*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 17STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
Har ga Allah ban yi wannan abin don cutarwa ba, kawai dai na guje ma Yaya Umar ne saboda kar ya dame ni da surutu, don yana son shishshige min, Bayan fitan mu da minti Arba'in da biyar, mun siyo maganin har na sha a hanya, da yake a kafa muka je muna yi muna hira har muka dawo gida ina shiga falon na ji gabana ya yanke ya faɗi, duk da ban ga abin faɗuwar gaba a falon ba, amma kuma babu Yaya Umar saboda tun daga waje na gane ya tafi kasancewar ban ga motar tashi ba a filin da ake aje motoci"
Na karasa cikin ɗakin "Inna lillahi wa'inna illaihir raji'un"
Abin da idanuwana suka gani shine ya sanya na fara jin jiri wanda da taimakon bangon ɗakin na jingina, babu abin da yake fita daga baki na sai salati, idanuwa na ba shiri yau suka soma zubar da hawaye sosai, Ni mai taurin zuciya sai gashi yau zuciyata na dukan uku uku ina ji kamar zata fashe ta fito waje tsabar tashin hankali.*Wannan ita ce ranar baƙin ciki na, ranar dana sani, wannan ranar ita ce ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata, ita ce ranar gushewar farin ciki na, ita ce ranar da ta dagula mun lissafin rayuwata, sa'annan ta katse mun karatu na,na kasa cika buri na, tsahon shekaru biyar* wannan rana ita ce sanadin barin ƙauyan mu Garin gado na koma JIHAR BAUCHI, ita ce sanadin yin nesa da ƴan uwa na.
***********************************
BAYAN SHEKARU ƊAI ƊAI HAR SHEKARU BIYAR
~BAUCHI STATE~
~TH~A kwana a tashi a sarar mai rai, Yau da gobe sai Allah, Kowacce rana darasine ga ɗan adam sai dai muyi fatan Allah yasa mu dace Amin.
Zaune nike a "reception" ɗakin karbar baki mata marasa lafiya ɓangaren likitan mata wato "gynecologist" gefe na wani kyakkyawan yaro ne sanye cikin kananan kaya har da kwallo "Ball" rike a hannun sa, Yaron bazai wuce shekara biyar ba yanayin hasken fatan mu ɗaya da nashi, so da dama mutanen asibitin cewa su keyi wai ya ɗauko uwar sa wai yana kama dani sosai, *Aarif* kenan asalin sunan Baba gare shi wato *MUHAMMAD* na ɗan share zufan da ya keto min alamar gajiya ina ɗan matsar da bokitin goge gogen tiles "mopping" da kafata ta hagu, Yayin da Aarif ke share min zufan goshi na yana cewa,"UMMI na sannu"
Na gyaɗa kai ahankali ina kallon kyakkyawar fuskar sa mai ɗauke da annuri, ina tuna wani abu game da yaron"
Aarif Ya ce,"UMMI yau ban je school ba amma gobe zaki je ki biya mun kuɗin ko UMMI, ya faɗa yana sake kallo na sai kuma yaɗan marai rai ce fuska Ya ce,"UMMI yau za a wuce ni ne a karatu shiyasa na yi magana amma ba zan kara ba ya faɗa yana kama bakin shi da hannunsa na hagu hannun sa na dama kuma ya kama kunnen sa, alamar bada haƙuri"

VOCÊ ESTÁ LENDO
UMMI KWARAS ✔
ContoLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...