04

73 5 0
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 4

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Baba ya ce, "Ummi a haka za'ayi karatun? na gyaɗa kai na kara langwaɓewa a jikin sa ina zumɓure baki har dai lokaci ya ɗan ja, Baba ya sake ce wa,"Ummi kin tsaida ni ban tafi ba kuma ke ba ki tashi kin shiga ajin naku ba"
Na ta shi zaune daga kwancen da nayi sannan na saki fuska ta na kalli Baba da mamaki sai kuma na sake tsuke fuskar" kamar dai mai shirin yin kuka  Baba ya ce,"Ummi lafiya kuwa, ya akayi kuma?
Na ce,"Baba dama ba tare zamu shi ga ajin ba, ni gaskiya sai da kai zan shiga saboda Abulle tace in baka iya karatu ba duka ake ni kam bani son duka Baba"
Baba da yanzu ya fara gajiya da rarrashi na sai na ga ya dafe kan sa ya girgiza kai na yi saurin  ce wa,"Baba ciwon kai ka keyi ne" "magana fa ni keyi kamin shuru ni wallahi ka taso mu shiga tare"

Na soma jan Baba har mun kusa shiga ajin da naga don dazon yara sa'anni na suna ta faman yin karatu da turanci wanda ba zaka gane me suke faɗa ba, da sauri na ja da baya ina sallallami ganin cikan da ajin yayi na ce," Baba ahaka za muyi karatun wai?
Baba ya ce," Ummi shiga ki samu waje ki zauna bari na je ofishin "Office ɗin" Headmaster yanzu zan dawo kinji" Ban mishi musu ba amma sai na tsaya na ki shiga ciki na tsaya ne awajan ina kallonshi yana tafiya har ya shiga ofishin Headmaster ɗin sai na juya ina sake kallon cikin ajin ina taɓe baki ina tunanin ta ina zan iya zama acikin waɗannan yaran wasu ma kayan makarantar su babu wanki duk yayi datti rigar ta dafe kamar dai ba farin kala ba, da yake farin riga da wando mai kalar ruwan bishiyar bedi muke sawa sai farin hijabi karama wanda mata ne ke sanya wannan,  gashi yawan cin yaran maza da mata a kasa suka zazzauna kalilan ne suke zaune saman wani kujera doguwa ta katako wanda bai wuci guda bakwai ba, na kai duba na ga "Tagar ajin" guda hudu ne amma ko wani taga yana ɗauke da ɗalibai biyar-biyar maza da mata sosai abin ya ban mamaki to a ina ma zan zauna ko ina a cike yake da yara na kara rike robar abinci na na gyara tsayuwa ina jin yadda suke karatu suna ihu malamar da take ajin itama ihun take yi acikin raina nace wai dama haka ake koyan turancin don ni duk a zato na turanci kaɗai ake zuwa koyo a makaranta, na wai ga ina so na ga ko Baba ya fito don na gaji da tsayuwa sai naga bai fito ba hakan yasa na sauka daga kan matakalar ajin namu kai tsaye ofishin na shiga ina ce wa, "Baba ina ta jiran ka ne fa kuma ka barni a tsaye kazo muje ka nema mana wajan zama saboda babu wajan zama a jin na karashe maganar ina kallon lungu da sakon ofishin wanda naga daga shi Headmaster ɗin sai wani mutumi da yake zaune a wata kujerar da take kallon teburin Headmaster ɗin ban ga fuskar tashi ba saboda bai juyo ya kalle ni ba hankalin shi na kan wayar salula da naga yana ta faman latsawa"

Headmaster ya katse min tunani da na ke yi wanda yasa hankali na koma wa wajan sa " tsawa ya daka min akan waya ce na shigo" na tura baki gaba ina kara dubawa ko zanga Baba don ni hargagin sa bai dame ni ba so na ke na hango Baba na saboda na yi kuka na da shagwaɓa ta da kyau amma wayam babu Baba babu alamar sa fita nayi da gudu zuwa waje naga babu mashin ɗin daya kawo mu turkashi ai komawa nayi ofishin ina murza idanuwa da hannu na soma shash-shekar kuka Headmaster ɗin ya sake duba na ya ce," ya akayi ne maza ki tafi ajin ku" Baban ki ya tafi sai an tashi zai dawo"

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now