27

30 5 3
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 27

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
BAUCHI STATE
GRA

"Me kuma kike zubawa a cikin abin cin, ina kara sowa in da take ta juyo ta rufe fuskar ta da bakin abu muna kallon kallo, kawai sai naga ta ciro wani abu kamar turare ta fesa min a fuska, to ni dai tun daga lokacin ban sake sanin inda hankali na yake ba.

************************************

Misalin karfe ɗaya bayan kowa yayi Sallan azahar, Abba ya huta, Suna zazzaune a falo don tun da Abba ya dawo babu wanda ya fita a cikin su, Mamie ta tashi tana cewa tun da munyi sallah ya kamata aci abinci, amma me ya tsaida Ummi ne na ji ta shiru har yanzu.

Abba ya ce,"Kin san Ummi da kunya yanzu haka wata kil ta shirya abincin kawai ta kasa shigowa ne ta sanar dake Mamie.

Mamie ta ce,"Lallai kam ka fahimci halin Ummi sosai yallaɓai, Abban Sadeeq bari naje to na duba ko komai ya haɗu.

Okay cewar Abba, Sadeeq yayi saurin mikewa yana cewa,"Muje na raka ki Mamie na.

"Nooooo my son, kayi zaman ka kawai your daddy needs you beside him kaji" Mamie na kaiwa nan ta fice da sauri tana wondering hali irin na Ummi, abin na birge ta.

Mamie ta shigo kitchen tana faɗa,
"Wai ashe Ummi bata ma jera coololin abincin ba, to ina tayi ne ma wai.....ta doshi kofar fita ne ta iske Ummi kwance kamar dai ta suma, don ta kira sunan ta yafi a kirga amma shiru, ta jijjiga ta nan ma shiru.

Wannan tashin hankalin shi yasa bata bi takan wani abin ci ba, bayan ta sanar da su Abba shine duk suka tashi duka zasu kai ta asibiti amma buɗar bakin Shatou ta yi gyaran murya kamar dai mai mura ta ce,"Uhm Uhm Uhm"

Hankalin kowa ya dawo kanta ana expecting ko wani abu ne.

Sannan ta ɗaura da cewa,"Abba, Mamie kuna son ba ma kan ku wahala ne, me zai sa baza ku haɗa ta da masu aiki ba dole sai ƴan gida sunje ne?

Ta cigaba da cewa,"Kuma ma Abba daga dawowan ka ko abinci baka ci ba, bari ma na kwaso kayan abincin tun da Mamie bata kwaso ba"

Abba ya dakatar da ita da hannu sannan yace,"No need Shatou"

Ya ɗaura da cewa,"A tunani na, ko ƴan aikin ma muna da damar da zamu kai su asibiti tun da a gidan mu suke zaune kuma a ka'idance ma muna matsayin iyayen su ne, tun da suna zaune da mu kuma suna kula da mu da lafiyar mu, Me zai sa mu masu kuɗi muki kyautata wa masu aiki ?,

Abba ya girgiza kai sannan ya ce,"Aisha ai Ummi tamkar ƴa na ɗauke ta a gidan nan Ummi ba bare bace da zaki ce a haɗa ta da ƴan aiki su kai ta asibiti, kuma ma kina faɗan waɗannan abun kin manta cewa ita ce yarinyar da Sadeeq zai aura, in ban da kaddara ai da tun tuni ya aure ta.....yana kai wa nan ya waiga ya kalli Mamie ya ce,"Mamie muje please duk suka fita cikin sauri amma ban da Shatou.

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now