32

32 1 0
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 32

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
KATSINA STATE
CHAKWAKIYAR YINI ƊAYA,RANAR SALLAH AKE TA WANNAN HARGITSIN.

Kowa ya samu waje ya zauna a babban barandar Mai dawa, Ina nan tsaye a nan in da nike idanuwa na shi ɗin jarumi na suke kallo bana ko kyaftawa, Kallo na yake yi shima murmushin da ke kunshe a fuskokin mu ka ɗai ya isa mutum ya fahimci soyayyar da muke ma junan mu,Wani farin ciki ne yake ziyartar zuciyoyin mu, Idan muka tuna cewa an ɗaura mana aure.
A hankali ya soma takowa har yazo daf in da nike kai tsaye ya sanya hannayen sa ya rike min arms ɗina, ya fini tsaho sosai hakan ya bashi damar sunkuyawa kaɗan ya sanya laɓɓan sa saman goshi na yayi min light peck wanda har cikin zuciya ta sai da naji shi.

Ya juya zai tafi ba tare da ya ce min kala ba, da sauri na sanya hannaye na na riko kasan rigar sa na janyo shi ya dawo baya,juyowan da zai yi na rungume shi tsam na shige na kwanta a faffaɗan kirjin shi ina jiyo yadda zuciyar shi ke bugawa in second ya sanya hannayen sa ya rungumo ni ta baya....Hmmm abin ba'a cewa komai, Mun kai dakika biyar a haka nayi cikin ɗaki da gudu ina murmushi.

S.Chubaɗo yayi murmushi yana kara jin soyayyar UMMI a cikin zuciyar shi, yana kara jin kaunar ta na mamaye shi,yana kara jin ta tamkar rabin jikin shi, ya sosa keya haɗe da sanya hannu ɗaya cikin aljihun wandon sa ya nufi barandar Mai dawa, Sai yaga ana ta kallon shi, kame kame ya fara yi amma inaaaa tuni Mai dawa ta sille shi tana ta tsokanar shi, duk da halin da mutan gidan suke ciki, ganin yaransu na farin ciki shi ya kara kwantar masu da hankali.

Ɓangaren Mama da Baba suna son sanin gaskiya game da Aarif, Fannin Mamie ma dai haka saboda hankalin kowa ya kwanta, amma tana son Sadeeq ya basu labarin yadda akayi ya san Shatou na cutar da su.

Bayan S.Chubaɗo ya ɗauko laptop ɗin sa, ya nemi gu ya zauna ya buɗe ta sannan ya fara binciken wasu abubuwa, Yayi gyaran murya ya mai da hankalin shi sosai akan laptop ɗin da yake tapping sai da ya ɗau akalla minti ashirin kafin ya ɗago kyawawan idanuwan sa, ya kalli duk mutanen dake zaune a farfajiyar barandar Mai dawa, musamman ma Abba da Mamie sai Ummi duk sun damu suna jiran suji wani abu daga bakin Sadeeq.

S.Chubaɗo Ya ce,"Uhmmm Abba ɗan matso kusa, Abba ya matso sannan ya cigaba da cewa,"Wannan ne sabon  password ɗinka yanzu sannan kuma duk wani takaddun da Shatou ta mallaka daga hannunka tun bayan lokacin da ban da lafiya....They are fake, ya ɗan tsagaita ya nuna masa wasu pictures, sannan ya cigaba da cewa,"Abba ba tare da sanin ka ba Shatou ta mallaki takaddun filaye dana gidajen ka.

Wata rana bayan na samu lafiya sai naje flat ɗin mu ni da ita, Ina neman wasu daga cikin kayan sawa na, anan na ci karo da files zube saman center table, security part ɗin ta sun tabbatar min da cewa cikin hanzari ta bar gidan, hakan ne ya bani damar duba files ɗin naga duk originals ne, a ranar kuma a lokacin ba tare da bata lokaci ba na kirawo lawyer ya min fake files, Allah ya taimake ni har ya kawo mun mu kayi replacing na bar part ɗin....yanzu haka suna hannu na, bata sani ba and by the time ta fara siyar ma mutane lokacin za'a gano ta har a kama ta.

UMMI KWARAS ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang