Part Thirty two

44 2 0
                                    

Typing~~~~📱

*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)

   🌼 *Saboda* *duniya* 🌃

Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗

07051376476

Nafeesa A Guga @ wattpad

*bismillahir rahman  rahim*
Page 62 ⏩ 63

  🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Dagowa tayi suka hada idanu da Ammar harara ta banka masa tana tura baki murmushin da bai shirya ba  ya subuce mata kallon mummy yy yaga hankalin ta baya kansu yy mata alama da taci Abincin ta nuke kafada ya marairaice yana langwabar kai.. Ta dauke kai.. Waleed ya zunguro Rahma yana nuna mata dan dama itace abokiyar gulmar sa ta wani waro idanu tana Kallon yayan nata da mamaki .. Juyo wa yy suka hada idanu ya sakar mata wata harara da sauri sukayi kasa da kansu ita da Waleed suna dariya kasa kasa... Mummy ce tace "lafiyar ku" suka hadiya dariyar su suna satar kallon Ammar da yake masu wani kallo  ... Mummy ta girgiza kai dan tasan halin Rahma da waleed da gulma.. Ammar ne ya tashi ba tare da yace da kowa komai ba Ya koma parlor ya zauna yana canxa tasha duk suka bisa da kallo a hankali a hankali duk suka dawo parlorn suka zauna.. Ana ta dan labari kuma sukan saka da Khadija  shiyasa tuni ta saki jikin ta dan dama duk ta saba dasu... Ammar kau ko uffan baice ba  sun dade a wajen kafin waleed ya tashi yy masu sallama  sameera ma ta tashi "nima nayi nan.. Daga haka ta haye sama.. Khadija ta bita da kallo snn ta kalli Rahma da take bacci saman cinyar mummy  sae ta mike tace "mummy Ina zuwa.. Daga haka tabi bayan sameera Ammar ya da kallo baki sake.. Dan juyo wa tayi suka hada ido ta daga masa hannu alamar bye.. Ya waro idanu sae kuma ya langwabar mata da kai gwalo tayi masa snn ta juya ta shige dakin sameera.... Sameera  na kokarin kwanciya taga khadija ta shigo tace "to ke kuma fa" tura kofar khadija tayi tana kara shigowa cikin dakin Ta zauna saman gadon tace "bacci zanyi " cewar Khadija tana kwanciya  saman gadon.. Da murna sameera tace "yauwa dama wlh ina kewae kwana ni kadae shekaran jiya mukayi fada da Rahma nace karta kara kwanar mun nan itama tayi zuciya ta tafi babu yanda banyi da ita ba taki dawowa ... ".. Sameera ta hawo gadon itama tace "Amma baki ganin yaya ko mummy zasu yi magana ki koma" girgixa kai khadija tayi tace "aa ko daya ai har sallama nayi masu" sameera tayi dariya tace "nasan idan Rahma taga nan zaki kwana sae taxo nan kokuma taji haushi.. Dariya khadija tayi tana gyara parking din dogon gashin ta .., s
Sun dade a parlor Ammar da mummy dan tuni ta kira Rahma zuwa dakin ta dan karma tace  tare da ita zata kwana.. Ammar kau mikewa yy ganin khadija da gaske baxata sakko ba kuma mummy taki cewa komai akai sallama yy mata ya nufi dakin sa   yana shiga bedroom dinsa ya fada saman royal bed dinsa tare da lumshe idanu yana murmushi wai yau shine ya dawo gida a hankali ya furta  "khadija" tare da lumshe idanu yasan duk itace silar samun sauki a rayuwar sa ita da kamal bashi da bakin da zai gode masu ta taimaka masa snn bata guje sa ba a ya lumshe idanu yana hango kyawawar fuskar ta da shirmen ta.. A hankali ya furta "cutie".. Pillow ya janyo ya rungume yana jin babu dadi da yau zai kwana ba tare da ita ba ... Jin baxai iya ba yasa ya dauko wayayoyin su dan har tata tana hannun sa sim dinsa na nan ya saka  .. Ya fara dialing numbern sameera..
Su kam har lokacin basu kwanta ba suna ta lvri sameera na bata lvrin sch  khadija najin wani irin kewar makaranta.. Wayar sameera ce tayi kara.. Ta janyo wayar tana dubawa  da sauri ta dago tana duban khadija da ita ma itan take kallo  tace "yaya Ammar ne kekirana" da sauri khadija ta zaro idanu sae kuma taja blanket ta rufa tace "nide kice masa nayi bacci idan ya tambaye ki" sameera na dan murmushi tayi picking call din "hello yaya" "bata wayar" kallon khadija tayi kafin tace "she slept" kashe wayar taji yy ba tare da yace komai ba... Ta kalli khadija "dama kin tashi dan yace na nuna maki part dinsa" "tab babu inda zani inma fada maki" Dariya Sameera tayi "dawasa nake maki bai ce komai ba su yaya an kasa bacci swtlove bata kusa" khadija dai bata tanka ba ...
Shikam furzar da iska yy yana gyara kwanciya dan yasan karya take da wuya sameera ta barta ta kwanta ynx dan yasan kannensa da surutu... Juyi yake tayi kwata kwata ya kasa bacci  dan a ynx yariga ya saba tayaya za'ayi yy bacci ba tare da yaji dumin jikin ta ba tare da daddadan kamshin ta.. Mikewa yy tsam  ta fito part din su sameera ya nufa .. Tura kofar dakin sameera yy ya shiga  tana ganin sa ta mike  khadija ma kallon sa take da mmki .. Murya kasa kasa yace "taso muje mu kwanta" . rufe idon ta tayi kuma tai bnx dashi kamar mai bacci.. Duban sameera yy da tayi tsaye da mmkin sa yace "leave" jiki na rawa ta fita tana ji ya rufe kofar yasa key Dariya ya ce ta taso mata ta rufe bakin ta tanufi dakin Rahma.. Tana knocking ta dade kafin Rahma ta bude mata da Alama ta fara bacci.. Bata amsa tambayar da rahma take mata ba ta shige tana dariya.. "Ke kuma lpr ki zaki wani shigo mun daki har na fara bacci"..  Murya kasa kasa sameera tace "ke nan zan kwana ya Ammar ya koroni" "kamar ya" cewar Rahma  .. "Hmm kamar yanda kika ganni nan ta kwashe ta fada mata duk Abinda ya faru"..  Rahma ta waro idanu tace "bari na bama idanu Abinci shi yayan da kansa" da sauri sameera ta rikota ta rufe kofar ta saka key tace "ba ruwana"..
   Ya dade yana kallon ta  kafin yace "tashi mu tafi" ta bude idanun ta tace "dakin sameera ne fa" ya dage kafadar sa  "I don't care ai matata na biyu tashi muje ko na dauke ki da kaina... " ta gyara kwanciya "wlh kana dauka ta zan kwalawa mummy kira"... Murmushi yy ya karaso ya hau saman gadon yana fadin "ok bari naxo mu kwanta anan din" da sauri ta tashi ya janyo ta tare da rungume ta tace "wai dan Allah mene haka " "madam period fa kike just relax babu fa abinda zan maki just can't sleep without you close"... Shiru khadija tayi tana shakar kamshin sa ita kanta sae taji daban da babu shi a kusa da ita... A hankali yace "cutie" har ciki kafar ta saeda taji sunan.. Ya raba ta da jikin sa yana kallon ta murya can kasa yace "so you can sleep without me".. Kallon sa tayi taga yy wani kalan tausayi kuma shi har ga Allah da gaske yake  tayi kasa da kanta.. Yace "stop ignoring me bana jin dadi you have become part of me  koda baki jin Abinda nake ji game dake try not to stay away from me hakan baya mun dadi" wani iri khadija taji to hakan na nufin me yana sonta knn?  No tama san kila kawae feeling ne.. Ji tayi ya rungume ta so tight.. A hankali tace "ina so na koma sch" shiru kamar baxae yi magana ba dan har ma ta cire rai sae taji yace "really" tace "yes" sakin ta yy yana kallon ta kafin yace "ok amma da sharadi" da sauri tace wane sharadi" myrmushi yy tare da kamo hannunta yana murzawa  yace "Sai kin haifa mun child guda daya" kallon sa tayi sae kuma ta zare hannun sa tare da juya masa baya  ya janyo ta tare da kara rungume ta kawae sae ta fashe masa da kuka... Da sauri ya hade bakin sa da nata tsit kakeji ya kara rungume ta kafin ta saki lips dinsa ya dawo yy kissing forehead nata snn ta daura kansa a nata yace "lets sleep"...
    Shine ya riga ta tashi da asuba ya shiga toilet yayo Alwala  snn ya fito fuskar ta ya kai daedae tata  ta bude idanun ta akan kyakkyawar fuskar sa ya sakar mata murmushi tare da dan yarfa sauran ruwan hannun sa ya fice...
Tana fitowa daga wanka saka pad ta shirya snn ta dauko kayan sameera sababbi ta saka tana gama shiryawa taji ana knocking tashi tayi ta bude rahma ta gani rike da flacks tace "morning auntyn mu" murmushi khadija tayi tace "morning"  Rahma ta mika mata flacks "gashi tea din yaya yace ya wa mummy a baki ki kaimasa dakin sa" ba musu khadija ta karba tace "muje ki rakani" "sae dae na nuna maki part din" ba musu khadija ta gyada mata kai suka tafi da nufin da ta aje zata dawo kafin ya dawo ta dawo koma da saka key suna zuwa bakin part din Rahma ta juyo ita kuma ta tura da shiga gaban na faduwa.. Kallo tabi parlorn dashi ganin yanda aka kawata shi kuma an zuba dukiya kamshi ta ko ina  dining ta nufa zata aje taji ance "ba anan zaki aje ba" da sauri ta juyo gaban ta na faduwa jin gine ta gansa jikin kofa murya na rawa tace "ina" bedroom dinsa nuna mata.. Tace "kona aje maka zaka shiga dashi" "no ida ladar ki"  jiki a sanyaye ta bude inda yake nuna mata na shiga ya bi bayan ta ya shi tare da saka key harda zarewa ya saka Aljihu... Da sauri ta juyo daga inda take dan har ta aje saman wani dan dining  table dake bed room din.. Tace "fita fa zanyi" baice da ita komai ba yaje ya zauna ya sha tea dinsa har ya gama tana nan inda take.. Tasowa yy zuwa inda take ta fara ja da baya ya cafkota daukar ta yy kamar yar baby bai aje ta ko ina ba sae saman royal bed dinsa mai taushi yajata suka kwanta yana rungume da ita..
   Wajen 10 Khadija ta farka  ta ta zare jikin ta a hankali snn ta tsaya tana kallon kyakkyawar fuskar sa mai ciki da annuri sae taga yy kyau sosae fatar sa ta kara wani fresh pink lips din sa sun kara wani haska sa kamar tayi kissing dinsu har bata san iya lokacin da ta dauka ba tana kallon su sae kawai taji yace "you feel lyk kissing me ko" da sauri ta rufe fuskar ta dan taji kunya yy murmushi mai sauti  yace "don't worry it's urs come and kiss" tana kokarin sauka daga bed din  tace "Allah ya kiyaye" yayi saurin riko ta yana zagayo da hannuwan sa ta cikin ta ya rungume ta ya daura kansa saman shoulder dinta  in a whisper voice yace "fadi gsky yan mata" tana murguda baki tace "ai gskyr knn" yy cute smile dinsa yana murza wuyan ta "don't worry one day one time ke da kanki zaki nema bama saina roka ba and that will be soon" "nide ka bude mun kofa na fita" sakin ta yy tana kwantar da bayansa a gadon yace "ruwan wanka".. Da kamar ba xata tashi basai kuma ta tashi ta nufi inda take sa ran nan ne toilet din... Shima kansa abin kallo ne ruwan wanka ta hada masa da turaruka a cikin bathtube ... Juyawa tayi da sauri jin an bude an shigo.. Ammar ta gani harda su rufe kofa snn ya jingina da ita....
       Magane....
More comments more typing.... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*

✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍

SABODA DUNIYA Where stories live. Discover now