Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 30 ⏩31
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Kamal ne ya duba ta tare da bata magunguna da allura... Anan parlor ta kwanta ta samu bacci Ammar kuma ya haye sama yy wanka snn ya dawo parlour ya zauna yana kallonta... Shi mmki ma yake wae ynx shike da mata ya dan furzar da iska . tare da dafe kai yarasa gane kallon da yan uwanta da wadan da tace ba iyayen ta bane.. To su waye iyayenta ko Kuma yace mahaifiyarta ta .. Infact shi yara sa ma dalilin da yasa Abie yi masa aure shida baice yana so ... Kuma arasa wacce za'a aura masa sae karamar yarinya below twenty wnn ai rainan ta zaiyi.. Dan guntun tsaki yy kafin ya tashi ya dauko system dinsa ya dawo ya bude yana danne danne.. Lokaci lokaci yakan kalleta.. Hankali kwance take baccin Kuma da alama zazzabin ya sauka ganin yanda take ta hada zufa... Ta dade tana baccin har kusan 3:30 snn ta farka dae dae lokacin da Ammar ya fito daga wani toilet dake nan kasa yayo Alwala kallo daya tayi masa snn ta tashi tana saka hular kanta shikam nunawa yy kamar bai ganta ba Yy ficewar sa..
Wanka tayi snn tayi sallah snn ta sakko kasa domin dafa masu wani abun sbd yunwa take ji dan ynx babu abinda ke damun ta sae kafar ta...
Har tagama girkin Ammar bae dawo ba.. Dibar nata tayi taci snn snn ta kunna kallo...
Duban kausar dada tayi bayan tagama cire kayan ta na alfarma tace "kausar malam yace mun Ammar yana da tsari sosae haka ma matar sa dan haka aikin babbane" shiru kausar tayi can kuma tace "umma hakan yana nufin baxae taba sona ba kome" DADA ta dauki tufa taci sau daya snn tace "ina so kisan yanda zakiyi ki zama very close da Ammar bawae sae kin rinka nuna masa kina sonsa ba inaso kisan yanda xakiyi har yadan fara sakewa dake sae kuma kinyi da gaske dan kinsan bashi da yarda... Ni kuna daga dan zan san yanda zanyi wnn karon bama son aiki ya subu ce mana dan da matar ammarrya samu ciki ta haihu ko to tamu ta kare..." "Umma amma kinsan halinsa bashi da yarda ko kadan" cewar kausar Dada tace "nafiki sanin haka nasani waye Ammar tun yana yaro mutum ne mai murdadden hali wanda ba kowa ke iya fahimtar sa ba snn dila ne mai shegen wayo da kaifin tunani.... " "umma kin san da haka kuma kk so nasaba dashi bayan kinsan abu ne mai wuya"Dariya Dada tayi "kar ki damu idan yasan wata ai baisan wata ba abinda nakeso kawae ko bai sake dake ba kisan yanda za'ai ko part dinsa ki rinka shiga ni kuma da abinda na shirya anan" murmushi kausar tayi "dan Allah umma" umma ta gyada mata kai.. Rungume umma tayi tana murna "shiyasa nake sonki umma na" wani murmushi Dada ta saki dan wnn karon ta dauki alkawarin ammar baxai subu ce mata ba sae ta kawar dashi....
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Tunda su khadija suka bar gidan Aneesa take ta kuka umma tayi lallashin har ta gaji.. Su farida dama tuni sunbar gidan ita da husna tare da hajjo xuwa gidan hajjon... Raliya ce ta dubi Aneesar "ke kukan nan fa babu inda zai kaiki dan wlh Ammar kallo baki ishesa ba dubi fa yanda yake ai itama khadijar bata ishesa kallo ba dan gayen ya wuce da ajinta.... " cikin kuka Aneesa tace "a hakan dubi fa yanda ya damu dan kawae ta fadi" tsaki saddiqa tayi "to saeme dama xai nuna baya sonta a gidan su ne. . ai kallo daya zaki mata kisan bata jin dadin zaman gidan babu wani ciwo" "wlh kau mu zasu fake mawa da ciwo amma daga gani wahala tayi mata yawa haske kawae ta kara amma ta rame" cewar mufeeda Aneesa tace "tonide wlh ina sonsa ai da can ni aka zaba masa ba ita ba" salima ta ja tsaki snn ta fice yayinda umma ta rungume Aneesa.. Kar ki damu auta ta za'a san yanda za'ayi....🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Ammar bai dawo ba sae bayan isha'i lokacin khadija na xaune tana kallo da sallama ya shigo ciki ciki.. Itama ciki ciki ta amsa masa. Ya haye sama ya dan jima kafin ya sakko sanye da kaya marasa nauyi.. Kallon TVn yy snn ya kalle ta ganin yanda ta mayar da hankali tana kallon cartoon kamar wata kid.bama tasan ya sakko ba.. Dan tabe baki yy kafin ya xauna saman 3seater ya dauki remote ya sauya tasha zuwa labaran ball da sauri ta juyo tana kallon sa tare da marairaice murya "meyasa" kamar ba zaeyi magana ba can kuma yace "am not a kid so I can't watch cartoon" tura baki tayi tanajin kamar ta fashe da kuka dan cartoon din da take so ne tace "Amma ai narigaka ko" kafin yayi magana taji ana knocking . murguda baki tayi snn ta nufi kofa tana budewa ta daure fuska ganin kausar dan haushin ta takeji ko daya bata son ganin ta..
Murmushi kausar tayi snn tace "aunty Hanan ya jiki" fuska daure tace da sauki" kausar tace "yaya Ammar na ciki" juyowa tayi ta kalli Ammar da hankalin sa ke kan TV yama nuna kamar baisan dasu ba.. Batare da khadija tace komai ba ta juya ta bar kofar .. Kausar ta shigo khadija kuma ta haye sama.. Bin khadija tayi da kallo kafin ta karaso inda yake ta zauna saman hannun kujerar da yake kai... Tace "ya Ammar ya mai jiki" dan kallon ta yy da mmki sae kuma ya dauke kai yace "she's gud" tana murmushi tace "Allah ya kara sauki" A hankali yace "Ameen"..
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace "ya Ammar dan Allah ka rokar min aunty Hanan ta yafe mun abinda namata naga kamar tana fushi dani" da mmki ya kalleta tace "am serious ni ynx na hakura da kai tunda naga soyayya baxai yiyu a tsakanin mu ba but dan Allah ka rinka sake mun tunda kaga ni yar uwar ka ce hakan zai sa naji dadi dan Allah" surprisingly yake kallon ta can kuma yace "ok" tayi murmushi "na gode" tashi tayi zuwa dining "yaya yunwa nake ji" ta bude food flacks din taga jealoef din cus-cus yaji vegetables sae farfesun naman rago sai kamshi suke a ranta sae mmkin wnn yar yarinyar ce xata iya wnn girkin.. Ganin ba'a ci ba yasa tace "lahh ya Ammar bama kaci ba kona xubo maka" batare da ya kalleta ba ya gyada mata kai... Dadi ne yakamata ganin wae Ammar ne ke amsata badan tana gudun ya disgata ba da tare zata zubo masu... A plate ta zuba masa snn ta xuba nata tace "yaya ko nan xan kawo maka" shiru yy har ta cire ran zae tanka ta.. Sae kuma taga ya taso zuwa dining din ya xauna ta tura masa yafara ci itama ta fara ci... Suna khadija ce ta sakko dan a tunanin ta tafi... Sae deme.. Tana sakkowa idanun ta ya sauka akansu suna cin Abinci ji tayi wani abu ya tsaya mata a makoshi ba tare da tasan dalilin hakan ba shin dama suba shiri be da har zata zauna suci abinci tare.. Koma dae suna shiri aiba hurumin ta bane kuma kafin ta zuba yakamata ta tambaye ta tunda ba ita ta xuba ba... (Nikam nace tohh ji wann tsakuwar sae kace ta girmi kausar din) ji tayi kamar ta koma amma sun riga sun ganta.. Dauke kai tayi ta dauki remote tana zance tasha zuciyar ta na suya... Kausar kau hakan yamata dadi tace "aunty Hanan ko na xuba maki" ji tayi kamar ta make ta.. Trying very hard to control her self tace "no" kausar ta jinjina kai kafin ta mike tace "ya Ammar am going karda umma taga na dade Gudnyt" "nyt dear" Ammar ya fada yana mikewa shima tare da dawowa parlor tana xuwa saitin khadija tace "nyt aunty" kausar ta fada tana wani lallausan murmushi snn ta fice... Xuciyar khadija ne take bnd kuna ji take kamar ta fashe da kuka.. She try very hard to control her self amma ta kasa dan kuka kawae ke cinta.. Tashi tayi ta haye stair.. Ammar ya bita da Kallo.....
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku