31

38 3 14
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 31

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
KATSINA STATE
JIBIYA, Garin gado

Kasancewar tsakar gidan namu babu kowa duk muna kunshe cikin ɗaki, mazan kuma duk suna Fadar Mai Anguwa hakan yasa waje yayi tsit baka jin motsin komai sai na akuyoyi da kaji, wannan ne ya bashi damar shigowa cikin gidan kai tsaye Allah kuma ya ba shi sa'a ya ci karo da abin da ya zo nema a tsakar gidan.

Aarif na ta faman wasa da ball ɗin sa, yana wurga ta sama sai ya chaɓe, idanuwan sa suka sauka akan *UMAR*

Umar ya sanya hannu ya kirawo Aarif , Aarif bai yi tunanin komai ba yaje wajan Umar har da murmushin sa, ya ɗauki Aarif yana masa wasa, hakan ne yayi daidai da fitowar Ummi daga ɗakin Mama tana sauri sai taci karo da su.

Bance kiyi magana ba, kin san dai baki isa ki hanani ɗa na ba ko, idan kuwa ki kayi gigin hanani ɗa na wallahi sai na miki abin da duniya ma  sai ta buga labarin ki.

Cike da bacin rai na ce,"Ai labari an riga an gama rubutawa sai dai kuma kai ka saurari makomar ka mugu azzalumi mai son kan sa kawai ka ajiye min ɗa na nace, na faɗa da karfi, hakan ya sa duk matan gidan suka fito kowa yana cewa lafiya UMMI sukayi tozali da Umar wanda yake rike da Aarif a hannunsa.

Mairo ta dafe kirji tana cewa,"UMAR yaushe ka dawo?

Yayi murmushin mugunta ya ba Mairo amsa,"Dama ina nan ai ba tafiya na yi ba"Yanzu ma na zo ɗaukan *Ɗa*na ne, na tafi da shi kuma babu wanda ya isa ya hanani wallahi"

Kalmar Ɗa daya faɗa ita ta girgiza tunanin duk mutanen dake tsaye a cikin gidan, tunanin dama *UMAR SHINE MUTUMIN DA YAYI SANADIN HAIHUWAR ARIF*

Muryar abulle ita ta dawo da su daga trance ɗin da suka shiga yayin, Tana ɗakin Mai dawa, muryar ta ya nuna alamar kuka ta fara magana tana  fitowa daga cikin ɗakin, ta tsaya dai dai sai tin inda Umar yake, ta cigaba da cewa.

"Wallahi Wallahi Wallahi!! ko kutu bata isa ta baka Aarif ba, duk faɗin duniyar nan babu wanda ya isa ya raba ni da Ɗa na Aarif sai UMMI, Tayi murmushi mai nuni da alamar mugunta ta kira sunan sa Umar kai tsaye babu ko Yaya sannan ta ce,"Mara mutunci idan kuwa kace zaka karɓi Aarif ta karfi to ina mai tabbatar maka da cewa wallahi za kayi na dama domin kuwa Aarif ba na ka bane, ka a je min ɗa na kayi tafiyar ka salin alin kafin na aikata maka abin da sai kayi danasanin tako kafafuwan ka ka shigo wannan kauyen mugu azzalumi, shege ɗan iska, tir da haihu............Mama tayi saurin toshe wa ABULLE baki tana cewa "Haba mana Abulle yau kece da zaki haka haba mana"

Kuka ne ya kwacewa Abulle ta kwanta jikin Mama tana mai da numfashi sama sama.

Mama ta ce,"Hakika lamarin nan babba ne, sai dai mu lallaɓi yaran nan su sanar damu gaskiyar al'amari......dai dai lokacin da su Baba suke shigowa..duk suka iske mu tsaye hankalin kowa a tashe, Baba ya ce "Meke faruwa ne anan?

Mahmud yayi saurin zuwa wajan Umar yana rungume sa yana cewa,"Ɗan uwa zuwan yaushe kuma, ka dawo kenan ban da labari.

Umar ya aje Aarif yana cewa"Kayi hakuri bro, akwai abin da ya kawo ni kuma yanzu nan zan gama na tafi, ba jimawa zanyi a garin ba....sannan kuma na zo ɗaukan Ɗa na, I need him beside me" ya faɗa yana hararan su Abulle da Ummi.

Mahmud ya nuna alamar mamaki don bai yi tsammanin jin kalmar Ɗa daga bakin Umar ba, dama Umar na da Ɗa ne, ko ko dama shi yayi wa Ummi fyaɗe ne,to amma shine bamu sani ba tun lokacin baiwar Allah akayi ta mata sharri....  Mahmud ya zurfafa cikin tunani sai yaji Umar na magana.

Umar ya ɗan kalli in da Abba yake yayi dariyan ƴan iska irin shi ɗan duniyan nan, sannan ya ce,"Alhaji Abubakar Jafaru Chubaɗo ko?

