Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 36⏩37
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼Cikin tsararriyar ma'aikatar su Ammar wacce tsayawa fada maku haduwarta bata lokaci ne motocin sa suka fara shigowa sojoji ne ko ta ina tunda suka ga shigowar motocin suka kame har suka tsaya da sauri aka bude masa batare da bata lokaci ba Ammar ya fito fuskar na shima kamar hadari ni kam nace to ashe daure fuskar da muke gani a gida nafila ce.. Cikin takunsa irn na jaruman maxa ya fara takawa ya kara so inda sojojin suke kara kamewa sukayi tare da saluting dinsa... Shima yy saluting dinsu snn ya nufi ciki wasu daga cikin sojojin suka rufa masa baya.. Duk inda ya wuce sara masa ake har ya isa office dinsa.nan ma wasu sojojin ne suna ganin sa suka mike tare da saluting dinsa shima yy saluting dinsu snn ya danna tum print office dinsa wanda ya gaji da haduwa ga wani kamshi hade da sanyin AC dake tashi ya bude .. Shiga yy batare da kowa ya bisa ba . Zaunawa yy tare da janyo wasu files dage gaban sa yana dubawa sae kuma ya dauko system dinsa yana wasu yan danne danne... Knocking aka masa ya bada damar shigowa wata ce ta shigo sanye cikin wasu uniform da alama na ma'aikata ne rissinawa tayi tana gaishesa ya amsa batare da ya kalleta ba ta nufi wajen da xata hada masa tea yace "no need" batare da ta kara cewa komai ba ta fice dan tasan baya son hayaniya ya cigaba da aikin da yake lokaci lokaci yakan kalli wrist watch dinsa.. bayan wani lokaci ya tashi ya fito office din ogan nasu ya nufa cikin kasai taccen takunsa a daedae wajen shiga suka cikaro Kasim..shikuma ya fito wani kallo tsana ya dinga bin Ammar dashi yayinda Ammar ya nuna kamar baisan da halittar sa a wajen ba yy shigewar sa dan shikadae keda damar shiga wajen ba tare da izini ba.. Kwafa kaseem yy snn ya fice kota kan soldiers din da suke Sara masa bai bi ba.. Ammar na shiga cikin kayataccen office din ogan nasu ya kame tare da sara masa cikin maxan taka jinjina kae A.Labib yy bayan ya mayar masa da martanin saluting dinsa snn yace "have a sit A.A" Ammar ya zauna yana fuskantar ogan nasu.. A. Labib yace "A.A we are always proud of you not only this country but allover the world kana share mana hawaye kana share na talakawa beside you sacrificed your life because of your people da zuciyar kowa irn taka ce da duniya ta zauna lpy I have no word to appreciate but thank you and i'll always pray for and wish you and your family all the best... " dan lumshe idanu Ammar yy a hankali yace "thank you sir" Murmushi A.Labib yy dan yasan bayan wnn baxae kara cewa komai ba miskilancin Ammar ba karamin kashe shi yake ba wanda wasu da yawa idan basu fahimta ba zasu dauka girman kai ne sae dae ba haka bane tsabar miskilanci ne da sarauta datake yawo a jinin jikinsa amma idan ka fahimce sa zaka gane shi mutum ne mai saukin kai da tausayin na kasa dashi... A.Labib yace "ka hadu da kaseem a waje .. " Gyada masa kai Ammar yy ya kallon ogan nasa kamar baxaiyi magana ba sae kuma yace "what brought him here" murmushi A.Labib yy dan yasan ko daya ba jituwa tsakanin su. Yace "so yake na na saka sa a tafiyar mu tagaba tunda wae kaine kayi wanda ya gabata baxae bani kunya ba and i'll be surprise You are not supposed to be the only one to be representing all the tym". Wani murmushi Ammar yy kafin yace "sir ina aiki and I want to done with them before I went home".. Gyada masa kai ogan yy.. Ammar ya mike tare da saluting din sa ta nufi hanyar fita har ya kai bakin kofa ogan yace "Ammar" tsayawa yy ba tare da ya juyo ba... Ogan yace "soon zamu zo ganin Amarya inshallah tunda bamu na akayi bikin but duk da haka say munyi biki idan Allah ya bamu sa'a in our next mission taron da zamu hada sai mu hada da taron da zamuyi a bikin ka don ace biki kamar naka ai dole duniya ta sani.. Murmushi Ammar yy snn yace "thankyou sir" daga haka ya fice....
