Part eleven

56 4 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 21⏩22
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Cikin kasaitaccen takunsa wanda ya nuna jarumtakar sa da kuma jinin sarauta yake yawo a jikinsa ya fara tafiya sojoji da hadimansa suna take masa baya daka gansa kaga sadauki.... Sakin labulen khadija tayi ta dawo saman gado gaban ta na faduwa da kyar take iya free ying numfashin ta.....
Direct part din maimartaba  sarki Ammar ya nufa domin kau yasan ynx ya tashi a fada.... Maimartaba naganin  dan nasa yasaki ya fadada fara'ar "barka da zuwa Aliyullah" kasa Ammar yy da kansa kafin ya duka har kasa "muryar sa can kasan makoshi yace "barka da hutawa Abie munsame ku lpy" murmushin manya Abie yy har ynx dan nasa na nan yanda yake babu abinda ya sauya daga halin sa na miskilanci sae ma abinda yy ba... Abie yace "Alhmdllh ya aiki hope an samu abinda ake so" jinjina kai Ammar yy kafin yace "Alhmdllh Abie an samu nasara"... Kafin Abie yace wani Abu kamal ya shigo da sallama har kasa ya duka ya gaisar da Abbie.. Ya kara da fadin "masu tafiya a iso lpy" jinjina kai Abie yy "masha Allah sundawo lpy" kamal ya dubi Ammar da yaki kallon inda yake.. Dariya yy kafin yace "Welcome frnd" ko kallonsa Ammar baiyi ba saema daukar tufar dake gabansa yy ya kishin gida snn ya fara ci... Dariya kamal yy kafin yace "Abbie wae fushi yake dani dan ba'ajedani tarbo sa ba kafada masa aiki ne ya mun yawa ga patience ina da ita..  Walid ne yace "zama ku shirya ne wake shiga tsakanin ku yaji kunya... Aunty fati ce tashigo da murnar ta ta rungume kanin nata ... Saida ta gama murnar ganin ta snn ta gaisar da Abbie kin amsawa yy "sai ynx kika ganni" kasa tayi da kanta tana murmushi... Ammar ne ya tashi tsam ya nufi dining.. Da sauri Abbie yace "kai ina zuwa kuma" dan marairaice fuska yy yana shafa ciki a hankali yace "Abbie yunwa"... Hararan sa Abbie yayi kafin yace "tafi can matar ka nacan nasan ta dafa maka wani" dan sosa kai Ammar yy kansa a kasa shi har ga Allah ma yama manta yana da wata mata dariya  kowa dake dakin yy harara ya sakar masu  nanda nan Rahma, sameera da walid suka hadiye dariyar su kamal da aunty fati ne kawae keyi tsaya wa yy tare da harde hannayen sa ya lumshe kyawawan idanunsa aunty fati ce ta taso zuwa inda yake ta kamo hannun sa "srry swthrt muje kaci abinci duk abinda mukasan kana so shi mukayi maka tare da Hanan.... Hanan...!  Ya maimata sunan a ransa... Kamal ne yakatsesa da fadin "su frnd fa ynx an zama manya" wata hararansa Ammar yy baidae ce komai ba... Abbie yace "kaima kar ka nemo matar ka gani very soon zan samo maka am still searching" kwalalo idanu kamal yy.. yayinda sauran suka fashe da dariya bnda Ammar da ya tabe baki.... Yayi ficewar sa Abbie ya bisa da kallo... Sallama sukayiwa Abbie snn suka biyo bayansa... Har ya kusa isa part dinsa.. Kamal yayi saurin karasawa inda yake ya rungume sa... "Miss you alot frnd am srry wlh inada patient... Ammar baice komai ba sae dae ya kama hannun kamal din yana murzawa hakan ya tabbatar masa da ya hakura.. Murmushi kawae kamal yy ba kowa ke iya ganewa halin abokin nasa ba....
Suna shiga Ammar ya haye sama dakin sa ya shiga wanda yake tsaf ko ina yana tashin kamshi  da kaga dakin kasan na dan gata ne kuma an zuba dukiya a ciki... Kayan sa ya rage snn yashiga bathroom wanka yy ya fito sanye cikin bathrobe da dab karamin towel yana tsane lallausar sumar kansa...  Saida ya gama shirinsa tsaf cikin kayan bacci sa masu taushi snn ya fito a dining ya iske dukkan kannen nasa sai aunty fati da kamal... Kusa da aunty fati ya zauna tayi serving dinsa... "Rahma je kikira Hanan nasan bata ci komai ba kuma xata iya kwanciya a haka nasani" cewar aunty fati.... Zaune ta iske khadija tayi tagumi da hannu biyu dan Kallo daya tayiwa Ammar tasan yafi karfin ta... Cire tagumin Rahma tayi "aunty tunanin me kk ki taso muci abinci tun dazu kefa ake jira..." Girgiza kai Khadija tayi "no am ok ni bacci ma zanyi idan kinshigo sae kurufe mana kofar" waro  idanu Rahma tayi "waya fada maki nan zan kwana yaya fa yaxo gani na ma wahala zai maki infact mun ma kusa tafiya misra kuma ki tashi muje muci abinci dan wlh baxa'a dauki excuse dinki ba tashi kawae muje aunty fati ce ta aiko ni" ajiyar xuciya khadija ta sauke kafin ta tashi ta dauko hijabi ta saka snn tace "to muje" dariya Rahma tayi "lallai kam su hijab manya... " harara Khadija ta bita dashi ficewa tayi Khadija tabi bayan ta gaban ta na  faduwa...  Tun kafin Khadija ta gama sauka daga saman step din kamshin daddadan turaren Ammar ya cika hancin ta gaban ta sae faduwa yake tama kasa dago kanta ta kallesu.. Kowa ya bita da ido bnda Ammar da ko dagowa baiyi ba bare ma ya nuna yasan da fito warta abincinsa kawae yake ci... Kusa da da sameera ta xauna tare dayi masu sannu.. Kamal yace amaryar mu.. Kanta a kasa tace ina wuni ya amsa mata da fara'a... Rahma tayi serving dinta... Aunty fati tace "Hanan here is ur husband" ta fada tana nuna Ammar da yanuna kamar baisan da xuwan ta ba... Gaban khadija na faduwa.. Cikin rawar murya tace "good evening" batare da ya kalleta ba yace "same" yana goge bakin sa da tissue snn ya dauko wayar sa yana latsawa... Duk basuyi mmkin yanda ya amsa ta ba saboda haka halinsa yake amma dukda haka sunji hakan da yamata bai kama ta ba dan zata ji babu dadi saedae sun dangata hakan da rashin sabo... Ita kam khadija jikin ta ne yy sanyi domin kau takula halinsa daban yake dana yan uwansa.. Dan da Alama shi yana da izza...
Kasa cin abincin ma tayi zaman gurin duk ya isheta tashi tayi tace "aunty fati am feeling sleepy.. Can i call it a day?" Gyada mata kai aunty tayi nyt sisi saeda safe" Kallon su walid tayi tace "good nyt " daga mata hannu sukayi suna kallon ta har ta haye sama... Suma basu wani jima ba kowa yayi sallama ya fice daga Ammar sae kamal aka bari.. Duban sa kamal yy "Ammar you have to change this your behavior" batare da Ammar ya kallesa ba yace "sure" dan tsaki kamal yayi "Ammar inaso ka fahimceni idan mu munsan halinka kasani ita wnn bata san ya kk ba nasan bata ji dadin yanda ka amsa gaisuwar ta kasani she's 'ur wife and part if 'ur life.. " Ammar ya kallesa da kyawawan idanun sa "ok hakora kk so na washe mata dan taji dadin raina ni ko" murmushi kamal yy manya knn ba'a son raini.. Amma Ammar... Sae kuma yayi shiru tare ta dage kafada "to ni meye nawa ma nasan nan gaba you must change dan dama shiru shiru din nan kunfi rudewa akan mace" da mmki Ammar ya kallesa  "What do you mean" dariya kamal yy yana tashi snn yace "kafini sani"daga haka ya fice .. Tabe baki Ammar yy yacigaba da danna wayar sa,... Ba'a jima ba saega khadija ta fito dan tagaji da jiran Rahma taxo tsoro kawae takeji.. zaune ta gansa a parlor yana danna wayar sa duk da ya ji fitowarta baiko kalli inda take ba... Juyawa tayi ta koma amma ta kasa shiga cik.... Ya dan dade kafin ya tashi ya hau sama... Ga mamakinsa sae ya ganta bakin kofar bedroom dinta tana gyangyadi shareta yy yai shigewar sa bedroom dinsa karar rufe kofar ne yasa tayi firgit ta farka.. Bin kofar tayi da kallo kafin ta fara sauka daga step din sae da takai na karshe taji muryar sa yace "hey" a rude ta juya.. Yace "what?" Kamar xatayi kuka tace "am afraid ina jiran Rahma ne" "come" shine abinda yace da ita jikinta na rawa ta fara takawa har ta karasa inda yake.. Bedroom dinta ya nuna mata yace "get in" kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki ta bude tashiga  ya karaso bakin kofar yana ita kuma ya haye saman gadon duk tsoran sa ya kamata ta ganin yanda ya wani hade fuska... " daga inda yake yace "sleep.. Don't let me see you out again" daga haka ya fice tare da rufe kofar" jan blanket tayi ta rufa tana matsar kwalla... Ji take dama bai dawo ba da tasan haka halinsa zai kasan ce da bata yarda ta aure sa ba.. Haka tai ta sake sake har bacci ya dauke ta....
More comments more typing.. ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now