08

91 3 25
                                        

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 8

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Kada ku manta masu karatu dama fa ni Ummi na iya ƙissa kala kala ko zan ƙirga muku su yanzu ba zasu iya ƙirguwa ba amma yanzu zan zayyana maku ɗaya daga cikin ƙissan dana iya"

Dama a kowacce rana wasu daga cikin matan sukan zo da wur wur sai su tsare ma masu zuwa latti wajen zama to ranar dai na zo da wur wuri sai na samu wajan zama to ana nan sai ga marasa kunyar nan sun shigo nan suka fara kokarin ajiye jukkuna suna tsare wa ƙawayen su wajan zama ban ce musu kala ba kuma ban ko kalle su ba, ka fin karfe tara ajin namu ya cika da ɗalibai, Benchin dana zauna ma ya cika maimakon mutum bakwai kamar kullun yau kusan mu tara don bala'i wallahi na matsu ko numfashin kirki ma bana yi ga zufa wanda har ya jika min wuyar hijabi ta kunsan kauyen namu lokacin rani ne gashi akwai zafi sosai ko da safe ne, sai da na bari an fita break, fuuuu na fita daga makarantar ko tambayar izini ban ba wani gida na shiga wanda yake bayan makarantar nayi sallama wata ƴar tsohuwar mace ce ta amsa min ta ce na shigo"
Bayan mun gai sa da tsohowar na ce mata ruwan sha zata sammin ta ko bani ruwa ina shan ruwa ina waige waige har idanuwa na suka hango murhu cike yake da toka taf, wata hamdala nayi sannan cikin dabara na cewa matar,
"Don Allah inna kina da tasshi "barkono dakakke"zamu ci doya ne da shi a makaranta" ai kuwa matar dana lakaba wa inna ta ce," eh baza a rasa ba ƴar nan bari na dubo miki a cikin ɗaki, tana shiga ɗakin ni kuma na buɗe leda ta dana samo a waje na cika ledar da toka na ƙulle na koma inda nike tsaye sai ko ga ta ta fito da leda fara cike da tasshi wata hamdalar na kuma yi kana na amsa ina godiya sosai, a bakin kofar shiga makarantar na tsaya na samu wani ƙyalle mai ɓuli ɓuli da shi na tankaɗe tokar na samu wata ledar na zuba na chakuɗa shi da wannan dakakken barkonon ya chakuɗu sosai nima duk ya shiga mini hanci amma yana iya, na ƙuƙƙulle a ledar pure water na kakkaɓe jikina sannan na koma aji lokacin har an koma aji ba tare da bata lokaci ba na yi wa malamar karyar cewa," HM" ya ce," maza su fita filin assembly matan kuma za'ayi checking ɗinsu sannan na kara da cewa,"ya ce ma," ba sai kinje kin tambaye sa ba wai anyi kiranshi a cikin gari baya nan"

Malamar cike da rashin yadda take bina da kallo, nima ina kallon ta ina jujjuya idanuwa yadda kusan ina filin dambe ne, kuma ta kasa fahimtar wani irin checking kuma yanzu da rana, amma koma miye ita taga HM yanzu nan ba da jumawa ba, bari taje ta same shi, Ina ganin sanda ta fita mazan ma suka bi baya ta suna ihun tsalle abin su hakan ya bani damar fito da ƙulli-ƙullin toka ta da barkono na, kana na hura ledar kaman zata fashe suna kallo na amma basu san me zanyi ba haka na rinka fasawa ɗaya bayan ɗaya nan da nan hayakin tokar ta turnuke ajin zuwa wani lokaci ko wacce ta soma mustsuke idanuwa sosai suke tari suna atishawa tsabagen yajin daya shige su ina daga bakin kofar ajin babu abin da nike ban da dariya ina rike ciki har da guntin hawayen dariya ina cewa UMMI ƘWARAS kenan kuke ji duk wanda ya taba ni sai yaji ajikin sa, daga yau duk wacce ta kara tsare ma wata wajan zama wa billahillazi sai na yi mata fiye da haka"

UMMI KWARAS ✔Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz