38

43 3 5
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 38

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

5years later
London Bridge Hospital part of HCA Healthcare UK

Faculty of Medicine

Cikin sauri kuma a layi uku uku student ɗin suke tafiya yayin da na hango kyakkyawar halittar nan namu a tsakiyar colleague ɗinta su uku layi na farko, tana tsakiyar su, suna sanye cikin shiga personal amma kowannen su ya sanya labcoat da hand gloves kai tsaye theater room suka shiga student ɗin suka zazzauna a wani ɓangare na daban wanda an katange wajan da farin glass amma kuma suna da babban T.V wanda ta nan suke kallon yanda ake operation, ko wani iri har haihuwa, har surgery da sauransu...Shekara Shidda ne yanzu suna shekara biyar practical na tsahon shekara biyu sukeyi, yanzu saura kwanaki ya rage musu suyi hutun shekara ɗaya sannan su dawo su cigaba.

A kullin idan suka shiga theater room ana kiran mutum ɗaya don suyi aikin, da an gama sai suyi ticking sunan wanda aka kira, kuma suyi recording abubuwan da yayi da sauransu a haka har kowa yayi.

*SALAMATU MUHAMMAD* "can you please come in side"

Uhmmmm sai da na sake kallon Ummi da kyau ni Diela kafin na cigaba da rubutu.....Hakika Ummi ta canja tayi kiba hutu ya nuna a jikin ta, tana da cikin da bazai wuce cikin wata bakwai zuwa takwas ba ma yanzu haka, da alama ma ta kusan haihuwa.

Cike da kwarin gwiwar ta taso ta nufo kofar da zai sada ta da theater room ɗin da likitoci da nurses suke,
Duk dama ba tayi tsammanin ita za'a kira ba, amma ako da yaushe suna zama cikin shiri don aikin su ne dole su mai da hankali idan suna class, Ta buɗe slicing door ta shiga theater room bayan ta sauya kayan ta a wani karamin ɗaki ta fito cikin shiga irin ta doctors ɗin doguwar riga irin ta masu cutar covid, fuska kawai suke bari shima kuma ana rufe wa da face mask .

"Are you ready?

"Yes sir, I am" Okay let get started"

Suka soma surgery ɗin ana yi ana tambayar ta cikin kwarewa da nuna jajircewa akan aikin ta ma take amsa tambayoyi tare da yin dukkan abin da aka sanya ta cikin natsuwa saboda gaba ɗaya ta tattara hankalin ta kacokam zuwa ga mara lafiyan, mara lafiyan daga Nigeria aka kawo shi, accident yayi tsahon shekaru biyar wanda ya samu karaya a kafa ɗaya, da kuma tsagewar spinal cord ɗin sa.

Successfully aka gama aka fito da shi wasu daga cikin nurses ɗin suka mai da shi ɗakin da yake daban, Ni kuma Ummi ina tsaye da likitan yana min bayanan wasu abubuwa, a dai dai lokacin na hango Yaya Mahmud da Aliyu kanin Umar sai wata Mace ta sanya abaya black ta rufe dukkan al'aurarta fuskarta kawai nake iya gani shima ban wani gane taba...duk dama she looks very familiar to me.

Sanin cewa Yaya Mahmud bai gane ni ba shiyasa na bar su suka gama yima doctor magana, ya sanar dasu dukkan abin da ya kamata sukayi godiya har likitan ya tafi ina tsaye na juya kenan ina kokarin cire face mask ɗina sai naji Aliyu na cewa,"Aunty Shatou kin ce Sadeeq da Ummi suna London wani hotel suke ne?

UMMI KWARAS ✔Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon