*UMMI KWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
Fan's naso na fara" AL'ADARMU " amma hakan bazai yu ba saboda wasu matsala dana samu a labarin shiyasa na D'an jinkirta" amma yanzu ga sabon labarin danake tafe dashi" Allah ya bani ikon gamawa lafiya".
UMMI KWARAS
PG 1STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_BISMILLAHI RAHMANIR-RAHIM
******************************
👠👠👠👠👠👠👠👠👠👠👠👠______________________________________
Garin gado
12:30pmKauyen garin gado yana karkashin JIBIYA LGA, jihar katsina*** kauye ne wanda suka dogara da noma, da kuma neman na kansu ba zance kauyen akwai ni'ima ba kasantuwar a kusa da bodar nijar suke yawancin kauyukan dake kewaye da wajan sun wadatu da yawan sahara ga zafi idan lokacin rani yazo" amma sukan samu saukin hakan alokacin damuna" duk da haka suna rayuwar su mai dadi a kauyen nasu.... kauyen garin gado basu wadatu da ilimin boko ba saboda gwamnatin jihar katsina bata gina musu makarantar boko ba a wannan lokacin, dukdama iyayan yaran basu damu da karatun bokoko ba sai na muhammadiya shima Mai Anguwa ne ya gina k'aton masallaci sai ta bayan masallacin aka gina makarantar allo wanda wakilin mai anguwa Malam Muhammadu shike kula da komai na makarantar sannan babban malami ne don kaf kauyen awajansa suke koyon karatun muhammadiya" shima ya koya ne ta sanadin mahaifinshi wanda ya turashi Borno yayi makarantar Allo" Malam Muhammadu kwarai shi ya fara kawo canji a kaf kauyen nasu ta fannin Addini, shi ne limamin kauyen nasu, Garin gado basuda wutar lantarki (NEPA) kuma sannan basuda ruwan fanfo amma ako wacce safiya 'yan mata da samarin kauyen suna daukan langa da tulu su tafi rafin garin domin samun ruwa wanda yake cen nesa dasu kadan ta bayan garin.
A ko wacce ranar LAHADI , dattawa maza da mata, samari da 'yan matan kauyen, yara yara suna barin kauyen su tafi cin kasuwa a garin jibiya, sai yamma ko ince sai dare suke dawowa.
Kauyen nasu yana dauke da mai anguwa" amma babu mai gari saboda karamin kauye ne, mahaifin Ummi " shine Malam Muhammadu shine wakilin Mai Anguwa kuma shine limamin garin gado" wanda ko babu mai anguwa shi ake samu domin shawarwari" Mal. Muhammadu shi babban amini ne ga mai anguwa kuma suna matukar kauyautata wa junansu.
Wannan gajeran labari ne game da garin gado.************************************
Gidan Mal. Muhammadu matsakaicin gida ne ginin laka, ta kofan shiga gidan akwai soro wanda yake dauke da dakuna biyu dakin mai gidan da kuma dakin baki, idan ka shiga ciki kuma d'akuna uku ne a kewaye sai tsakiyar tsakar gida ne da kuma kitchen wanda akayi kaman bukkan Fulani" sai wasu d'akuna guda biyu da suka kalli yamma hade da barandar su, cen karshen gidan zakaga wajan kiwo ne garken shanu dana raguna da tunkiya, sai kajin hausa, agwagwa da talo-talo, ta gefen wajan kuma ban daki ne har guda biyu ajere.Mal. Muhammadu yana zaune da mahaifiyar sa, sannan shida iyalansa mata daya(Mama) da yara mata guda biyu Mairo da "Ummi" sai kaninsa wanda ake kiransa da kawo Shafi'u" yana da mata daya da yara 'yan biyu" Halilu da Harira...Mal. Muhammadu su biyu ne awajan mahaifiyar tasu mai suna Salamatu amma anfi kiranta da "Mai gidan dawa" sunan tsohuwar yasamu asali ne tun mai gidanta na raye".
DU LIEST GERADE
UMMI KWARAS ✔
KurzgeschichtenLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...