*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 26STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
BAUCHI STATE
GRAUmar ya zare idanu yana cewa,"Wani irin aiki ne wannan da kike ikirarin zaki bani abubuwa haka?.
Shu'uma Shatou tayi murmushi ta ce,"Kaje kayi tunani, idan na gama tsarawa zan sanar da kai, kar ka manta daga karshe zaka iya samun Ummi da Ɗan ka Aarif a garabasar aikin daka yi.
Tana kai wa nan ta tashi ta shiga gida, ta barshi zaune cike da tarun maganganu a cikin ransa, Umar ya koma hotel yana ta faman dialing number Mike amma bata shiga.
After 1 week
Tsahon sati kenan da maganar su da Shatou, yana ta kiran layin Mike baya samun sa, dama dan ya fara sanar dashi abun da ke faruwa kafin yayi moving...ana haka Umar ya yanke shawaran yin aiki tare da Shatou ba tare da ya samu amincewar abokin nasa ba.....and ya samu Shatou har sun tattauna akan maganar wanda har sun gama tsare tsaren yadda al'amarin nasu zai kasance.An ɗau kusan wata uku ana abu ɗaya basu samu cikar burin na su ba,zamu iya cewa suna nan suna tsara muguntar tasu....A wannan lokacin ni kuma Ummi na gama rubuta jarabawar waec da neco abin farin ciki ma shine naci jamb na samu maki ɗari biyu da ashirin wanda ban yi tsammanin samun makin nan ba, hakan yasa Ɗan binni yayi min kyautar waya android phone, for the first time dana taba rike waya a rayuwa ta wayar ma iphone wayar da naga ana ta yayin ta, wayar da sai ƴaƴan wane da wane suke rike ta yau itace wai a hannu na.
Abin da ban sani ba ashe Mamie ta gama tsarawa akan da zarar Abba ya dawo daga tafiyar daya sake yi, gaba dayan mu zamu tafi katsina ban san komai a kai ba sai ana gobe Abba zai dawo ina zaune a garden ina yanka fruits, Aarif na gefe na yana wasa, Yaya Sadeeq na zaune kasa saman carpet ya tsura min kyawawan idanuwan sa yana kallo na kamar zai cinye ni.
Na rufe idanuwa na ina cewa,"Haba mana yaya na wai tun kana kallon kyau na har sai ka gano muni na, na faɗa cike da shagwaɓa.
Dariya S.Chubaɗo yayi with so much excitement a fuskar shi yayi pouting bakin sa kamar yadda *Salma* tayi sannan ya ce,"Ummi na siyo miki wani abu yau, amma sai kin faɗa min shin me kika fi so tun kuruciya wanda har yanzu abin yana ranki kuma kina burin ki same shi ko nan gaba.
Na ɗan zare idanu ina cewa,"Yaya Sadeeq ni kam ban san abin da nike so tun kuruciya ba, abubuwan suna da yawa ba zan iya lissafa maka su ba.
Uhm Uhm!!! *Salma* kina nufin kice kin manta abu ɗaya da kika so tun kina yarinya.
Ni dai na girgiza kai ina daɗa cewa,"Ni na manta Yaya.
S.Chubaɗo ya murmusa sannan ya miko min wani abu a leda baki.
Na karɓa da sauri ina buɗe kwalin to my own surprise sai naga *ƘWARAS*
na ce,"Lahhhhh ƙwaras Yaya, wallahi ƙwaras ne...Farin cikin dake kunshe a fuska ta kaɗai ya isa mutum ya gane cewa lallai ina masifar son takalmi mai tsini wato ƙwaras ƙwaras, tabbas takalmin ya haɗu iya kar haɗuwa saboda ƙwaras ɗin dogo ne kuma glass ne wanda yake dauke da adon duwatsu a cikin sa, kamar dai takalman da amare suke sanya wa masu tsadan nan.

YOU ARE READING
UMMI KWARAS ✔
Short StoryLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...