29

33 2 10
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 29

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
KATSINA STATE
JIBIYA, Garin gado
ABULLE

Ina kokarin mayar ma Aarif da wando bayan yayi fitsari, Abulle ta ce,"Ina zaune a ɗaki, Harira ta shigo gidan mu da gudu ta sanar dani kin dawo Ummi.

Na ɗan matse hawaye na ban san lokacin dana rugo da gudu na rungume ta ba, ina kuka mai tsuma zuciya na ce,"Abulle na yi nadamar tafiya, da na sani da ban bi shawarar ki ba, Allah sarki Abulle na kalli yan da kika dawo.....na faɗa ina kara sautin kuka na, daga bisani Mamie ce ta lallashe mu tai mana nasiha sannan muka shiga ɗakin Mama ni da Abulle don akwai sirrin da muke son tattauna wa akai.

Abulle na ta wasa da Aarif karo na farko da taji zuciyar ta ta buga da son yaron,sosai Aarif yake ta kwantawa a jikin ta, har Ummi na cewa,"Kiga yan da Aarif ya sake dake ko da yake*BLOOD IS TICKER THAN WATER*

Ni dai Diela ban gane me Ummi take nufi ba, da wannan karin maganar nata, shin ko kun fahimce ta?

..Karshe ma anan gidan na mu Abulle ta kwana, Mai dawa na cewa,"Toh fa Ummi ta dawo za'a ɗaura daga in da aka tsaya,....Mairo ta ce,"Mai dawa kin manta soyayyar dake tsakanin Ummi da Abulle,Maman Halilu na gefe ta ce,"Wallahi ni har mamakin irin kawancen su ni keyi azamanin yanzu dai babu kamar su, dubi dai yanda Abulle ta lalace duk wai saboda rashi UMMI a tare da ita"

Mama ta ce,"Ku dai ku taya su da addu'a Allah ya basu mazaje na gari

Amin Amin, cewar Mamie da Mai dawa.

______________________________________
THE NEXT DAY

Mai gari musamman ya sa aka gyara wa su Abba gidan baki wanda yake bayan gidan sa "Gidan da su Ɗan binni suka zauna wancen lokacin , tsab tsab ɗakin da aka baiwa Abba da Yaya Sadeeq babu abin da babu har leda an sanya da sabuwar katifa har da zanin gado kasancewar ƴaƴan Mai Anguwa suna da arziki bai da matsalan wannan.

Abba yayi matukar jin dadi da karrama shi da su kayi, duk da bai taba zuwa katsina ba sai wannan karan lallai Abba ya yadda cewa Katsina ta dikko ce, kuma ɗakin kara"

Kasantuwar yau jajiberin sallah babba, sai hada hada ake yi masu zuwa kasuwar jibia suna hanya masu aikin gida suna ta kai, masu debo ruwa a rafi saboda hidiman gobe suna ta kai, Ana ta haɗa kan raguna ana sanya su a motar a kori kura suna ta kai wa zuwa jibia don cin kasuwar jajiberi.

Trailer biyu manya na ɗaukan kaya suka tsaya daidai kofar gidan Malam Muhammadu, Buhunhunan shinkafa, dana semovita, katan ɗin taliya da macaroni, akallah ba a lasari ba zasu kai Hamsin sune shake da motar.

Abba ya sanar da Malam muhammadu cewa shi yasa a kawo kayan abinci.

Abba ya ce,"Ina son a bawa kowani gida Shinkafa buhu ɗaya,taliya, macaroni da semovita kowanne katan ɗaya ɗaya

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now