Typing~~~~📱
*© HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*
'''(home of peace,joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)
🌼 *Saboda* *duniya* 🌃
Writing by......
<<<<≤<≤<<<<<<<<<<<<
*Annafie*💗07051376476
Nafeesa A Guga @ wattpad
*bismillahir rahman rahim*
Page 68 ⏩ 69🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
Washe gari suka shirya domin tafiya amma batare da su Rahma ba dan su tuni sun tafi.. Ita da Ammar zasu tafi ... Zaune yake a parlorn sa dake part dinsa yana latsa waya sanye yake cikin kananun kaya Blue T-shirt da white jeans.... Khadija ce ta fito sanye cikin Arabian dress tayi kyau kamar balarabiya tayi kyau sosae tunda ta fito Ammar yake kallon ta dan tayi mugun tafiya dashi mikewa yy ya kara sa inda take yana kallon ta yace "Anya xan bari kifita bazan je ni kadae ba" marairaice fuska tayi "why?"... Ya Langwabar da kai kafin yace "am jealous" da sauri ta rufe fuskar ta tana murmushi... Ji tayi ya janyo ta tare da hade bakin su dan lipstick din da tasaka ya tsotse snn ya sake ta da sauri ta taba lips dinta daji babu ta kallesa kamar zatayi kuka tace "kafa goge mun".. Ya dage gira snn yace "most you take make-up when going out Let me see it again" murguda baki tayi "what consine you" Juyowa yy yana mata wani kallo tayi saurin jada baya a tsorace... Ficewa yy batare da yace mata komai ba ta hararesa kafin tabi bayansa bata samesa a main parlor ba mummy kadae ta samu tayi mata sallama snn ta fito... Compound din duk masu aiki ne birjit da dogarai hausawa da larabawa sai gaishe ta suke.. Parkin space din ta karasa amma ta rasa wata motace yake ciki.. Hon yayi mata hakan yasa ta gane inda yake Snn ta nufa inda yake tunda ta taho yake kallon ta sae yaga ta kara masa kyau da ba lipstick din dan karamin lips dinta ya fito pink shar dashi.. Fuskar ta a hade... Tana karasowa ya dauke kai.... Har ta bude ta shiga bai kalleta ba kamar yanda ita ma bata kallesa ba yaja motar.. .. Suna hawa main road ya fara magana ba tare da ya kalleta ba yace "a week din nan zan tafi malesia a kwai wasu yan ta 'adda da zamu kama so your prayer is needed coz suna da hadari ... Idan mun samu yanda mukeso bamu wuce two weeks ba idan kuma hakan batayi yu ba sae munyi 3 weeks or may be one months..... Kallon sa tayi hankalin sa na saman titi shi kamar ma ko a jikinsa jikinta duk yayi sanyi cikin sanyin murya tace "Yan ta'adda fa kace" kallon ta yayi sau daya sann ya maida hankalinsa ga titi ... Ya kamo hannun ta yana murzawa "kwantar da hankalin ki inshallahu komai zai zo da sauki adduar kawae muke bukata" ya karashe maganar yana kallon cikin idanun ta.. Ta gyada masa kai tare da zare hannun ta tana maida hankalin ta ga titi..
Makaranta tar ba karamin birge khadija tayi ba ga kowa yana ta harkan gaban sa .. Wani office suka je mai kyau wanda ganin sa kadae abin kallo ne daga gani mai office din babbane.. Ammar ne ya fara shiga tabi sa a baya wani balarabe ne zaune yana dan rubuce rubucen sa dagowa wa yy ganin Ammar ya saki fara'a ya mike tsaye yana yana dunkula hannu alamar jinjina yace "tha great Nigerian prince your highness our king grandson .the best soldier I ever knw" murmushi Ammar yy yana mika masa hannu suka gaisa ya dubi khadija da murmushi a yace "welcome madam have a seat" khadija ta zauna tana murmushi Ammar ma ya zauna Dr. Lukman zaisa akawo masu tea .. Ammar yace abar shi dama sunxo ne a ida mata registration" Dr. Lukman ya kalli khadija snn ya kalli Ammar yace "couples know she's"... Khadija tayi kasa da kanta ga mmkin ta sai taji Ammar yace "no she's my sis" Dr lukman yace "I only knw sameera and and Rahma" Ammar ya gyada kai "yes she's my cousin sis" Dr lukman ya gyada kai snn yafara yi mata abinda ya kamata . ta kasan idanu Ammar yake kallon khadija yana ganin yanda tasaki baki tana kallon sa Da kyar yasamu ya danne dariyar sa.. Yake kawae take har aka gama abinda za'ayi dan wani irin zafi take ji a zuciyar ta wato ita ba matar sa bace ko yana kunyar cewa ita matar sa ce ne... Ana gamawa tayi ma Dr sallama Ammar ma yayi masa ta riga sa fita hakan yasa Ammar yace "I was jocking she's my wife".... Dariya lukman yayi "I know just kept quiet may you have your reason.. Or may be she's stubborn lyk my imaan" dariya Ammar yy sukayi sallama har yana cewa zai kawo masu ziyara shida matar sa imaan... A mota ya sameta ta kifa kanta tana hawaye... Da sauri ya dago ta yana tambayar ta abinda ya faru tayi bnx dashi yace "pls wife tell me what's wrong" cikin tsiwa tace "don't ever call me your wife again just be calling me your sister kamar yanda ka fada masa"... Waro idanu yayi yace "oh wai fushin da kike kenan zabga masa masa harara tayi" yace "to no different ai daka da sister na duk daya domin har yau bakin bani damar na maida ke matar tawa ba you're ignoring me is lyk you don't have any feelings on me" shiru tayi sae ynx da gane dalilin da yasa yace ita sister dinsa ce wato dan yasamu damar da zata amince dashi... Fuskar sa ya matso kusa da ita .. In a wispher voice yace "but idan kin yarda am ready na maida ke matata" ture sa tayi tana dauke kai.. Shikuma yy dariya snn ya tayar da motar suka bar makarantar...
ranar aka siyo mata duk abinda ya kamata abinda yakamata dan jibi zata fara zuwa kuma daga inda ta tsaya a Nigeria... Ranar ko daya bata yarda su tsaya su kadai ita Ammar tana cikin su mummy sae murna take..
Washe gari Dr. Lukman yaxo da matar sa imaan itama yar Nigeria jigar katsina.. Lukman ya dunga tsokanar ta wai matar yareema ita kam kunya duk ta isheta wae ya akai ya sani .. Sun sake sosae ita da imaan har tace suma zasu je masu ziyara .. Sun dan dade kafin su fara shirin tafiya ... Har balcony khadija da Ammar ta suka rako su bayan sun yi sallama da mummy .. A balcony khadija ta tsaya tana dagawa masu hannu.. Lukman ya juyo yace "to Amaryar mu sae kunxo bari nayiwa mijin ki warning a gabanki " ya dubi Ammar yace "daga yau kar ka kara cewa sister dinka ce inba haka ba wata rana sai ta kaimaka duka domin inda lura da ita lokacin kriss ya rage ta fashe.. Dariya suka fashe dashi da sauri khadija ta shige ciki....
Ammar bai juyo ba saeda ya ga fitar su.... .. Ganin bata parlor yasa ya wuce Part dinsu.. A bedroom dinsu ya same ta kwanta rubda ciki .... A hankali ya yaje ya kwanta kusa da ita tare da daura kansa saman bayan ta... Yace "kinga har lukman ya gane yanayin ki a ranar.. ".... A yanda take tace "ni fa babu wani haushi kawai nayi tunanin ban kai matsayin da zaka nunani a kace ni matar ka bace... Hannuwan sa ya daura saman nata "only a luckiest man can have you as wife you're best wife I ever see... am very proud of you so ki dena tunanin akwai inda zanji kunyar nunaki a matsayin mata ta.." Lumshe idanu tayi tana jin wani dadi har cikin ranta.....
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
Washe gari khadija ta fara zuwa makaranta tare da su Rahma suka tafi kuma Ammar ne ya kai su.. Har su sameera na tsokanar ta wai tunda suke bai taba kaisu sch ba sai yau wai dan yaga harda love dinsa...
Sosae khadija ta maida hankali akan abinda aka kowa masu sai taji kamar ma revision ne dan acan 300level din sun shiga second semester anan kuma farko....
