22

35 1 0
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 22

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
BAUCHI STATE
9:00am

Na dau kusan minti goma kafin na samo ball, wanda na same sa acen wajan tank din hotel din da alama wani ne ya canja mata waje, Ko dana dawo to my own surprise banga Aarif ba, Baya wajan na soma kwala masa kira amma shiru bai dawo ba Ina zuwa gaban flat din na hango shi yana tsaye da wani handsome man wanda yake sanye da track suit da canvas ya juya baya yana yiwa Aarif wasa, murmushi nayi, sannan na nufi wajan da fara'a Ina cewa,"So Aarif dama nan kazo ina cen Ina neman ka, to taho mu tafi ko kada Mamie tayi ta neman mu............ban gama rufe baki ba idanuwana suka yi min tozali da mutumin da na fi tsani duk fadin duniyar nan, mutumin daya sanya ni a cikin kaddarar rayuwa mutumin da yasa na amsa laifin da ban aikata ba, kuma mahaifi ga Da na Aarif.

Da saurina kauda idanuwa na daga gare sa bayan na tuna shi ya ja mana bakin jini a garin mu na fizge hannun Aarif bayan na galla masa harara sannan na Mai da kallo izuwa ga Aarif na ce,"Kul Aarif, ka dena zuwa wajan mutanen da basu san Allah a al'amuran su ba kaji son" Kasancewar Aarif karamin yaro ne, bai ma fahimci  abin da take nufi ba, Aarif duk da ba wani fahimtar abin da na fada yayi ba amma sai ya gyada kai yana cewa,"Ummi to amma shima ai Uncle dina ne ko?

Ban iya bashi amsa ba, saboda wani abu da ya tsaya min a zuciya, cikin raina na ce,"*Ba uncle kaɗai ba Aarif shi ɗin Mahaifin ka ne* A fili kuma  naja hannun sa da sauri muka bar hotel din....Umar na nan tsaye ya kasa gaba ya kasa baya, zuciyar sa na tafarfasa yana tunanin anya wannan yaron ba jinin sa bane don for the first time da ya ga yaron sai da tsigar jikin shi ya tashi, ya sake ya jijjiga kan shi ya ce,"Hmmmm
After all yaron yayi kama dani sosai, babu wanda zai je wannan ba jini na bane.....ya dafe goshin sa da yaji wani azababben ciwon kai ya rike masa saman kai, da kyar ya iya komawa daki ya kishingida.....yana mai kokarin kiran Mike a waya, bugu daya ya dauka yana cewa,"Aboki ka tashi lafiya?

Umar ya ce,"Haba Ina fa lafiya Mike, asiri na yana shirin tonuwa fa.
Mike ya ce,"Ban gane bayaninka ba, kamin dalla dalla ya faɗa da hausar shi irin ta kabilu.

Umar ya ce,"Ina yarinyar da nayi wa fyade Mike friend din cousin dina a katsina!

Mike ya ce,"Uhmm go ahead"

Mike I saw her today, Ta shigo compound dinmu yau da safe and naga wani yaro a wajan ta, Mike idan kaga yaron nan zaka rantse nine saboda kamannin mu ya baci, Amma na rasa gane yanda a kayi ta zo bauchi bayan na san basu da kowa anan.

Mike yayi dogon ajiyar zuciya kafin yayi gyaran murya ya ce,"Umar in dai yarinyar nan ce to tabbas yaron daka gani jinin ka ne, maybe ko tayi aure a bauchi ne" view dina kenan.

To Mike kana ganin hakan bazai zaman min matsala ba? Noooo cewar Mike "Babu wani problem bro kawai ka kiyaye haduwan ku da ita.
"Okay na gode Mike"
You always welcome, ka kwantar da hankalinka babu komai In Sha Allah idan ma yaron ka ne da gaske zamu San yadda zamuyi da shi saboda kada asirin mu ya tonu.

Da sauri Umar ya tari numfashin sa yana cewa,"Yawwa hakan ma za'ayi Mike, zan rinka watching moves dinta da zaran naga wani abu zan sanar da kai da wuri.

Alright no problem sai mun sake magana cewar Mike. Suka kashe wayar.

Bangaren Ummi kuwa tana komawa gida hankalin ta a tashe ta kasa zaune bare tsaye, tana tunanin ko ta kai karan shi kotu ne, tun da tana da hujja a tare da ita *Aarif* shine shedan ta saboda confirm jinin Umar ne, Sai dai dole kotu zata bukaci muhimmiyar sheda, Kuma *ABULLE* na daya daga cikin manyan sheda saboda ita ce...................ban kara sa maganar ba naji Mamie ta dafa kafadata tana tambayar,"Ummi kin kama wanda yai miki fyade ne, tun dazu nake ta sauraron maganganun ki Ummi.

Inda inda na soma yi, wanda na rasa ma me zan fada mata, shirun da nayi shi ya bata tabbacin an samu mahaifin Aarif, Mamie ta ce,"Idan har da gaske ne kimin magana Ummi ni zan taimaka miki a kwato miki hakkin ki, da mutuncinki daya zubar miki.

Ban san lokacin da kuka ya kwace min ba mai karfi take Mamie ta rungume ni tsam a jikin ta tana rarrashi na tana cewa yi shiru Ummi kinji babu Abin da zai faru komin mulkin sa da kudin sa mu ne za muyi nasara.

Ita Mamie batasan me nikeyi wa kuka ba Abulle nike tausayi wacce take cen katsina, kuma Abin ya shafe ta, ta yaya zata zo bauchi?
Wata zuciyar tace,"Ummi komawar ki Garin gado shine abin da ya kamata kiyi a wannan lokacin, wata zuciyar kuma ta ce,"Kin manta akwai mara lafiya a karkashinki Ummi, Shin wanne zakiyi, zaki koma kauyen ku ne ko kuma zaki kula da mara lafiya?

Har Mamie ta bar dakin tunanin da nikeyi kenan na kasa yanke hukuncin abin da ya dace, idan har na dau lokaci mai tsaho watakil Umar ya gudu, ko kuma ya aikata wani abun, Ohh Allah ina neman tsari daga sharrin wannan mutumin.

Misalin karfe ɗaya na dare, bacci ya kaurace wa idanuwa na, Na ta shi na ɗauro alwala na fara nafilfili ajere ajere nayi ba adadi, Ina zaune misalin karfe uku da rabi na dare naji motsin tafiya ta bayan window na, da sauri na tashi ina kokarin lekawa sai na hango inuwar mutum kamar dai macce cen kafin ka kai flat din Mamie kasancewar flat din Mamie yana gaban dakunan da muke, na sake labulen ko tsoro ban ji ba na bude kofa na fita ina takawa a hankali na laɓe wajan flawoyin dake gefen ɗakunan mu, anan Allah ya hasko mun fuskar Shatou, Zuciya ta tayi mummunar bugawa sakamakon ganin Shatou na durkushe a wajan tana kokarin tona rami ta sanya wani ɗan misilin tulu wanda ban isa ince ga abin da yake ciki ba, Ina kallon ta ta gama ta kakkaɓe kayan ta sannan ta tashi ta tafi nata gidan ɗin wanda a kewaye yake gefen ɗakunan mu.

Da sauri naje wajan ramin da addu'a na sanya hannu na tona ramin na ciro tulun, ina kokarin tashi ne ya ɓare ya faɗi ƙasa warwas ya fashe, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un wani ruwa ne mai yauki ga wani ɗoyi da yake yi wanda nayi imani da Allah warin ruwan nan zai iya halaka mutum.

Sai wani kadangare wanda aka nannaɗe shi da zare, har da laya a bindin sa, da alama kadangaren nan baya da rai, Ni dai Ummi yau naga jalala!!!! Leda na sanya a hannu na, na warware zaren sannan na cire layan, bayan na tattara wajan na zuba komai a sharan kofar ɗakunan mu da niyan gobe in Allah ya kai mu zan ɗauka na zubar a waje.
Na dawo na buɗe layan.

Subhanallah!!!!!! Sunan da nagani ne kaɗai ya rikita min hanjin ciki duk da cewa da larabci aka rubuta sunayen ,zama nayi ina tunanin yadda zanyi da layan nan nama fa manta cewa dare ne.

*Masu karatu kun san UMMI ƘWARAS babu abin da ba zata iya ba, karfe ukun dare ta fita ta tono abu kuma ta zauna a wajan tana tunanin yadda zatayi da abun lallai Ummi kina da karfin hali.*

Ni Ummi na tashi na shiga daki dauko a shana, na tuna wani lokaci Baba yana karantar wa yake cewa ita laya an fi konata idan ana so a karya asirin dake cikin ta, hakan yasa na zauna zaman dirsham na kona wannan laya kurmus,na koma ɗaki na cigaba da nafilfili, ina rokon Allah da yasa idan kudirin sharri ne ya koma kan wanda yayi, idan asiri ne kuma Allah ya karyar da shi.

Misalin karfe biyar saura minti shidda ana ta kiraye kirayen sallah hakan yayi daidai da jiyo muryar Mamie da alama wani sabon al'amari ne yake faruwa, kasancewar hayaniya tayi yawa,
Hayaniyar ƴan aiki da na masu gida.

Hakan yayi daidai da tashin da nayi na ɗauro wata alwalar don yin niyan sallan asubahi.

______________________________________

*Kuyi hakuri da rashin saurin labarin UMMI ƘWARAS, ku kasance masu danna min like akowani update.*

______________________________________
STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE

UMMI KWARAS ✔Onde histórias criam vida. Descubra agora