*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 33STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
HARGITSIN RANA ƊAYA, RANAR SALLAH"Kisa zakayi ko, Bari ni na fara kashe ka ta faɗa yayin da take kwaɗa masa taɓarya a kafar sa guda ɗaya, kuma da karfin da Allah ya bata, zata kuma wani ne aka rirrike ta ana cewa,
Haba ABULLE miye haka?," Zaki raunata shi fa, cewar Babban wan su.
Cikin muryar kuka take cewa,"Gwara na raunata shi, ku barni na karasa shi don Allah, Baba shine wallahi shineeee kuka ne yaci karfin ta wanda ta durkushe da gwiwoyin ta biyu, tana mai rufe fuskar ta, kuka take mai tsuma zuciya.
Duk dama basu san me ya faru ba, basu san dalilin kukan ta ba, amma sai suka tausaya mata suna mai bata hakuri duk a tunanin su tana mi shi hukunci ne sanadiyar cin zarafin kawarta da yayi.
Sai dai kash, basu ɗauko zancen daidai ba, bari mu cigaba da kasa kunne musha labari.
Ihun da ya sake saki na biyu shi ya dawo dasu daga hakurin da suke bai wa Abulle, gaba ɗaya suka tafi wajan Umar wanda yake kwance ya rike kafar sa ta dama yana ta faman ihu.
Mummy tayi gun ɗanta wanda shakka babu ba karamin bugu Abulle tayi masa ba, ji yake yi kamar jijiyoyin kafar tasa guda sun dena aiki kamar ma dai ba ajikin sa kafar take ba, sai zugi da raɗaɗi da ya biyo baya wanda hakan ne ya sanya shi kurma wata kara daga nan kuma ya faɗi kasa sumamme.
Daddy ya nuna yana son kai Ɗan sa asibiti, amma ina Mai Anguwa ya hana, Abulle ta fita waje da gudu taga hadari na shirin haɗuwa, ruwa ta ɗebo cikin wata roba babba ta shigo da shi ta sheka wa Umar.
A firgice, cike da raza na ya tashi yana ihu wayyo Allah na Mummy mutuwa wallahi mutuwa na gani ku taimake ni Daddy.
Umar ya rinka wasu abu kamar zararre sai da Mummy ta lallaɓa shi ita ta zauna kusa da shi tun da an hanasu fita daga garin...Abulle ta ce kaɗan ma ka gani daga wallahi.
Bayan kamar minti arba'in da faruwar hakan, ruwan sama ya sauko, wannan ne ya basu damar zama ɗakin Umma sannan Abulle ta basu labarin komai da yadda abin ya kasance.
Mai Anguwa ne yake ta safa da marwa daga bakin kofar ɗakin zuwa karshen bangon ɗakin, da alama ranshi yayi dubu ya baci, Abulle ne tazo masu da sabon zance wanda kunnuwan su ma ya kasa ɗauka balle gangar jikin su.
Ɗakin yayi shiru na tsahon minti arba'in ko tari ba kaji balle motsi tsabagen zuciyar kowa tafarfasa ta keyi da wannan labarin na ABULLE....kowa dai ran shi ya jagule, babu mai yima ɗan uwan sa magana....Zunnu ne bawan Allah da tausayin Abulle ya kama shi.
Toh fah bari mu leka gidan su UMMI ƘWARAS muga wainar da ake toya wa.....kafin muji abin da ke faruwa anan ɗin.
Misalin karfe ɗaya da rabi Baba ya umarci dukka mazan da suje suyi sallah sai su dawo.

ESTÁS LEYENDO
UMMI KWARAS ✔
Historia CortaLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...