Abba ya ce "Yes suna na kenan, sai dai ni ban gane ka ba"

"Ahhhhh inaaa ai ba zaka sanni ba, kana da suruka Aishatou ko in ce kana da suruka ƴar daba" Umar ya faɗa yana murmusawa.

S.Chubaɗo ya nufe shi zuciyar shi na yi masa ƙuna zai yi magana kenan abokanan sa guda biyu suka rirrike shi suna cewa "Nooooooo kar ka biye mai please"

Dallah dube sa kamar wani zaki, me zaka iya yi, bayan baka kula da abubuwan da suke faruwa daku duk tsahon shekarun da kuke zaune da macuciya, ka bari zakanyar matar ka tana muku farauta a cikin gida, to bari kuji na faɗa muku, idan kun ɗauki shawarata gwara ma kuyi sauri ku koma gida don kuwa idan ku ka jinkirta kuna iya iske abin mamaki....ya cigaba da cewa Password ɗinka Alhaji Abubakar na asusun bankin ka wanda yake ɗakin kwanan Matar ka *333SABCHUBAƊO333*

Mamaki yasa Mamie durkushewa nan kasa tana dafe cikin ta don kuwa wannan asusun nasu yana ɗauke da duk wani tarin dukiyar su, Wani babban asusu ne da aka gina musu ta cikin gini wanda yake bayan wardrobe ɗin Mamie, an sanya mishi wani slicing door black wanda baya buɗuwa sai da password, komai ana iya sanyawa aciki har kaya ma idan kaga dama, amma su dukiya suka zuba.
Takaddun filaye ba adadi, Takaddun gidaje ba adadi, Takaddun company guda ashirin sai zallan dollars wanda zasu kai akalla bandir ɗari uku, Sannan sai zallan kuɗin nijeria wanda ya tasanma billion dubu dari biyu da hamsin, ragowar suna banki.

Mamie ta daga jajayen idanuwan ta wanda sun riga da sun fara zubowa da kwalla, bawai tana kuka don rasa tarin dukiyar nasu bane, aa sai don cin amanar da Aishatou tayi musu, ashe ba son su take tsakani da Allah ba dukiyar su take kwaɗayi, lallai Shatou ta tabbata butulu, ta kalli Abba wanda yake jikin S Chubaɗo yayi niyar faɗuwa sai Sadeeq suka taro shi yana ta zufa suna share masa.

UMAR ya gama fallasa duk sauran abin da yazo fallasawa sannan ya ce,"Karin bayani kwanaki mun haɗa baki da ita Shatou akan zamu sanya muku guba acikin abincin ku, gubar nan da muka zuba ranar da Alhaji Abubakar Jafaru Chubaɗo ya dawo daga London, mun zuba a komai na ci da sha amma saboda wannan yarinyar tana tare da ku ita ta bata mana shirin mu, mind you da yanzu duk kun zama shekakku saboda gubar nan ba karamin dafi bace musamman na sanya aka kawo mun ita daga lagos..... yayi dariyar mugunta sannan ya cigaba da cewa "Shatou ta nuna bata bukatar support ɗina, shiyasa naga gwara nazo na faɗa muku cewa kuna tare da killer a cikin gidan ku...In kunne yaji gangan jiki ya tsira,uhmmmm by the way mutanen gidan nan ina mai son sanar da ku cewa "Ni nayi sanadin samun cikin Aarif, so Ni ne dai Mahaifin Aarif don haka zan tafi yanzu amma ku sani ina kauyen nan anjima ko gobe zan dawo ɗaukar Ɗa na....sai da ya karasa wajan Aarif yayi masa kiss a peck sannan ya ce,"Sai anjiman ku masu gida da bakin gida.

Mahmud dake gefen sa ya cafko hannun sa yana cewa" Umar Yaushe ka zama mugu ne ban sani ba??

Umar ya sheke da wata dariya sannan ya ce,"Bro ina respecting ɗinka, So please kar ka shiga rayuwa ta ka gane ko" Umar ya galla masa harara ya fizge hannun sa yayi gaba abin sa.

Mahmud ya juya yana kallon Mairo don yana bukatar karin bayani game da hakan.

Abba ya ce,"Mamie anya ba zamu kama hanyar Bauchi ba yanzu?

Baba ya ce,"Abba hakuri za kuyi, gaggawa bai da kyau, ko kun kama hanya yanzu dole sai kunyi dare kuma baku san abinda take shiryawa ba agidan.

S.Chubaɗo yayi murmushi ya ce,"Abba ku kwantar da hankalin ku na riga da na canja password ɗin, kuma ni na canja abincin ranar shiyasa da muka ci wani abu bai same mu ba.

Mamie ta ce "how comes, you did all this without our knowledge son?

Mamie is a long story mu zauna na sanar daku yanzu.


______________________________________
STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now