30

52 2 5
                                        

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 30

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
GARIN GADO
Ranar Sallah

Yau take babbar sallah gidan su Abulle muka kwana, muka wayi gari kowani gida ana ta hada hada, Ma su zuwa masallaci na ta shiryawa,Motoci manya manya har sun fara tseren shigowa cikin Garin saboda su fara sana'arsu, zasu kai wasu daga cikin masu zuwa Sallar idi jibiya dama cen suke tafiya duk sallah.

Bangaren S.Chubaɗo kuwa wasu daga cikin abokanan sa sun zo don ya tura musu katin gayyata ta shafin whatsapp, ciki harda ZUNNURAINI  wanda ya damkawa amanar Ummi lokacin da ya tafi kasar waje.

Abin mamaki Zunnu yazo Garin gado shi da Mahaifin sa don zuwan su daban suka yi shi da mahaifin sa da kanin mahaifin sa, tun daga bauchi.

Muna gidan su Abulle muna ta shirya abinci a fada, yayin da duk Dattawa maza da matasa da kowa ma sun tafi sallar idi, fadar dake lulluɓe da rumfa ta kara wacce ta keru iyakar keruwa,abinci ne kala kala kamar su Masar gero, Masar Shinkafa da miyar taushe,wannan daga gidan mai Anguwa aka kawo,
Dambun Shinkafa wanda yaji zogale da yajin tafarnuwa, Shinkafa da jar miya da yankakken latas, Sai kulolin soyayyen nama, har da farfesun kayan ciki, wannan daga gidan Mal. Muhammadu aka kawo, sai sauran abincin da aka kawo daga makota.

Aunty Mairo kawai muka gani ta zo da kanta har fadar ta kamo ni, sannan ta ce "Abulle ki harhaɗo kayanki kema ki taho gidan mu " Na yi saurin cewa"Abulle ga Aarif ki masa wanka na taho masa da kayan sa yana ɗakin Baba Sa'adiyya"

"Toh Ummi lafiya lau ku tahi zamu taddo ku cen" Ta faɗa da hausar ta na katsinawa.

Da isar gida kai tsaye ban ɗaki ta wuce da ni,an ajiye ruwan wanka, Aunty Mairo ta ce,"Yi maza kiyi wanka da kyau ki fito.

Na gyara tsayuwa ta ina yamutsa fuska haɗe da ɗaura hannaye na saman cinyoyina, "Aunty Mairo wankan ne sai an kasa an tsare kamar Ummin da..."Chab Lallai ma" Na faɗa ina tafa hannye na ina dariya mai ɗan sauti kaɗan.

Mairo ta ce"Ni kiyi wanka bana da wannan lokacin na maganganun ki, kiyi sauri fa" Ta faɗa tana niyar fita daga bayan gidan.

Murmushi nayi kawai abin na ban mamaki amma ya na iya.

Fitowa ta daga wanka yayi daidai da shigowar Abulle da Aarif wanda ya rugo a guje yana min oyoyo, na ɗauke sa muka shiga ɗakin Mai dawa yayin da na ke korafi ina cewa"Abulle wai ni Aunty Mairo ta kai bayan gida wai nayi sauri nayi wanka mai kyau na fito" Ki ga ni fa wallahi ta goge mun hadda, Kamar dai ni UMMI ƘWARAS ni fa yanzu na canja ba Ummin da ba ce, yoo ko a da ɗinne ma ai bawai bana wankan bane, kawai dai in aka matsa min ne sai nasa kuka kuma nayi sub" Na faɗa muna shekewa da dariya

Mairo ta shigo hannayen ta ɗauke da wasu kaya peach color kamar material kamar dai lace ga net a jiki da adon stone masu yawa sai kyalli sukeyi, kai har da ma ƘWARAS, Kaya dai guda biyu ne, iri ɗaya, karshen bayani dai ni da Abulle ne, sanya kaya  mukayi, na zauna ana min ɗauri,ina cewa "Abulle kin gan ki kamar Amarya" ita ma ta ce,"Ummi da kin san yadda kayan nan ya amshi surar jikin ki da baki tsaya kina magana ba"

10:30am

Karfe goma da rabi daidai na safe aka fara dawowa daga sallar idi, tuni faɗar Mai Anguwa ta soma cika da mutane makil saboda Abba na ta rabon raguna kowa yana ta zuwa yana karba ana sa albarka tare da addu'an Allah ya maimata musu saboda hakan bai taba faruwa ba a kauyen su.

Bayan misalin minti ashirin da dawowar su gari ya ɗauka an ɗaura aure akwai taro a gidan Mai Anguwa da Gidan Malam Muhammadu, Yayin da mai shelar yai ta faman zagaya wa yana cewa "Jama'an Allah Jama'an kwarai  yau take salla babbar rana kuma a yau aka ɗaura auren ƴar Malam Muhammadu wato *SALAMATU UMMI ƘWARAS tare da kyakkyawan angon ta mai suna *Sadeeq Abubakar Chubaɗo* shela ake tayi wanda mai shelan yazo ta kofar gidan da Allah ya bashi sa'a da karfi ya ke yi kamar an aiko sa....Ya cigaba da cewa "Jama'an Allah jama'an kwarai a yau ɗinnan aka ɗaura auren ƴar gidan Mai Anguwa wato *ZAINABU ABU* mai tagwayen suna ABULLE tare da angon ta *ZUNNURAINI*

Zaune nike ɗakin Mama muna hira da Mamie wacce take ta faman koɗa ni wai dama haka nake da kyau kamar ba Ummi ba.

Nayi dariya ina kallon gefen da Mama take na ce"Mama ke ma kin gan ki kuwa, wato dai wannan sallar kowa kyau yake yi, Mama duk saboda murnar dawowa ta ne ko?

Daidai na faɗi hakan kenan naji muryar mai shela na ambaton suna na kamar shi ya raɗa min, sake kasa kunne nayi naji abin da yake faɗa da kyau.

Wani ras naji a kirji na, don ban kawo hakan nan kusa ba, muryoyin su Mama ne ya dawo dani daka tunanib dana faɗa suna hamdala suna addu'ar   "ALLAH YA SANYA ALKHAIRI, ALLAH YA BASU ZAMAN LAFIYA MAI ƊAUREWA"

Duk dama abin a ba zata ya zo min ban yi tsammanin auren ɗan binni nan kusa ba, kwata kwata bana kawo hakan a cikin rai na amma wani farin ciki ne ya ziyar ci zuciya ta yayin da na ji har da Abulle aka ɗaura wa aure,
Yanzu kenan mun yi aure ni da Abulle kawata hamdala na keyi cikin zuciya ta hakan yasa na fita tsakar gidan mu don in taddo Abulle wacce take ɗakin Mai dawa amma abin da idanuwa na suka gane min shi ya sani na tsaya chak a tsakar gidan ina zare idanu kamar wata mujiya.

______________________________________

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE

UMMI KWARAS ✔Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon