15

49 3 3
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 15

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye

______________________________________

Ranar monday ita ce ranar da muka fara *Junior waec*, sai da muka kwashe akalla sati uku sa'annan muka gama, wannan karan ba tare da ƴan makaranta hutun mu zai fara ba, muna gamawa aka sallame mu, amma da yake hutun JSCE ne muka gama kuma wasu daga wannan ranar sun bar makarantar, wasu kuma zasu cigaba kamar mu dai. Wannan dalilin ne yasa muka fara yin ƴar gaɗar mu a makon da zamu tafi, da yawa daga cikin ɗaliban aji ukun an kawo musu abubuwan da zasu rabama ƙawayansu kamar su: Sticker mai ɗauke da hotunan su, Hand fan, Memo da sauran su, na samu abubuwa da yawa daga wajan ƙawaye na har da wa'inda bamu magana dasu haka suka rinka bani kyautar abubuwa acewar wasu daga ciki za suyi missing ɗina kuma wai nice Woman leader ɗin su komai da ruwa na.

Ranar laraba ana gobe zamu tafi gida muna tsaye ƙasan bishiyar mangwaro ta gefen hostel ɗin mu, Ni da Abulle da wasu daga cikin ƙawayen ta,  muna ta hira kasancewar kwana biyu kowa yana free ne tun da exam a keyi don su Abulle basu gama jarabawa ba, wasu ɗalibai muka hango suna dunfaro inda muke, ƴan JSS1 zasu kai mutum takwas sun taho ajere kamar ƴan matan amarya hannayen su na ɗauke da kaya niki niki a hannu, katan ɗin fanta da maltina kowanne uku uku, katan ɗin ruwan gora kamfanin "SWAN" guda biyar sai katan ɗin biscuits guda uku, sai jakan kwali mai ɗauke da hoto na da sunana ɓaro-ɓaro abin mamaki, sauran kuma ledoji ne bakake manya manya har guda huɗu.

A inda muke tsaye suka dire mana kayayyakin a gaban mu suna cewa, Ance mu kawo ma *UMMI ƘWARAS (Woman Leader)* suka faɗa da su, suna sassauke kayan a gaban Abulle.

Abulle ce ta amsa musu tana cewa inji wa kenan? Su kace,"Wai saƙon daga wajan Baban ta ne inji principal"

Abulle ta jinjina kai alamar gamsuwa tana mai sake duba saƙon da yawa kam."

Ko da muka soma buɗe Ledar farko abin da idanun mu suka gani shine ya sa mu kallon juna muna mamaki, wata leda ce cike da memo irin mai kaurin nan ma'ana mai tsada duk ɗaliban aji uku babu wanda aka kawo ma irin wannan, bangon memo ko in ce joter na ɗauke da danƙareren hotona wanda ni dai ban san yaushe nayi wannan hoton ba , Abulle ta sake ta buɗe leda ta biyu inda taci karo da "key holders" masu kyau na gani na faɗa wanda a cikin kwalayensu suke sai wani kyalli da sheki su keyi, key holder ɗin na ɗauke da sunana wanda aka rubuta da manyan haruffa wato: SALAMATU MUHAMMAD, muka sake wangale baki muna kallon kallon juna saboda gaba ɗayan mu mun ɗauke wuta.
Sake buɗe leda ta uku Abulle tayi anan ne muka ga Hand fan irin na gidan sarauta ɗinnan amma yana ɗauke da suna na shima wanda rubutawa a kayi kuma babu yadda mutum zai yi ya goge" sai kuma abin ya soma bani tsoro ko da yake dama babu wanda yayi magana a cikin mu har yanzu.

Leda ta huɗu kuma cike yake da kayan makulashe "chocolates" ire-iren wanda ɗan binni ya taɓa kawo mun" amma wannan kam yaci uban wancen yawa saboda wallahi ko wani box yana ɗauke da chocolate akalla sun fi ɗari a ciki,. wannan karan kafafuwana sun kasa ɗauka ta, hakan yasa na nemi waje na zauna daɓas da ɗuwawuna ina ƙare ma kayan kallo.

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now