07

53 4 12
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 7

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Wani irin murmushi naga yayi ya sauke ajiyar zuciya mai dadi lokaci ɗaya sai na koma kallon sa da kyau ya lumshe idanuwan nasa sannan yace "Shatou na" kinji yanda muryar ki ta bugi kirji na" wallahi sai naji ina ma ina kusa na ringumo ki zuwa jiki na saboda bani kaɗai ba har gaɓoɓin jiki na sunyi kewar ki Shatou na"

Zuba masa idanu nayi don ban gane abin da yake nufi ba, taɓe baki nayi na cigaba da rubutu na amma duk da haka sai nake jin raina bai kwanta ba da maganar da yayi shin me hakan ke nufi kenan? daga bisani na aje alkalamin rubutun, na zauna da kyau ina kallon sa har ya gama wayan wanda har wani lumshe idanuwa yake yana murmushi sosai abin ya bani mamaki.

Kamar ance ya kalli inda nike sai ya ga na dena rubutun shi dai ɗin ni ke kallo, mustsuke idanu yayi sannan ya ɗaure fuska ya ce,"Ni kam ba rubutu na saki ba? Me kuma kike kallo ko saurare?
Ban bashi amsa ba sai na zabga uban tagumi hannu biyu na zuba masa idanuwa na, yai ta magana yai ta magana amma shiru ba ansa ya soma shirin tashi ya matso daf dani ya tsugunna ahankali ya sanya hannayen sa ya kama hannun da nayi tagumi da shi, ya ɗan matsa su kaɗan a hannun sa
*Karo na farko da naji tsigar jikina ta tashi wanda so nawa Baba yana rike min hannu amma ban taɓa jin komai ba duk dama ni yarinya ce*

Ya zuba min idanuwan sa yayin da nima kallon shi ni keyi, Hakika ina hango wani abu acikin idon nasa amma naka sa gane shin miye shi wannan abun? sauke idanuwa na nayi ahankali na cire hannye na acikin nasa sannan na ɗan ja baya kaɗan duk yana kallon abin da ni keyi, ka fin na samu kwarin gwiwar tambayar sa na buɗe baki na ce,"Kana da aure ne ɗan binni" Wallahi ni kai na ban san ya a kayi nayi tambayar ba tun da a kuruciya ta dai ban san abubuwan da suka wajaba ga mai aure ba "Ni dai na san wata rana Mama tana yiwa Mairo faɗa sai na kasa kunne ina ji da yake ina cikin ɗakin ban fita ba, ina sauraron su Mama ta ce kar ki kuskura ki bari namiji ya taɓa jikin ki ko da ɗan yatsa ne hakan babu kyau a musulunci ko da kin ga wasu nayi ki kokari ki hane su saboda saɓon Allah ne sai dai idan su ɗin ma'aurata ne" alokacin da take yi mata bayani sai ban gane ba sai na buɗe baki na ce," Mama miye ma'aurata kuma sai ta harare ni daga bisani sai ta kalli Mairo ta ce ina nufin Mata da Miji idan su kayi aure sune Ma'aurata kin fahimta Mairo" Ban sake magana ba don wallahi ni dai har ga Allah ban fahimci abin da take nufi ba amma kuma tun daga ranar maganar ta dasu acikin zuciya ta bana barin namiji ya taɓa ko da ɗan yatsa ta ne shiyasa ma wancen ranar na samu kwarin gwiwar marin Kamale"

Yayi matukar mamakin tambayar da nayi masa wanda yasa shi kallo na amma ya kasa amsa min" na sake na ce," Ba ance Mata da Miji bane suke taba hannu ko jiki ba?
Da mamaki ya sake kallo na, yana mamakin shin dama yarinyar nan tana da wayau haka,na katse masa tunanin sa da cewa," Me yasa to kai kake cewa kayi kewar jikin ta a wayar? na karashe maganar ina yawo da hannaye na biyu, duk tambayar nan babu wanda ɗan binni ya samu damar amsa min saboda muryar Aminiya kuma ƴar uwa ta da naji

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now