Ana tashi motar Ammar taxo su Rahma na ganinsa suka ce "to yaya fa zai zama driver dinmu saboda ynx harda love dinsa... Hararan su tayi har suka karasa Ammar ya zuge glass din kyakkyawar fuskar sa ta bayyana Khadija ya kalla yace "shigo" zagayawa tayi shiga ya kallisu Rahma da suke Kokarin bude baya yace.. "Driver is coming to pick you" yana fadin haka ya zuge glass dinsa ya ja motar ya bar su Rahma da sakakken baki.. Sai kuma suka fashe da dariya.. Rahma tace "kinga yaya za'aje a sha love Shine ake ta ci mana magani" kafin sameera tace wani abu drivern su ya iso....
Duban sa khadija tayi snn tace meyasa baka dauko su ba yace "ba gida mukayi ba"...
Gidan lukman sukaje.. Ai kam sunji dadin ganin su aka kawo masu abinci mai raida lafiya imaan bakaramin murnar ganin khadija tayi ba.. Sun dan dade dan acan sukayi sallahr la'asar... Sannan suka taho imaan ta hada mata kayayyaki....
Daga nan maikamakon su wuce gida sai suka shiga cikin gari suka je shan ice cream Khadija tuni ta sake da Ammar tana rike da hannun sa ko ina fuskar su da ka gansu kasan suna cikin farin ciki .. Suma idan ka gansu kamar larabawan sun sha yawo har masarautar su mummy saida ya nuna mata babbar masarauta amma basu shigaba yace ba ynx ba... Har aka magrib basu dawo ba.. Wani gida ya kaita mai kyan gaske an zuba dukiya sosae dukda gidan bashi da wani girma kuma a wajajen hutawa... Ba kowa gidan sai securities da gate man... Anan sukayi sallahr mangariba da isha'i daga nan Ammar yace ta tashi suyi nafila... Raka'a biyu sukayi Ammar ya daura hannu a kanta yana kwararo addu'o'i.. Bayan sun gama ya ya janyota ya rungumeta ta lafe a jikinsa tace "wai ina ne nan ka kawo mu" ya hade fuskar su waje daya yace "gidan da zamu sha amarci ne" da sauri ta tashi zaune tana ware idanu.. Ya fashe da dariya saida yayi mai isar sa snn yace "ke wasa nake fa nida ko kaza bn siyo ba" ta rufe fuskar ta snn ta mike ta nufi kofa "nide ka taho muje ... " tashi yayi yabi bayan ta yana murmushi.. Daga nan gida suka hannun sa na cikin nata dayan kuma yana driving dashi.. Har suka isa gida...
A parlor suka iske dukkan ilahirin gidan.. Mummy tace "sannun ku masoya sai ynx aka ga damar dawowa... " kowa yy dariya khadija taji wata kunya amma ta kula su ko ajikin su...
Dukan su kadan suka ci abincin Dare dan a koshe suke ......
Ammar bai wani dade a parlor ba ya haye saman sa... Ita kam khadija saida suka gama lvri snn tabi bayansa .. Zaune ta samesa saman kujera yana danna laptop 💻 har yayi wanka ya sauya kayan sa zuwa na bacci... Itama wankan tashiga tayo ta saka kayan bacci kallon ta yy snn ya ture system din ya mika mata hannunsa alamar taxo .. Ba musu ta karasa inda yake ya daura ta saman cinyar sa yace "gobe ne tafiyar nan fa" da sauri ta kallesa tace "gobe?" Ya gyada mata kai... "Nima bn sani bafa sai daxu kinsan inza'ayi tafiya irin wnn saidae kawae kuji ane kuje.. Su shine nima ynx nagama informing wa sauran soldiers din... Jikin ta ne yayi ya kamo hannun ta "kar ki damu inshallahu zamu dawo lpy naso ace zamu rinka waya amma hakan baxaiyi yu ba dan daji zamu shiga but idan komae yaxo da sauki zamuyi waya... But ynx ki kwantar da hankalin ki tashi ki tayani hada kaya.... " jiki a sanyaye ta tashi ta bisa haka kawae taji bata so ya tafi....More comments more typing... ✍️
*#VOTE*
*#SHARE*
*#COMMENTS*✨✨✨✨
*NAFEESA A GUGA*
😍😍😍😍😍😍😍😍
YOU ARE READING
SABODA DUNIYA
RomanceLabarin yana dauke da abubuwan bn mmki.. Labarine akan wadanda duniya ta rufe masu ido sun manta Allah ne mai komai snn yana dauke da salon soyayya mai bn sha'awa.. Zai fadakar kuma ya nishadantar daku