A daedae coridor din office dinsa ya hadu da wata kyakkyawar budurwa wacce a shekaru xata kai 23.. Dauke kai Ammar yy tayi saurin cewa A.A..." Batare da ya kalleta ba ya shige office dinsa tayi saurin binsa dan tasan idan kofar ta rufe baxata samu damar ganin sa ba.. Sojojin da ke wajen suka tabe baki wani da ake kira Samuel cikin hausar da bata gama isarsa ba yace "wann mutumi ya like ma ogana yaga dan handsome ba dole yaxo yau yaxo gobe ba kwana biyu ya ber xuwa nace kila don yaga Oga yy aure ashe mayen bai hakura ba gsky Oga akwae kasuwa munci kudin yan mata saboda shi.. " dariya sukayi ishak yace "wlh idan ya jika ba ruwa na" da sauri Samuel ya rufe bakin sa yana kwalo idanu...
Xaunawa yy ya cigaba da danne dannen sa a system ta dade tana kallon sa kafin tace "A.A kamar yanda kace baka son kara gani na na dauke kafa daga zuwa inda kake because am doing what you want but naji wani rumor pls tell me that is not true.." Bai ko kalleta ba ya cigaba da abinda yake.. Ta kara sa matsowa tace "A.A shin da gaske ne kayi aure kace mun aa don Allah" wani banxan kallo ya mata kafin yace "sure da gaske ne wnn magana haka take" jitayi kamar an buga mata guduma a kai tayi baya snn ta dawo cikin daga murya tace "Ammarrr kai nawa ne ni daya wlh nason ba sonta kake ba Ammar meyasa kayi aure bayan gani mean rasa kyau ko sura ta fara juyawa Ammar dubeni fa" tabe baki yy yaci gaba da abinda yake.. Tace "nasan baka son ta"... "Inda bana son ta xan aureta" dafe kai tayi kamar wata mahaukaciya tace "karya ne kai nawa ne ni kadae yarima, zan iya yin komae akan ka kasani wlh saina halaka mutum akanka" wata tsawa ya daga mata "look Rafee'a inajin kin manta da wa kk tare ko better taje your foot out of here kafin na karairaya maki jiki and duk abinda ya samu mata ta you're to hold responsible get out my friend" wani murmushi tayi kafin tace "wlh prince babu abinda baxan yi ba akan ka kuma duk wanda ya shiga gona ta sae ya dandani fitina kuma kar kasa ran akwae wanda ya isa ya rabani da kai".tana fadin haka tafice fuuuu... Anan ta wuce su ishak suka bita da kallo Samuel yace "tunda Oga yace no let her come to me i'll say yess the girl is beautifull" wata harara ishak ya sakar masa samuel yace "Oga have fne fne ladies but why is ignoring them da nine da nasamu chance fa.. "
Tunda ta fita Amma ya dafe kansa dake masa ciwo dan baya son hayaniya wayar sa ya dauko yy ma kausar transfer din kudi ta account numbern da ta tura masa snn ya cigaba da abinda yake... Sae wajen 4 suka tashi ya fito tare da system dinsa da sauri si ishak suka mike suna saluting dinsa.. Samuel ya karbi jakar system din "Oga brk da xuwa" tallabar masa kai Ammar yy brk da fitowa ake cewa" sosa goshi Samuel yy Ammar yy gaba suka bisa a baya a hanyar sa ne suka hadu da kaseem ya kishin gida a saman wata resting chair kallo daya Ammar yy masa ya dauke kai yy gaba kaseem yace "baxan kara tsayawa ina kallo ana fifita ka a kaina ba bacin dani da kai matsayin mu daya i'll take a very good Action a kanka A.A" dakatawa Ammar yy har ya gama snn ya juyo tare da sakar masa wani murmushi ya taba hannuwan sa irn muje xuwa snn ya juya aka bude mota ya shiga.. Suka bar wajen hakan bakaramin yi wa kaseem ciwo yy ba ya tashi ya bar wajen...
...... Bai iske kowa a parlorn ba sae dae koina a gyara yake ga kamshi ta ko ina dan lumshe idanu Ammar yy yana mmkin khadija gata dae yarinya karama amma sae tsafta tunda taxo gidan bai taba ganin ta da kaxanta ba saema abinda ya karu koma koda yaushe xaka ga tana taya yan aiki aiki bata da girman kai ko daya ga kuma iya girki kallon dining din yy ganin ta jerasu a foodflacks masu kyau .. Saman ya haye sai da yy wanka ya shirya snn ya fito dakin ta ya bude kwance ya ganta saman gado tana game a wayar ta tana ganin sa sae ta tura baki tare da juya baya sar kuma ta juyo tana daure fuska tace sannu da dawowa taso basa dariya amma ya dake ya kara daure fuska yace "ki shirya zamuje ki siyi abinda kk da bukata" washe baki tayi tace "todaga nan xamu je wajen su yaya Auwal ko" baice komae ba ya fice ta bisa da harara tare da murguda baki ..
Ammar na shirin bude ma khadija mota knn saega kausar itama cikin kwalliyar ta tace "yaya ina zakuje" atakaice yace mata "shopping" ta lahh nima can zanje kawae bari na tafi tare daku taxo xata bude front seat din motar Ammar yace "go to another car" ya bude ma khadija ta shiga shima ya zagaya aka bude masa ya shige kausar ji tayi kamar ta fasa tafiyar danne zuciyar ta kawae tayi tashiga wata motar suka tafi.. Sun dan fara tafiya khadija ta dubi Ammar da idon yake a lumshe tace "yaya dan Allah muje gidan su ya Auwal" ko bude ido beyi ba bare tasa ran amsa haka ta yi shiru tana takaicin wnn hali na mijin da Allah ya bata...
Siyayya sosae kausar tayi khadija kam abu kadan ta dauka sae dogayen riguna da kayan ciye ciye wata baiwa ce ma ta daddaukar mata wasu da khadija na birgeta duk Ammar ne ya biya kudin komae hardana kausar da wasu sauran bayi.. Suna shiga mota yace "inane address din" juyowa tayi ya wani dauke kai kamar bashi yy maganar ba itama sae ta dauke kai tayi kamar bata ji sa ba kamar yanda ya mata daxu.. Ji tayi yana cewa mu wuce gida kawae... Da sauri ta juyo kamar zatayi kuka tace "to ba tunanowa nake ba" ta fada masa address din ta tabe baki yana fadawa drivern ta tura baki tana kallon window...
Gidan yaya Auwal suka fara xuwa bakaramin murnar ganin su sukayi ba tarba mai kyau aka masu with respect Ammar ya gaisa da yaya Auwal khadija sae zuba masa shagwaba take Ammar dae sai kallon ta yake husno kamar ta cinyeta dan murna kausar dae da kyar take kakalo murmushi dan ranta duk a bace yake Aneesa ma na gidan kallo daya tayi wa kausar tasan bata kauna khadija tayi wani murmushi...
Basu wani jima ba suka wuce gidan farida itama murna kamar me wnn karon ya mujaheed ya sakar mata fuska ba kamar da ba ..
Ana kiran Sallahr magrib suka iso masallaci Ammar ya wuce. Khadija na idar da sallah kausar ta shigo tana mata wani kallo... Tace "oh yau dae naji komae naji abinda aje boye mana kinxo kina wani daddare mana kai ashe dama baki da asali ashe dama uwarki mahaukac.. Bata karasa ba khadija ta sauke mata wani lafiyayyen mari tana huci da sauri kausar ta dafe wajen tace "ke kika mare ni" kanta tayi zata shako ta taji an fisgota tare da sauke mata wasu takwayen maruka wanda saeda tada wata wuta wuta.. Kamshin da taji ne ya tabbatar mata da ko waye idanun ta na hawaye tace "Ammar you slapped me?" Yace "an mare ki and if you dere repeat that nonsense i'll do it over and over again" "Ammar sbd wnn" cikin harxuka yace "say any bad word to her i'll show you how capable I am get out from here my friend and look dis should last day da zaki kara xuwa part din nan" ficewa tayi da sauri tana kuka a zuciyar ta tana tunanin hukuncin da zata dauka akan khadija dan taga Dada kamar bata da niyar daukar wani action akai..
Khadija kam fashewa tayi da matsanan cin kuma ta haye sama yace "HANAN" ko sauraren sa batayi ba ta haye sa jiki ya sanyaye yabi bayan ta....
More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku