KARSHE

70 2 15
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 39
Last page

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

*A journey of a thousand miles begins with a single step*

UMMI ƘWARAS Has come to an end__________________________________

THE NEXT DAY
FRIDAY
LONDON ISLAMIC SCHOOL
8:30am

Duk friday nake kai su islamiyya da safe wanda yake kan titin Damien St, primary and secondary school ne wanda sosai ake koyar da addini...kabilu daban daban, turanci da larabci ake koyarwa...idan suka tafi tun da safe basu dawowa sai 5pm dot.

Da yamma musalin karfe biyar naje na ɗauko su muka dawo gida...bayan munyi sallan magrib muka zauna na koya musu karin da akayi musu a islamic school sannan muka yi karatun alkur'ani, na koya musu kananan littafai, na musu tarihi kaɗan daga cikin wasu littafan su, kafin su kayi bacci, na gyara musu kwanciyar su sannan na tashi na tafi wajan Ɗan binni na.

Yana zaune a wata sofa daga cikin bedroom ɗin, yana karanta news paper nayi mi shi peck a wuya, na rungume shi ta baya.

Ajiyar zuciya yayi, yayi wulli da news paper ɗin sannan ya janyo ni na faɗo jikin shi ina dariya saboda chakulkulin da ya ke min.

Sai dana tsagaita da dariyan ya kama hannaye na biyu yana nazarin wani abu...cen kuma ya ce"Salma na"

Na ce," Na'am Ɗan binni na"

Yayi dariya ya ce,"Ina so muje Nijeria ba dan komai ba saboda a cen tarihin soyayyar mu ya fara, katsina, jibia, garin gaɗo.

Can't forget the first day I set my eyes on you *SALMA* kina sanye cikin uniform ga ki lokacin ƴar haka...yayi nuni da hannunsa irin ƴar haka ɗinnan wai karama.

Na zumɓure baki ina cewa "Yaya ɗan binni, bana so ni"

Dariya ya yi yana cewa,"Kamar kin san ko haka kikeyin magana lokacin, komai akayi rigima ga neman tsokana, ga wani soyayyar ƙwaras da Allah ya ɗaura miki Hahhhhhhh  Salma ranar dana fara ganin ki fa kuka kika rinka yi wai bazaki shiga aji baaa" hahhhhhhhhhhh ya kwashe da wata dariyar.

Ina kwance ina dariya nima sai na ce,"Yaya ɗan binni ka tuna wata rana daka fara nuna min kamar so na kake?

"Yayi murmushi ya ce,"Salma bana manta every single moment ɗin da mu kayi spending years back.

Bana mantawa na ce miki,"

"Meya sa baki da saurayi naga dayawa ƴan matan ƙauyen nan sa'annin ki ko wacce na da saurayi ke kuma baki taɓa yimin maganar samarin ki ba" Na ɗan zare ido kaɗan sannan na ce," ni bana da saurayi ni ba aure zanyi yanzu ba Baba ya ce *Mairo* zai wa aure da *Yaya Mahmud*

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now