36

52 0 0
                                        

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 36

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
KATSINA STATE
General hospital

WASHEGARIN SALLA BABBA

Karfe bakwai daidai agogon dake cikin reception ɗin ya buga, yayin da duk zuri'ar Mai Anguwa suna asibitin, wasu suna cikin reception wasu suna waje, an fito musu da corps ɗin Mummy da Daddy.

Babban Accident and Emergency ɓangaren male ward muka nufa,mutane ne mara sa lafiya gasu nan abin gwanin ban tausayi wasu karaya a kafa, wasu a hannu, wasu an yayyanke musu kafafu wasu babu hannaye, wasu konewa su kayi, wasu kuma gasu dai a kwance ko mosti basayi numfashi ma da taimakon oxygen suke numfashi.

Mikewa mu kayi har karshen ward ɗin nan muka iso gadon mara lafiyan, wanda mu kaji likita nayi ma su Mai Anguwa bayanin cewa,"Spinal cord ɗin sa ya samu matsala ba zai kara mikewa tsaye ba, sai dai a kwance kullun.

Ƴan uwan sa na jini kuka kawai su keyi, Mai Anguwa ma dai kallo ɗaya yayi masa amma sai da ya zubda masa hawaye.

Haka ake ta shigowa ana duba sa ciki har da su Ummi da Abulle da mazajen su, Yaya Mahmud kam dama suna asibitin tun safe hankali tashe saboda Umar ɗan uwansa ne tare suka tashi kuma amininsa ne zugan abokanaye ne shine halayen sa suka sauya.

Ni Ummi na jima tsaye ina kallon yadda Umar ya kasance lokaci guda kamar bashi bane yazo jiya yana ta faɗan maganganu barkatai, yau kuma gashi kwance bai ma san su waye a kan shi ba...ko wannan aka barka dashi Allah ya nuna maka iznaa sai dai muce Allah yasa mu dace.

Abulle ta ce,Na yafe masa baba, ku duba halin da ya shiga a ɗan kankanin lokaci wallahi na yafe masa, Allah ya yafe mana gaba ɗaya, su Mummy kuma Allah ya gafarta musu yasa sun huta.

Mansura kanwar Umar tayi aure a Abuja, dama ɗan abokin Daddy ne ta aura, ita ma tazo da mijin ta sun duba yayanta, sannan suka tsaya ayi jana'iza da su, sai kanin Umar Aliyu wanda dama shike kula da kasuwancin Daddy yanzu haka shine a yake yi masa jinya...likita yace wata kil idan aka fitar da shi ƙasar waje ya mike har ma ya taka.

Anyi jana'izar Daddy da Mummy ana ta karɓan gaisuwa sai dai muce Allah ya musu rahama, Allah ya gafarta musu.

Satin Umar guda a hosptal aka dawo da shi gida Aliyu ke kula da shi...Umar bai da aiki kullun sai kuka yana hawaye, kullin maganar sa ɗaya Allah na tuba, Allah ka yafe min.

______________________________________

Dama Sadeeq da Zunnu sun ɗauki Aunty Mairo da suka je asibiti suka biya Market suka ce mata ta haɗo ma kowacce Amarya kaya na gani na faɗa haka aka haɗa akwatuna.

UMMI dozen uku Abulle ma dozen uku babu kaya masu tsada wanda ba'a siya ba, daga kan laces, swiss laces, kamfala, gezner, atamfa ƴar yayi me golden, da latest chiganvy, super wax ƴan dubu ɗari ɗari haka aka zuba kaya na gani na faɗa a kowanni akwati, kana nan kaya kama daga kan latest gyalluluwa, hijabai jilbab, takalma latest one da hand bag dozen dozen.
Sannan ta siyo ma kowacce ainahin lifayan maiduguri kala ukku ukku, da turarukan wuta masu tsada sai humra.

Akwati dai da aka kawo ana ta zuwa ana kallon abin da ba'a taɓayi ba, wanda labari har yaje kauyu kan makotan Garin gado.

Baba da Mai Anguwa suka ba ma Yaya Mahmud kuɗi shi ma ya sa wani abu daga cikin aljihun sa, kuɗi suka tashi mil biyu da rabi aka shiga garin katsina aka zabo furnitures na ƙasar waje masu kyan gaske, da kayan kitchen babu abin da basu siya ma kowacce Amarya ba.

Mairo kuma tayi magana da masu yin cin cin da dublan ɗin biki, da alkaki, tace ayi ma kowacce Amarya cikin bambum ruwa babba, bibbiyu abin dai na masu kuɗi ne fa, ba'a cewa komai masu abu da abin su.

Mahaifin Zunnu kwana ɗaya suka kara a garin ranar ukun sallah suka tafi da Amarya Bauchi.

Unguwar federal low cost suna isa layin su motoci ne makil ana ta biki a kofar gidan su rumfa aka sanya wanda abokanan Mahaifin Zunnu da kuma ƴan uwa da abokan arziki wasu na cin abinci wasu kuma na jiran isowar Amarya, Ango da Uban ango.

Babban gidane don Mahaifin Zunnu shima ba baya ba in dai arziki ne to fa akwai shi.

Ƴan uwan sa da ƴan mata matan gidan duk suka fito ɗaukar Amarya sunyi mamaki matuka da ganin irin shigar dake jikin Amarya Abulle saboda su an ce musu ƴar kauye ce amma ko kaɗan ba su ga alamar kauye a tare da ita ba.

Bayan Amarya ta huta an kwana washe gari aka shirya ta aka ɗauke ta sai gidan ta wanda yake bayan airport cikin bauchi sabon gida ne ginin zamani, four bedroom flat da two palour, sai dinning da kitchen babu abin da ba'a sanya ba agidan.

Ƴan uwan Zunnu dai sun sha mamaki ba kaɗan ba don kuwa sam ba suyi tsammanin ganin garar da akayi wa Abulle ba, kuma dai Amaryar ba laifi akwai kyau tubar kalla, dangin Zunnu sun amshe ta hannu bibbiyu ba karamin ji da ita suke ba, haka suka gyara mata gida tsab suka sanya turaren wuta, suka shirya ta sannan suka bar gidan misalin karfe shidda kowa ya tafi nan abokanan ango suka rako ango har palon Amarya suka musu nasiha sannan suka kama hanya suma sukayi musu sai da safe.

Ni ma dai Diela nayi musu sai da safe na janyo ko kofar ɗakin na dawo tsararren falon nasu wanda yaji kayan alatu anan na hau kan kujerar royal sai kyalli ta keyi na kwanta tuni bacci yayi a wan gaba da ni.

______________________________________
THE NEXT DAY

Ni Diela ina tashi daga bacci na buɗe idanuwa na sai kuma na ganni a Garin gado, gidan su Ummi misalin karfe Shidda na safe sun gama shirya furnitures da kayayyakin Amarya a wata babbar mota aka fito da Amarya UMMI sanye cikin lifaya sai kuka ta keyi suka shiga motar S.chubaɗo, shima yana seat ɗin baya, biyu daga cikin abokan sa ne suke tukashi.

Mamie da Abba da Aarif suna mora ɗaya sai Motar Yaya Mahmud shi da Mairo zasu raka ƴar kanwar su.

Babu wanda ya bisu don su Mairo ma a motar mijin ta zasu bi bayansu amma ban da yara shi ma dai don suje suga gidan Ummi da na Abulle.

karfe uku daidai suka iso GRA kofar gidan su S.Chubaɗo an shigar da Amarya ita da Mairo, Sadeeq kuma ya karbi keys ɗin sabon gidan shi da yake nan cikin GRA ɗin ba nisa dasu Mamie, Ya jagoranci motar kayan shi ya buɗe kofar suka shiga ciki.

Ni Diela ban san lokacin da alkalamina da littafi na suka suɓuce ba suka faɗi kasa tsabagen kyau da haɗuwar gidan Ummi, lallai an zuba dukiya waje kaɗai na gani ina ga ma an shiga ciki...na ce Ummi Allah ya baku zaman lafiya yayin da naga ana ta jera kaya ba'a jima ba kaɗan Mairo ta biyo su ita ta shirya duk wasu abubuwa na mata da sauran su sai misalin karfe goma na dare masu saukar alkur'ani suka zo don kwana uku zasuyi suna sauka sai sunyi sau uku.

Washe gari Mairo da Mahmud suka je gidan Amarya Abulle, Hummm kun san dai yadda gidan amare yake gwanin ban sha'awa to haka gidan Abulle shi ma ya kasance duk in da suka sa kafa kanshin gidan masu kuɗi da kanshin turare ke tashi abin dai ba'a cewa komai...Sun ci sun sha sunyi hani'an, sai dare suka bar gidan, Washe gari Mamie, Abba, Yaya Mahmud da Aunty Mairo sai Ɗan Mamie Aarif suka raka Ummi gidan ta suka musu nasiha mai ratsa jiki sosai, karfe takwas suka baro gidan aka bar Amarya da Angon ta suna marmarin juna, nima dai sai da safe nayi don idan nace zan tsaya ganin soyayyar nan wallahi alkalami na bazai iya rubutawa ba.

______________________________________
Ina AISHATOU?

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE

UMMI KWARAS ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora