02

102 5 0
                                    


*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 2

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Baba da Ummi suna zaune ne dama a ƙofar barandar Mama Ummi na kwance saman ƙafar Baba yana rarrashin ta akan tayi haƙuri amma Ummi ta ki yin shuru, ganin Ummin sa shalelen sa ta ki yin shuru sai ya tada ita suka fita cikin daren nan basu jima ba suka dawo sai ga Ummi anyi shuru ja'ira ta langwaɓe a jikin Baba sai faman shagwaɓa ta ke yi ashe tsiren naira ɗari Baba ya siya mata

Ɗakin Mama suka shiga anan suka tarar da Mama akan katifar ta sai Mairo da take zaune gefen Mama, Mairo na riƙe da alƙalami da tawadar ta tana rubutu a Allon ta".

Ummi ta taka ahankali ta wuce cen k'uryar gadon k'arfen Mama kasantuwar dama asaman gadon shillon Mama take kwana, to a ƙasan gadon ta zauna, ta bude ledar tsire ta soma ci tana kallon yadda Mairo ta zuba mata idanu amma hakan baisa ta samma ta tsiren ba ta na jin Baba yana yiwa Mama fada yace", Maman Ummi__da yake Baba baya iya kiran Mama da sunan ta sai dai yace *Maman Ummi* Baba yace", ku dena aiken yarinyar nan waje mai nisa tun da kun ga idan a ka aike ta cewa ta ke yi ta gaji kuma idan kun aike ta ku ka ga ta jima bata dawo ba sai ku bi ta kuga ko lafiya yanzu ga shi wannan yaran Kamale shi ya rike ta har wanki yasa tai masa kuma ya kwace mata kuɗin hannun ta wannan ai rashin mutunci ne suna ganin karamar yarinya ce ba wayau gareta ba zasu iya cutar da ita Don Allaah Maman Ummi a ki ya ye gaba kuma a kula don Allah". Tun da ya fara maganar shi Mama bata ɗago tace mashi uffan ba har ya ga ma zai fita yace", A kawo min abinci dakina", Sai a sannan Mama ta buɗe baki tace "Toh"

Baba yana fita Ummi na gama cin tsiren ta hakan kuma yayi daidai da jin saukar ranƙwashi a kanta, Mairo tace", Bana hanaki samin takalmi ba ? na hanaki ɗaukar min ƙaya ko ban ha na ki ba ? Ummi fa ta ji zafin ranƙwashin, ta buɗe baki kenan za ta yi kuka suka hada ido da Mama sai ta sunne kanta amma hakan bai ha nata hararar Mairo ba harda yi mata gwaliyo bayan Mama ta fita ne suka soma yin cacar baki kaman za su yi dambe wanda idan kaga yadda Ummi ta ke yi kamar ita ce babba kuma fa idan aka barta sai Mairo tai mata dukan tsiya ba za ta iya taɓuka komai ba Ummi irin yaran nan ne masu neman tsokana da iya sharri idan aka zo wajan dambe kuwa guduwa suke basa iya yin komai amma fa ta iya kissa kala-kala wanda idan tai maka sai ya sanya ka kuka wallahi",

Mama na dawowa ɗaki Ummi ta yi shuru kamar munafuka ta haye saman gadon shillon Mama tana kallon Mairo tana shillo ahankali tana kuma yi wa Mairo gwaliyo", ita fa in aka barta dadin ta ta ke ji a wannan lokacin ta tuna tayi yawo son ranta taci ta soyu da kuɗin kukar Mama sannan ta sha ƙanya gashi ta dawo Baba ya siya mata tsire tsabagen wani farin ciki da jin dadi ne yasa tayi ihu da ƙarfi ta ce sai ni *UMMI ƘWARAS* harda tafa hannuwa wallahi ba tasan tayi ba sai dai kawai ta ga su Mama sun zuba mata ido suna kallon ta sosai ta tsargu da kallon tayi rau rau da manyan idanuwan ta sannan ta juya baya ta kwanta tana jin su suna hira amma ba ta iya sanya musu baki ba saboda ta san Mama na fushi da ita tace",cikin zuciyar ta Mama ai nasan gobe zaki sakko hmm in ma baki sakko ba Ina miki magana zaki amsa ni tana ta tunani barkatai idan tayi gabas tayi yamma a haka har bacci ya dauke ta.
______________________________________

UMMI KWARAS ✔Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin