13

53 3 2
                                        

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 13

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

_____________________________________
THE NEXT DAY
FRIDAY
______________________________________

Yau da farin ciki na tashi daga bacci,na fito daga ɗakin Mai dawa na tsaya a barandar ɗakin ina ƙare wa mutan gidan namu kallo, suna ta faman aikin biki, masu kunu da kosai nayi,masu gyara kayan miya dangin su tumatir,tattasai,tarugu, ganyen albasa da albasa, kowa da abin da ya keyi, na kai akalla tsahon minti ashirin ina tsaye a wajan, tunanin me ni keyi ohhhoooo.

************
Da sassafe, misalin karfe takwas na safe yazo kofar gidan mu, Allah ya taimake shi ya samu wani yaron malam(almajiri) wanda da alama ruwa yake ɗebo mana, ya bama yaron sako ya ce ka kaiwa Ummi kace inji Sadeeq.

Ina nan tsaye yaro yamin sallama, na amsa cike da fara'a ta yaron ya miko min leda baka babba guda ɗaya yana min bayanin wanda ya aiko shi.

Na amsa na shiga na ce,"Abulle hinn Ɗan binni ya bayar wai a kawo mun.

Abulle ta karɓa tana cewa Lahhh Haba kawo muga miye a ciki ta faɗa a lokacin da take buɗe ledar, wani ɗan akwati ne karami kamar abin agogo, sai wani babban gyale fari mai kyau da tsada a cikin ledan sa, sai kayan shafa masu tsada saboda ko na akwatin Mairo bai kai wannan tsada ba, acewar Mansura saboda tasan kayan binni, ita kanta tayi mamakin kuɗin da aka kashe a kayan, sai wani roba babba robar cike yake da kayan zaki irin na ƴan binni *chocolate* da sweet da yawa. na sake baki ina ƙare wa kayan kallo don wallahi ni dai ban taɓa ganin irin shu ba, Abulle ta ce,"Ummi ɓoye mana wannan kayan zakin anan ɗakin sai mun dawo gobe daga kai amarya zamu sha.

Na taɓe baki, ina kokarin buɗe karamin akwatin, Ma shaa Allah sarƙa, warwaro da agogo ne masu kyau suna ta kyalli.

Mansura ta buɗe baki tana cewa kai! Ummi wai wannan bawan Allahn ɗan ina ne, amma da alama yana da kuɗi, kin san tsadan kayan nan kuwa.
Nidai ban ma ce mata komai ba, arai na, na rasa dalilin da yasa Ɗan binni yake siya min abubuwa. babu mai amsa min.

Karo na farko da na ji zan iya anfani da abin da ya fito daga hannun Ɗan binni hakan ya tunamun ƙwaras ɗin daya bani wancen lokacin, ba shiri naje ɗakin Mama na ɗauko ajiyar da tafi wata biyar kayan sunyi kura na buɗe na ɗauko takalmin na mai da sauran na ɓoye sannan na kaiwa Abulle takalmin na ce  "yau zanyi amfani dasu Abulle"

Abulle tayi murmushi ta ce,"Tun yaushe nike bin ki, na ce Ummi ki ɗauko takalmin nan ki sanya, kinki wallahi da sai dai anjima kiga na sanya nawa wanda Yaya Ibrahim ya siya min.

Na ce, Uhmm to gashi nan dai yanzu na ɗauko toh, Mansura ta ce,"ku kam kuna son Ƙwaras, ni fa nafi son takalmi wanda ba ƙwaras ba,

Na ce"Takalmin ƙwaras musamman irin wannan wanda saman shi a rufe yake yana da kyau fa, wata kila don ke a binni kike shiyasa baki so, kun san ku ƴan binni ba komai yake muku kyau ba, ku komai naku daban ne. Tayi dariya abin ta kawai.

UMMI KWARAS ✔Onde histórias criam vida. Descubra agora