*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 34STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
Mai Anguwa ne da zuri'ar sa kacokam suka shigo tsakar gidan mu, fuskokinsu duk babu fara'a, babu anashuwa.
Abulle ta zauna gefen Ummi ƙwaras, yayin da kowa ya nemi gu ya zauna, ban da Mummy ita da Ɗan ta Umar suka nemi waje suka zauna cen ta wajan bukkan kitchen ɗin mu.
Na fara ba da labari kamar haka:
SHEKARU SHIDDA DA SUKA WUCE
Attached page 17 nd page 34
LABARI
Har ga Allah ban yi wannan abin don cutarwa ba, kawai dai na guje ma Yaya Umar ne saboda kar ya dame ni da surutu, don yana son shishshige min, Bayan fitan mu da minti Arba'in da biyar, mun siyo maganin har nasha a hanya, da yake a kafa muka je muna yi muna hira har muka dawo gida ina shiga falon naji gabana ya yanke ya faɗi, duk da ban ga abin faɗuwar gaba a falon ba, amma kuma babu Yaya Umar saboda tun daga waje na gane ya tafi kasancewar ban ga motar tashi ba a filin da ake aje motoci" da alama ya bar gidan, nayi wata hamdala ina murna na shiga gidan cike da zumuɗin yin magana da Abulle don nayi niyar bata labarin dukkan abin da Yaya Umar yake min a yau ɗin.Na karasa cikin ɗakin "Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un"
Abin da idanuwana suka gani shine ya sanya na fara jin jiri wanda da taimakon bangon ɗakin na jingina jiki na, babu abin da yake fita daga baki na sai salati, idanuwa na ba shiri yau suka soma zubar da hawaye sosai, Ni mai taurin zuciya sai gashi yau zuciyata na dukan uku uku ina ji kamar zata fashe ta fito waje tsabar tashin hankali.Na ɗan tsagaita kuka yaci karfi na, Ina tsakiyar su Ɗan binni da Mamie sai Mai dawa a baya na, S.Chubaɗo ya ciro wankakken handkey ya share min kwallar da take zubo min yana tapping baya na alamar in yi shiru.
Na cigaba da cewa,"Ina kuka ne saboda ganin halin da ƴar uwa ta Abulle take ciki, Fyaɗe yayi mata, duk da karancin shekaru irin namu, tun da ba mu wuce goma sha biyar zuwa sha shidda ba, Mun ci kuka sosai kafin muka ta shi na taimaka mata na kai ta ban ɗaki, na zuba ruwan zafi na sirka sannan na ce ta zauna, fita nayi a bayan gidan saboda ina jin zafin kukan da take yi, Ni kuma ina gyara ɗakin ina kuka, zuciya ta na yimin quna, har na gyara komai tsab yadda babu wanda zai gane abin da ya faru a ɗakin, kayan da suka bace na wanke su na fita waje na shanya su na dawo na sanya turaren wuta na koma bayan gidan na taimaka mata muka dawo ɗaki, na bata wani kaya ta sanya sannan ta kwanta ina jin ta, kuka take tayi sosai har cikin ranta, tausayin ta shi ya hanani ce mata komai illa nima dai hawayen kawai ke zuba a idanuwa na.
Mun jima a wannan halin kafin su Aunty Mairo suka dawo gidan, hakan ya bata damar yin lamo alamar rashin lafiya ni kuma na tashi nai musu sannu da dawowa, don in rike sirrin ƴar uwa ta...faran faran da sake fuskar da nayi shiyasa duk su Yaya Mahmud basu fahimci abin da ke faruwa ba, bugu da kari munji cewa an nemi Umar an rasa don nayi niyar tona mishi asiri.
Haka muka dawo Garin gado hutun mu ya kare muka koma makaranta, duk da Abulle ta zama kamar bata magana, ta dena hira, ta dena sakewa da kowa har ni karan kai na ba wata hira mu keyi ba, sai na lura ko da muka koma makaranta bata bama kowa attention ɗin ta sai nasa aka dawo dani ɗakin su wanda ga gado na ga nata, da kyar na shawo kan ta ta fara sakewa da ni, ta fara mai da hankali a aji, ta kuma fara yin hira kaɗan kaɗan.
Kalu balen da muka fuskanta a faruwar wannan al'amari shine rashin ganin period ɗinta na tsahon watanni uku, Duk dama ba muyi tsammanin ciki ya shiga ba, Ni na rinka kwantar mata da hankali har term ya kusan karewa muka fara jarabawa.
Lokacin da muka fara jarabawa sai Abulle ta samo saran bacci hakanan muna zaune muna hira sai ta fara gyangyaɗin bacci, muna library muna karatu sai ta fara bacci, idan mun dawo ɗaki ta fara bacci komai dai bacci. Wasu daga cikin kawayen mu suka fara taokanar ta wai sleeping sickness, kwata kwata ba muyi tunanin komai ba a ran mu, har muka tafi hutun gida.Anyi anyi mu je katsina hutu amma sam muka ki zuwa, kasancewar Abulle ba macce mai jiki bace asalima babu wani canji a tare da jikin ta da har za'ayi tunanin wani abu, mu kayi hutun wata ɗaya muka koma makaranta.
To a wannan komawar ne nake tambayar Abulle yaushe rabon da taga al'adar ta, kuka ta farayi duk dama ni da ita bamu sani ba ko hasashen mu gaskiya ne kar ace ciki take da shi, sai muka nemi pass da kyar aka bar mu, muna fita daga cikin makarantar asibitin hayin gada muka je ni da Abulle, muka biya kuɗin test a kayi mana PREGNANCY TEST.
Muna zaune saman benci Abulle na kwance saman cinyoyi na tana sana'ar bacci, aka kawo mana takarddar test ɗin.
Ni na buɗe na fara karantawa ban san lokacin dana zame kasa ba take hawaye suka fara tseren fitowa daga kwarmin idanu na,jiki na rawa, murya na rawa nake kirin sunan Abulle,Abulle na da cikin wata huɗu duk bamu sani ba.
tana tashi taga abin da ke cikin takardar kawai ta faɗi kasa.
Tun daga wannan ranar bamu sake komawa makaranta ba.Mun haɗu da wata tsohuwa, hakanan kawai wanda take cen kauyen dake kusa da asibitin ɗan ɗauri na cikin garin jibia, ita ta bamu wajan kwana, ci da sha, da duk abin da muke bukata.
Karya mu kayi mata shiyasa ta taimaka mana, Ummi tace Mama kun san ni da iya karya wallahi ban yi tsammanin matar zata saurare mu har ta taimaka mana ba.
Dalilin kin komawa makaranta kuwa, da zaran an fahimci Abulle na da ciki to kashin ta ya bushe, bama iya student ba har ta principal sai ya ci mata mutunci, ya sa akira iyayen ta kuma a yaɗa labarai na karya, sannan daga karshe a kore ta daga makarantar....Kada kuga laifi na don na bada shawaran mu gudu, Hakika bana son hankulan ku ya tashi.
Mun cigaba da zama a gidan matar tsahon watanni biyar. Abulle ta na shiga watan haihuwa, matan tai ta taimaka mana da ruwan addu'a na masu ciki, Allah cikin ikon sa Allah ya sauke ta lafiya, ta haifi Ɗa namiji kyakkyawa, Abulle ta raɗa masa suna Muhammad Aarif sunan Baban mu...Ni ke rainon Aarif sosai nake kula da shi ita ma ina bata kulawa yan da ya kamata.
Saura mata kwana biyar tayi arba'in Allah yayi wa tsohuwar nan rasuwa kuma gashi makwaɓtanta kawai muka sani, su suke ta shigowa ma, muke karbar gaisuwar, bayan kwana bakwai muka tattara komatsan mu muka tashi komawa in da muka fi wayo wato KAUYEN GARIN GADO.
______________________________________
STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE
KAMU SEDANG MEMBACA
UMMI KWARAS ✔
Cerita PendekLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...