abi bayan ta hakan kau akayi....
Suka bi bayanta harta isa wata babbar masarauta dake cikin yanki misra... Sarki basu sha wata wahala ba aka barsu suka shiga domin ganin suma duk royal family ne.  Kai tsaye suka ga sarki batare  da bata lokaci ba sarki yace yana neman auren ta. Mahaifin ta yace Indae har ta amince yabasa saedae kuma ya tabbatar zai rike masa amana....
Sarki yasha wahala kafin ya shawo kan farha har ta fara kulasa kuma soyayya tashiga tsakanin su  Farha yarinya ce kyakkyawa ajin farko ga kamun kai da addini batare da bata lokaci ba aka saka ranar auren su ... Hankalin Dada yy mugun tashi sosae tayi hakan tabi bokan duk a banxa.... Dan babu wani abunda ya faru har Farha  tashigi cikin masarautar gadanga tafara fuskantar matsaloli dayawa wajen Dada saedae hakan baisa ta kawo mata wargi dan itama tana ji da Sarauta gata da kwar jini harda karin kuma hausa ba gama isarta tayi ba... Shekarar farha daya ta haifi diyarta mace itama aka saka mata Fatima Zarah... Hakan yayiwa Dada dadi dan bata so wani ya haifi da na miji idan ba ita ba... Saedae tana yaye zarah ta fara wani ciwo wanda aka rasa gane kanta ganin abin yaki ci yaki cinyewa ne ga bari da tayi har sau biyu yasa Baba Rashid aminin sarki bashi shawarar akan ya dauke ta daga masarautar.. Hakan kau akayi mahaifinta ma yace ta dawo Egypt kawae...
Sarki yasa aka gina mata gida na gani na fada irin na sarauta a kasar misra... Daganan kam sauki ya fara samuwa.. Ko shekara batayi ba ta samu ciki... Hakan yama sarki dadi kulawa sosae ake bama cikin.... Har ya kai wata tara  babu wanda yasani a masarautar gadanga sae mai martaba sai kuma Baba Rashid...
Ranar sarki na Nigeria aka sako ya iso masa cewa matar sa farha ta haifi dana miji.... Misalta irn farin cikin da wnn masarauta tashiga bata lokacine..
Hankalin Dada yayi matukar tashi ganin yanda sarki yake ta rawar kafa akan yaron da aka haifa bama shi kadae ba kowa dake cikin masarautar    Ana sauran kwana uku da suna farha da jaririnta da sauran tawagar su suka dawo Nigeria.. Kowa sae farin ciki yake bnd Dada da take ta yake..
Kowa yaga yaron sae ya yaba da kyawunsa dan ya hada duka kamannin mahaifin dana mahaifiyar sa.   Ranar suna yaci sunan gadanga wato Aliyu sae suke kiransa da Ammar  sunane akayi na gani na fada dan an kashe dukiya... Ammar ya taso cikin gata ga tarbiyya farha kin yarda tayi ta xauna a Nigeria dole zamanta ya koma can Egypt... Acan Ammar yacigaba da karatunsa bai ... Dada tabi duk wata hanyar da xata bi dan batar da Ammar amma abin yaki yiwuwa.... Shekarar ammar biyar Dada ta haifi walid daga nan ta kara haihuwa samira bayan samira mom din Ammar ta haifi Rahama wacce a ynx itace auta A wajen sarki.... Yaran dukkan su suna kaunar junan su basu banbanta kowa cewa wnn dan wance ne ko dan dakin mune aa duka kansu a hade yake duk da dada tana kokarin cusa ma yaranta kiyayyar yan uwansu hakan baiyiwu ba..  Dukkan karatun Ammar a misra yayi shi tun yana yaro yake sha'awar zama soldier kuma dashi ya girma kuma iyayensa sun basa goyen baya dan ya cancanci zama soldier din duba da yanda yake da jikin jarumai sann da tsabar miskilanci da kuma jinin sarauta.. Ko  shiga mutane bai cikayi ba bare magana dan shi ko yawan magana baya so... Hakan yasa wasu ke masa kallon mutun mai girman kai amma kodaya ba haka bane haka Allah yayisa gashida kwarjini... Yana gama training din sa na soja ya fito da babban matsayi.... Prince Ammar shine sunan da kowa ke kiransa mutum ne mai shiga rai kowa na sonsa ciki da wajen masarauta duk da ba a cika ganinsa ba sbd bai fiya zama a kasar ba sbd yanayin aikin sa da kuma rashin son hayaniya ko aboki bashi da shi sae wani dan uwansa a cikin masarautar kamal abokinsane na kut da kut shi kadae suke zama suyi fira idan ka cire sarki da mom dinsa.... Soyayyar da akewa Ammar a wnn masarauta ba kadan bace duk da yana da mahassada da makiya a cikin ta da suke nuna masa suna sonsa a zahiri amma a badini ba haka bane irn su Dada da sauran su dan duk wata hanya da Dada tasan zata halakar da Ammar tana binta  sbd  yandaya sarki yake sonsa kamar ransa saedae ba nasara .. Ammar ko abincin gidan baya ci Dada tasha hada sa da Mata akan ta aure su yace baya so dan shi soyayya bata birgesa ko kadan mata basa gaban sa yayinda sukuma suke binsa kamar me....
Sanda Baba Rashid ya xo ma da sarki lvrin Abba da iyalansa harda lvrin khadija da hajjo ta basa sae yaji sun burgesa yayinda tausayin khadija ya kamasa... Yaji yana sha'awar wnn family din masu karamci... Baba Rashid ne ya nemi alfarmar  yana ma Ammar kwadayin auren khadija... Sarki yaji dadin zancen da yasha fada wa Ammar akan ya nemo matar aure amma yaki
Sarki bashida shakku akan dansa dan yasan kiwane zabi ya masa zayi amanna dashi dan haka yace  da Baba Rashid da yaje ya nemawa Ammar auren ta karya nuna masa shi mai kudi ne kowani abu yaje a matsayin talakansa..  Sae akayi sa'a suka amince.. Sarki yayi farin ciki sosai dan kau ya fahimci mutane ne masu karamci kuma marasa kwadayi saeda yakira mom din Ammar ya sanar da ita tare da bata lvrn khadija tayi farin ciki sosae tare da masa fatan Alkhairi.. . shi kau gogan baisan make faruwa ba dan bama ya kasar yana Germany 🇩🇪 akan wani course da suka je yo wa sae dae kawae sarki ya kirasa ya sanar dashi ya nasa mata kuma za'a daura auren nan da wata biyu" babu abinda yace "sae Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" sarki ya katse wayar yana mmkin halin dan nasa baiko damu ba kodaya baitaba musu dashi ba.... Yayinda cikin masarauta ya dauka cewa Ammar xaiyi aure wasu na farin ciki wasu kuma bakin ciki yayinda wasu mmkin kamar prince dan sarki gaba da baya zai auri wacce ba jinin sarauta ba... Yan uwansa kam sae murna suke yayinda Dada take ta ma sarki kirafin akanme bayan ga kausar nan da take son sa (diyar kanwar ta ce da take son hada su aure)  ynx duk aji irn na Ammar a rasa wacce za'a hada sa da ita sae diyar talaka kasan dae ba sa'arsa bace... Sarki ya tabe baki kafin yace "sbd ita ba Allah ne ya hallicceta ba ko bari kiji daga yau sae yau karna sake jin wan zancen kinzomin dashi nan ya mata ta tas......

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now