*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 21STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
BAUCHI STATE
GRAFarka wa nayi na ganni kwance a wani katafaren daki wanda ba zan iya cewa ga bangaren da nike ba, Aarif na gefe na yana rike da hannu na guda daya, yana murnar na farfado a daidai lokacin da aka murda handle din kofa aka shigo, Mamie ce take tahowa kai tsaye zuwa in da nike hannayen ta na rike da tray babba tana cewa,"kin farfado Ummi Sannu ko.
Na gyada kai a daidai lokacin da na tashi na zauna Ina kokarin sanya kafafuwa na a kasa ni agani na bai kamata na kwanta a wannan luntsumeman gadon mai kama da gadon sarauta.
Mamie ta ce,"No ki mai da kafar ki, ki zauna comfortable, ta fada tana Mai sauke tray din, Ta na cewa," Ki dan ci wani abu ko kyaji karfin jikin ki, ta koma gefe ta janyo Aarif tana wasa da shi tana cewa,"To yanzu dai Ummin ka ta farfado ko babu sauran kuka ko"
Aarif yayi yar dariya irin ta su ta yara yana cewa,"Mamie ball dina ya fada cen gidan Ina wasa a garden dinki dazu"
Mamie ta ce,"Really, you mean ya fada hotel dinnan, Aarif ya gyada kai alamar "Eh" Mamie Ta ce,"To bari za'a siya maka wani sabon ball kawai"
No Mamie ni wancen ball din ni ke so, Ummi na ta na yawan cewa babu kyau yawan kashe kudi.
Mamie ta jinjina kai yayin da take kallon Aarif tana kuma kallon Ummi, she can't believe that Wai ashe Ummi ita ce yarinyar da ta jima tana nema bata sani ba, Ta tura Aarif parlor ta dawo kusa da Ummi ta zauna ta rike hannayen ta biyu tana cewa," Ummi zan fara da godewa Allah da ya sa na gane kece yarinyar da Sadeeq ya jima yana bani labarin ta.
Na zare idanu Ina tambayar ya akayi ta San hakan?
Mamie ta murmusa da murmushin ta na kasaita Ta ce,"A gaban idanuna kika suma Ummi daidai na shigo dakin don in duba ko al'amura suna tafiya daidai, sai na ji kina kiran sunan Sadeeq *Dan binni* Tabbas
na san sunan a bakin Sadeeq, shiyasa reaction dinki kuma shi yayi min dukkan wani explanation da ni ke bukata,
Mamie ta daura da cewa,"Ko ba kece SALAMATU ba?, Na gyada kai ina kara mamakin yanda al'amarin ya kasance.Mamie ta cigaba da cewa," Amma kafin na karaso cikin dakin, kin fadi kin suma, sannan tun daga lokacin da Sadeeq yaji muryar ki muka ga yana ta faman waige waige In fact for the first time da naga yau Sadeeq ya sauka daga kan keken sa yana kokarin zuwa in da kike, Ummi warakar Sadeeq yana tare da ke idan har kin bani hadin kai, zan baki labarin rashin lafiyar sa tun daga farko har zuwa yau.
Ban san lokacin da guntun hawaye suka fara tsere a idanuwa na ba, wai dama ashe zan sake ganin *S.CHUBADO* Mamie na cewa ki dena kuka,
"Ina cewa uhm uhm Mamie barni kukan jin dadi ne,Mamie kukan farin ciki ne, Mamie taimaka ki kai ni wajan Sadeeq don Allah.
Muna zuwa sashensa na iske sadeeq dina, Dan binni na kwance saman sofa ya lumshe idanuwa kamar a kira sunan sa ya amsa, ga Abba a gefen sa yana matsa masa hannu ita kanta yau Mamie ta rasa ya a kayi Abba ya dawo cikin hayyacin sa.

BẠN ĐANG ĐỌC
UMMI KWARAS ✔
Truyện NgắnLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...