Page ten

56 7 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 19⏩20
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Kiran wayar ta da akayi ne ya tashe ta daga bacci dan tsaki tayi kafin ta duba mai kiran ganin Husna ce yasa ta dauki wayar da murna take fadin "Amarya amarya" daga can bangaren husna tace "dallah can mara mutunci tun dazu inata kiran ki amma ko kidauki waya ta sbd baki damu dani ba ko har guguwar sarautar ta fara dibar ki kin manta damu.." Waro idanu tayi kafin tace "ni na isa ashe zan manta da kaina srry but  what happened to 'ur voice wani abu aka maki ne" ajiyar xuciya Husna ta sauke da har saeda Khadija ta jita can tace "wlh yaya Auwal mugune" shiru khadija tayi  can kuma ta fashe da dariya tana rufe baki kafin tace "yayan nawa me ya maki" kamar Husna zatayi kuka tace "shimana wlh bai saurara min ba bakiji ba har ynx da zafi" dariya khadija take sosae.  Husna tayi kwafa muguwa dariya ma kk mun ko zaki sani ne .. Khadija ta dan tsagaita kafin tace daga dan wnn abun kikema cema yayana mugu sbd ya maida ke mace" cikin tsiwa Husna tace "ba'a son xama macen dani namiji ce zaki gane dan abu kema ai zai zo kanki dan nakula har ynx yarima bai rike ki ba" shiru Khadija tayi. Can kuma tace abinda ma baya kasar nifa ko ganin sa bn taba yi ba" Husna tace "Allah ya dawo dake lpy zaki zo kiban lvri.   Kafin Khadija tayi wata magana ta katse wayar. . bin wayar tayi da kallo tana murmushi.. Numbern farida ta fara nema... Farida na daga wayar ta fashe da kuka... Khadija ta danne dariyar dake cinta tace "sisi meya faru.. Wani abu aka maki ne.. " cikin kuka farida tace "yo meye ma ba'a mun ba wlh nide gidan mu xan koma idan ba haka ba yaya mujaheed kashe ni zaeyi.. Khadija ta fashe da dariya harda rike ciki... Farida tace "mugawa dama baki tausayina ni ina nan sae tunaninki nake tun daxu nake son kiran ki amma ya hana ynx ma ya fita raka doctor ne Shiyasa na dauki kiranki... Waro idanu Khadija tayi tana tsagaita dariyar ta tace "me kuma ya kawo doctor ko yaji maki ciwo ne" cikin kuka da masifa farida tace "bn sani ba muguwa kawae... " dariya khadija keyi sosae har bata san lokacin da faridar ta katse wayar ba....
Da ranama tare sukayi lunch da aunty fati sae bayan ta fita ne su Rahma da saleema suka shigo suka zauna suna ta lvri tun bata sakin jikin ta har ta sake dasu dan ta fahimci su din masu son mutane ne..  Walid ne ya shigo rike da system yana ganin su Rahma da sameera ya rike haba "oh ni dan Abdurrahman naga ta kaina wato dan yaya baya nan shine kuka maida part din sa kamar naku ko... Ae ya kusa dawo wa nan da sati biyu nasa kewar wanin ku baxa'a sake gani ba"...  Rahma tace "ni wani lokacin har bana so ya dawo idan kau muna can misra ji nake kamar da gudo nan" walid yace kamar a kunnen sa." Marairaicewa tayi "dan Allah ya walid kamun rai" murmushi kawai yy yana bude system dinsa kafin yace "aunty Hanan bari na kira mummy ku ga juna tun dazu take ta kirana wae na kawo mata tana son ganin diyar ta.. Kusa da ita ya zauna kiran momy ta vedio call... Cikin ya mintuna fuskar wata kyakkyawar mata ta bayyana daka ganta kasan hutu ya ratsa ta baxaka ce ta haifi kamar sameera ba ma bare aunty fati..tace walid "where is she"  "mummy gata" ya mikawa Khadija system din karba Khadija tayi tana murmushi... Shiru mummy tayi tana dan kallon ta da wani tunani a zuciyar ta...
Muryar khadija ce ta katseta da fadin "mummy an wuni lpy" kan Khadija a kasa tayi maganar.. Mummy ta fadada murmushin da ya kara fito da kyawun ta tace "Hanan..." Khadija ta dago amma ta kasa kallon mummy.. Murmshin manya mummy tayi yarinyar ta birgeta ga kunya tana son yarinyar mai kunya... Tace "how you doing my daughter" kan Khadija kasa tace "fne mummy" mummy tace "hope all is fne" khadija ta gyada kanta tana murmushi... Mummy tace "very soon Aliyu zae dawo ki kwantar da hankalin ki ji gasu sameera suna tare dake" "to mummy nagode" "Allah ya maki albarka" daga haka sukayi sallama Rahma zatayi magana knn walid ya katse yana hararanta "ki kirata da kanki" tura baki Rahma tayi kafin ta fice daga parlorn .. Suka fashe dariya Khadija tace "wae meyasa kukewa auta hakane" walid yace "rabu da ita nima haka take mun daxu baki gani"....
Shakuwa ce ta shiga ysakanin khadija da kanne Ammar dan kowane yana kokarin faranta mata tama mance da wata Dada dan tun ranar da aka kawota ... Ynx su walid sameera da Rahma sune abokan firar ta har girki sunayi tare dan  Ce ma aunty fati tayi a bari ta rinka girkin da kanta sae ta birge aunty fati da ko aiki wani lokacin sae kaxo kaga tana taya bayin ta a gyra ko ina tsaf da ita bedroom din yarima ne kawae bata shiga rahma ko sameera ne kullum sae sun shiga sun gyar dan a yanda ta kula baya son aikin hadima... Kuma tana yin waya da yan gidan su da yan uwanta irnsu da fadila...
Kwanan ta tara su hajjo suka xo ita da Aneesa da faruk sae fadila .. Ranar murna wajen Khadija kamar me rungume su tayi.. Tama rasa abin fada masu nan da nan aka cika masu gaba da kayan motsa baki Aneesa kam yake kawae take dan zuciyar ta fal take da bakin ciki da ynx itace a wnn daular... Fadila tace "Frnd kina nan abinki nasan har kin fara mantawa damu ko" hararanta Khadija tayi.. "Ashe zan manta da kaina" faruk yace "ai ke ynx kin xama babba idanma kin manta mu ba laifin bane sae dae idan mun ganki gyara kintsi sama gyara kintsi kasa..." Hararansa tayi tana tura baki "Faruk xaka fara ko" dariya yy yana daga mata gira  hajjo tace wai ni ya bangs mijin nawa ba ki baki so na gansa" khadija tayi kasa da kanta kafin tace "ai har ynx bai dawo ba ya tafi wani course ne Germany.. " sakin baku hajjo tayi "meye kuma wa kwas shi baxae da wo ba har ynx kwana goma da aure ba sae ya dawo ya tafi da ke ba.. .  "
Kafi Khadija tace wani abu.. Rahma ta shigo da sallama... Tana ganin su hajjo ta fadada murmushin ta har kasa ta sun kuya ta gaisar da hajjo.. Hakan yawa khadija dadi.. Hajjo ta washe baki tace "sannu yan nan kina mun same ku lpy" Rahma tace "lpy qlw hajjo"hajjo tace "ashe har ynx mijin nawa bai dawo ba" murmushi Rahma tayi kafin tace "eh wlh amma rana ita yau zai dawo aikine ya rike sa" "masha Allah kice zamu dawo bude jaka knn" dariya tayi Rahma tayi snn ta gaisar da su faruk ta haye sama hajjo sae saka mata albarka take.... Sun dade a suna ta fira kafin suce zasu wuce. Nan Khadija ta bata fuska kamar zatayi kuka da kyar faruk da fadila suka lallashe ta Aneesa kam tabe baki tayi hajjo ko balbaleta da farayi... Turaruka masu yawa ta debo ta basu ta rakasu bakin kofa bayan sun tafi ta dawo jiki a sanyaye wae ynx ba hali ta bisu....
Wayar Rahma ce dake dining area ta kara ringing a karo na biyu zuwa tayi ta dauko wayar very own bro taga yana yawo a screen din wayar... Tayi dan jim kafi ta fara hawa step din da sauri a bakin ko zuka ci karo da Rahma kuma dae dae nan wayar ta katse..
Mika mata wayar tayi Rahma na dubawa ta waro idanu "na bani ya Ammar 2 missed call meya baki dauka.. " tana gama rufe baki kiran yasake shigowa.. Mikama khadija wayar tayi "aunty Hanan dan Allah kice masa ina wanka" "babu ruwana" cewar Khadija.  kamar Rahma xatayi kuka ta daga wayar tana karawa a kunne "Hello yaya good afternoon" shiru tayi  da alama magana yake... Can tace "am srry ya Ammar I was inside the toilet that's why I wasn't picked the call" a rude take maganar.... Khadija dae bedroom room ta shige...
