09

56 4 10
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 9

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

_____________________________________

Baba ya saki murmushi sosai yana cewa "abbb to to tooo na gane ya ka nan ɗan samari"

Na koma wajan ɗan binni na kamo hannun sa na ce," Taso muje Baba na kiran ka, muka tako a tare ina murmushi shi ma dai murmushi ya keyi har muka isa Barandar ɗakin Baba wacce aka kewaye wajan da ginin laka ma'ana akai wa wajan katangar laka karama, muna isa Baba ya ce," Bisimillah zauna mana, Ummi ɗebo masa ruwa a randa ko"

Ya zauna saman tabarmar Baba daga gefe ni kuma naje randar Baba wacce take tsakiyar kusurwar hanyar ɗakin sa na ɗebo masa ruwa a kwanon tasa  na rufe nazo na ajiye agaban ɗan binni sannan na zauna kusa da Baba kaina jingine a jikin sa ina wasa da yatsun hannun Baban ina kallon ɗan binni ya wani sunne kai abin shi.
Baba yayi gyaran murya Ya ce,"Bakon mai gari ko?

Ɗan binni ya gyaɗa kai yana mai jin nauyin Baba shi dai ya rasa dalilin da yasa yake jin kunyar Baba tun ranar da ya fara ganin sa a makaranta....
"Baba ya katse mishi tunaninshi da cewa,"Ni kam miye asalin sunan ka ɗan samari?

Ya ɗago kai cikin girmamawa da ladabi Ya ce," *Abubakar Sadeeq Chubaɗo* Baba amma kowa Sadeeq yake kira na ya faɗa yana ɗan shafa suman kanshi.
Baba yayi murmushi Ya ce,"Ma sha Allah babban suna ne,Sunan ɗaya daga cikin khalifofin Annabi wato Abu-bakr Al-siddiq mafi kusanci da kuma siriki ga fiyayyun halitta Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W). Baba ya cigaba da cewa,"To Allah ya shi albarka Sadeeq" Amiin ya rabbi ɗan binni ya amsa da fara'ar sa wanda nima har murmushi nayi muka haɗa ido sai na galla masa harara haka kawai shima hararar ta bashi dariya sai ya gumtse ƴar dariyar sa ya samu ya ɗaure fuska ya koma sauraron Baba.

Baba ya ɗaura da cewa," Wato a ƴan kwanakin da ku kayi a ƙauyan namu hakika ina lura da mu'amular ku da Ummi duk dama bata fito ta faɗa mun ba amma Ummi ƴata ce wacce nike matukar ji da ita shiyasa ni ke lura da mu'amular ta ko a ina,
Baba ya cigaba da magana cikin natsuwa Ya ce,"Lallai kayi ƙokari sosai wajan ganin ka koyar da ita kaɗan daga cikin ilimin boko sannan na san saboda kai Ummi take daurewa tana zuwa makaranta saboda haɗuwa dakai ya kara sa mata son karatu a cikin zuciyar ta" *Abubakar* Kai ke koyawa Ummi karatu idan ta dawo, kuma Ummi ta saba dakai sosai amma kuma sai gashi naji Mai Anguwa yana cewa gobe zaku tafi? Eh Baba ya bashi amsa.

Baba Ya ce," To dama kai ɗan wace jiha ce *Abubakar* Baba ya karashe maganar yana mai kallon fuskar ɗan binni.

A hankali ya ɗago kai ya fara magana,
"Eh Baba ni ɗan asalin jihar Bauchi ne kamar yadda ka sani Baba Bautar kasa ta kawo ni jihar katsina cikin garin jibiya, Gobe in shaa Allah zamu bar nan dama mun kara hutun sati biyun ne don mu kara fahimtar wata rayuwar kasantuwar dukkaninmu daga nesa muke kuma ba lallai mu sake haɗuwa ba sai mun ɗau lokaci mai tsayi, Baba a taƙaice dai ƙauyen Garin gado muka zaba a duk cikin ƙauyukan da suke kewaye da Jibiya saboda shine mu kafi kusa dashi daga in da aka sauke masu yin *Bautar ƙasa*

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now