05

65 6 2
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 5

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Da ƙyar na iya ɗaga kafata ɗaya ahankali ni ke tafiya kamar wacce bata da jini a jiki har na isa wajan mairo na zauna nasa hannu biyu na amshi jaririn wanda ashe namiji Mama ta haifa kyakkya dashi kuwa na mai da kallo na zuwa ga Mama da naga ana ta faman yi mata fiffita alamar tana da rai kenan ajiyar zuciya na sauke na kalli Mairo da idanuwanta suka ciko da kwalla Ban san lokacin da nima na wan suka ciko da kwallan ba har na fashe da kuka.

*karo na farko kenan a rayuwa ta da na fara zubda hawaye don ganin halin da Maman mu ta shiga*

Mai gidan dawa ita tai ta faman rarrashin mu hakan ya sa na fita na bar gidan da kayan makaranta a jiki na ina tunanin Abulle a rai na ina cewa da tana nan da ta taya ni kuka saboda itace abokiyar komai nawa ina tafiya ina hawaye har nazo dai-dai kwanar rumfar Mai Anguwa inda su Baba suke zama daga cen nesa kaɗan na ɓuya jikin wata ƴar bukka na iccen kara ina leken mutanen dake zazzaune saman tabarmar Mai Anguwa, su biyar ne daga ganin su baki ne saboda yanayin shigar dake jikin su shiga ce ta alfarma wanda ƴaƴan Mai Anguwa ne kaɗai suke irin wannan shiga suma idan sun dawo daga binni, ta ɓuli ɓulin bukkan nike hango kowannen su yayin da suka tashi da alama Mai Anguwa zai kaisu wani waje ne saurayin dake tsakiyan samari biyar yana sanye cikin sabuwar shadda ruwan toka sai ƙyalli ta keyi shi idanuwa na suka hasko min fuskar sa
Ya ilahi! idanuwa na suka hango min *Ɗan binni* Mai Anguwa na tafiya suna biye dashi abaya har suka bace wa gani na, na ɗan karya kwana ina tambayar kai na to shi me ya kawo shi ƙauyen mu kuma, Ina tunani har na iso wajan wani babban dutse wanda yake cen bayan gidan Mai Anguwa anan muke yawan zama ni da Abulle aduk lokacin da aka aike mu to nan muke gudowa mu ɓuya mu zauna muyi ta raira wakar hausa wanda ƴan mata ke rairawa a dandali lokacin gaɗa da sauran su, kasantuwar wajan akwai bishiyoyi wanda suke sanya wajan yayi damshi damshi tare da ni'ima mai dadi na zauna na cire takalmin makaranta da safa na cire hijabi na gashin kai na ya baiyana a waje wanda Mairo tai min kitson calaba ya sauka har gadon baya na duk da na kama da abin kama gashi wanda Yaya mahmud ya siya ma Mairo tun daga binni ta bani ɗaya, ahankali na soma raira waƙa

*ke ƙawa ƴar gayyar soɗi kina inaaaa
Ina ta kewanki Abulleee ki taho
guna muyi gaɗa*

Ina waƙar ina tuna halin da Mama take ciki hakan yasa nai ta zubar da kwalla kaman an buɗe famfo ban ji motsin tafiya ba ji nayi kawai an miko min farin ƙyalle irin na ɗa zu shi ma ɗin dai sai kamshi ya keyi hakan yasa nabi hannun da ido har na sauke idanuwa na a fuskar sa wanda shima ya zuba min idanuwan na sa ko ƙyaftawa ba yayi.
Na sha majinar hanci na alamar na ci kuka sosai hakan yasa na janyo ɗayan kyallen a aljihun wando na na share fuska ta da shi duk da kuwa yayi datti nayi hakan ne gudun kar na sake ɓata masa wani kyallen.
Ya kawar da kansa gefe sannan ya samu waje gefe na ya zauna yaja numfashi ya ɗau tsahon minti biyu ka fin yayi gyaran murya ya ce," Miye sunan ki?
Ahankali na amsa masa da, "Ummi"
Ya ce, "Na yanka fa nake nufi? Ba tare da na kalle sa ba na ce, "Suna na *SALAMATU*
Murmushi naga yayi wanda ya kara bayyana kyawun kwantattaccen sajen dake fuskar sa sa'annan ya dube ni *karo na farko kenan da naji bugun zuciya saboda irin kallon da yai min* Ya ce, "Me ki keyi ne anan kuma wakar me kike rairawa haka ? Fuskata babu yabo babu fallasa na ce da shi," Ina raira wa Abulle waka ne nan kuma shine wajan zaman mu ni da Abulle sannan kuma ina tausayin halin da Mama na ta shiga ne bata da lafiya ne"
Ya ɗan gyara zama ya jinjina kai sannan ya ce, "Allah ya bata lafiya"
"Amiin ya rabbi" na amsa masa ina mai wasa da yatsun hannu na ashe kallo na ya keyi sai naji ya ce, " Ki sanya hijab ɗinki ko babu kyau zama babu kallabi" ban mishi musu ba na sa hijab ɗin sannan na tashi na nufi inda muke carapke da Abulle na share wajan da kara na ɗebo ɓoyayyun duwatsun mu wanda suke ɓoye a cikin leda na zazzage duwatsun a cikin rami sannan na zauna na soma yin ƴar carapke ni ɗaya yana kallon yadda nike tayi ko ɗaya ban faɗi ba har na lashe ramin duka sai alokacin na saki ihun murna ina ce wa,
"A WINNN" Baki ya kama yana murmushi bayan ya fahimci *I won* nake nufi ina yi ina tafi da hannu biyu duk yana kallo na wanda ashe na sashi dariya sosai hakan yasa ya gyara zama ya cigaba da kallo na.

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now