Aneesa na komawa gida su mama da umma suka saka ta gaba suna tambayar ta ammaida khadija baiwa ko" Aneesa ta fashe da kuka "wlh umma babu wata baiwa wae kunga part din da take ma wlh duk cikin masarautar Albarka" wata kune ta tsaya masu a makoshi mama tace "To shi yariman yana sonta" "nima bn sani ba dan har ynx bae dawo ba basu taba haduwa ba" dariya sukayi "hhh bari ya dawo tayaya zae dauketa a matsayin mata ae daya dawo baiwa" ahaka dae suka dunga karyata auren khadija da prince...
ONE WEEK AFTER
A yau ko ina zaka zagawa cikin masarautar shirye shirye ake kasancewar yau yarima zae dawo kowa ya xama busy yayin da  kowa ya shiga taitayinsa..  Ko yau gyaran a kayi wa part dinsu na musamman ne. .. Sarki yasa sae hura algaita ake murnar tarar ana ta shagulgula domin yau dan gatan masarauta zaedawo bayan tafiyar wata twakas da yy zuwa kasar Germany 🇩🇪.. Su Khadija ma yau gaba dayansu suna kitchen har da aunty fati suna girki dan bayacin abincin kowa a masarautar indae har mummy batanan ko ita aunty fatin shiyasa cikin bayi babu wanda ya saka masu hannu  sae su miko masu abubuwa.. Gab da magrib suka gama komai snn aka kara gyara gidan... Bayan sun gama kowa ya fice domin yin wanka Khadija ma wankan ta shiga jikin ta a sanyaye idan ta tuna yau prince zae dawo shi koya halinsa yake oho... Sai da tayi wanka snn tayi sallah magrib bata tashi ba har sae da tayi isha'i.. Snn ta shafa mai Rahma ce ta shigo cikin shirin tayi kyau ta dauko ma Khadija kaya tace "aunty Hanan kusaka wadan nan daga haka ta fice Khadija ta bita da kallo kafin ta dauki kayan ta saka ta feshe jikin ta da turare....  Rahma ce ta shigo tana kallon ta "wow aunty Hanan wlh kinyi kyau sosae" kasa Khadija tayi da kai tana murmushi zaki fara ko Rahma" Rahma tace "wlh kau duk abinda nake fada gsky ne kina da kyau"... Karar shigowar motoci da jiniya ne yasa Rahma ta mike da sauri aunty yaya yadawo"tana gama fadin haka ta mike ta fice da sauri.. Khadija ta bita da kallo gaban ta na faduwa... Karar jiniyar duk tacika ko ina a hankali ta tashi ta xuge window yanda za ta iya hangowo... Motoci ne da yawa manya manya ga hiluxs nan kusan guda shida  ga sojoji birjit kowane cikin uniform dan ana gani sosae duk da dare ne amma da hasken futulu sai yy kamar rana... Wata mota da tafi kowace kyau aka bude kusan minti biyar naciki bai fito ba sae ya xuro kafar sa wacce take dauke da tsadadden takalmi... Babu abunda gaban khadija yake sae faduwa ta kosa yafito ta gansa a ranta tace lallai wnn  a kwai jin kai fito wa motar ma sai yaja aji.. Kafin ta gama tunanin idanun ta ya sauka a kan kyakkyawar fuskar AMMAR Yana sanye cikin T-shirt mai tambarin   fara wacce kedauke da tambarin dake nuna soldier ne dake nuna cewa ba kasar sa yake karewa ba yana aiki ne tare da hukumar kasa da kasa... Yana sanye da wando su sojoji...
Saeda ta kusa shidewa a gurin dan da ka gansa kaga jarumi mai Kwarjini   sann duk kyan su walid da Rahma da take gani Ammar ya zarta su nesa ba kusa kuma babu wanda baya kama dashi a cikin su .. Daga inda tana iya hango kyawawan fararen idanun sa  masu  pick lips dinsa da bakar madaidaiciyar sumar sa..... Walid ya basa side hug da murna sau Rahma da sameera suka rungume sa suma... Wani light smile ya saki wanda har dimple dinsa ya lotsa 😍😍
More comment more typing.. ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now