16

46 3 5
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 16

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye

_____________________________________~~MAFARIN KADDARAR RAYUWATA~
~UMMI ƘWARAS~

~KASTINA STATE~
~SHAGARI~

Mairo kawai ta girgiza kai ta ce,"To ku taho mu je" Yan da tayi maganar wallahi sai ta baka dariya da tausayi, mu kam ko a jikin mu"

Muka bi ta a baya muna ta kalle kallen falon na ta, Hakika falon ya tsaru iya kar tsaruwa Yaya Mahmud ya zuba kaya masu tsada na gani na faɗa a gidan na su, ba za a taɓa cewa daga ƙauye aka ɗauko Mairo ba saboda yadda ta canja a shekara uku kacal tayi kiba, tayi haske, tayi ƙyau, ta zama babbar mace kamar dai ba Mairo da aka ɗauko daga ƙauye ba, ga shi kuma hankalin ta a kwance sosai.

Kwanan mu biyar a gidan amma mun saba da rayuwar tasu kasancewar muma mun taba rayuwar "boarding school" makarantar kwana, muna da "experience" a wani abun muna da ilimin mu, "Hmmmm"
Yaya Mahmud ya shirya mana kayan mu da kan shi don shi yana da daɗin mu'amula sosai yake sakewa da ƴan uwanshi.
Da kan shi ya kaimu gidan su Mansura a nan muka haɗu da ita ba karamin dadi gidan nasu yayi mana ba, kwanan mu biyar aka mai da mu, Mansura na cewa In sha Allah ita ma za ta zo ta mana kwanaki kafin mu tafi.

A kullin da safiyar Allah muna ta shi da asubahi muyi sallah, sa'annan muyi kararun Alkur'ani mai girma ni da Abulle wanda Yaya Mahmud shi ke koya mana da daddare sai muyi bitar karatun" Har da Mairo duk dama ita ta sauke abin ta" zuwa karfe bakwai da rabi zamu gyara ɗakin mu, sa'annan mu fita mu gyara mata falon ta,ɗakin ta mu wanke bayi duk dama tana da mai aiki amma mu babu ruwan mu kowa yana da aikin da yake yi, Mairo kuma na kitchen tana shirya abincin kumallo, zamu bari sai mun karya, tukunna Yaya Mahmud ya fita sa'annan muyi wanka mu kwanta, ko mu zauna muyi ta hira da Mairo muna bata labarin makaranta tai ta cin dariya.

Da wannan rayuwar ne na fara koyon girki wajan Mairo ashe ya sanya ta a makarantar koyon girki wanda a yanzu haka Mairo babu abin da ba ta iya girkawa ba, hakan yasa muma duk girkin da za ta yi sai ta kira mu ta nuna mana.

Wata ranar Lahadi satin mu biyu da kwana biyar lokacin saura mana sati ɗaya mu koma makaranta.
Mu kayi baƙo *Yaya Umar faruk* ranar ya kawo musu ziyara suna zazzaune a falo suna hira da Yaya Mahmud.
Mu kam muna kitchen muna girki, bayan mun gama ne aka shirya komai a "tray" abin ɗaukar abinci, ni da Abulle mu kaje falo muka aje musu" mun gaishe shi bai yi mamaki ba saboda tun a gida aka sanar da shi cewa Abulle ta zo, sai dai shi dama akwai dalilin daya sa yazo ya tabbatar da ganin nasu kuma Alhamdulillah ya gani"

Muka zauna muma a falon ana ta hira ni kam hankali na baya kan shi, amma kuma sai kallo na yake yi duk inda na bi sai ya kalle ni, ban lura ba sai da Abulle ta biyo ni kitchen alokacin da muke kwashe kayan abincin muna kai wa ciki"
Tana mun gulma, ni kam na taɓe baki ina cewa "Uhmm shi ya sani ko me zai kalla anan"

UMMI KWARAS ✔Место, где живут истории. Откройте их для себя