11

46 4 15
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 11

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

_____________________________________
KATSINA STATE
JIBIYA, KAUYEN GARIN GADO.

Muna zaune a farfajiyar barandar ɗakin Mai gidan dawa muna ta faman shan rake, gefen mu su Halilu ne suke ta faman wasansu, cen tsakar gida kuma Mama da Maman Halilu ne suke ta kiciniyar haɗa wutar murhu suna niyar ɗaura sanwar dare.

Mai dawa na kwance saman tabarmar "kaba" wacce take shimfiɗe a gefen inda muke zaune, ta dube mu ta ce," Ni kam Ummi yaushe za'a tafi makarantar nan ne?
Abulle ce ta bata amsa don ni santin rake ma ya hanani magana sai faman lumshe idanu nike alamar zaki, Abulle ta ce mata,"Mai dawa ai ba yanzu ba da saura, saura sati biyu nan masu zuwa.
Na ɗan dago kai ina kallan Mai dawa bayan na kashe mata ido ɗaya sa'annan na buɗe baki na fara yi mata magana.
Uhmmm *Mai gidan dawa na*
Ta amsa da na'am shalelen Baba.
Uhmmm na ce ba ko kin kosa mu tafi ne Mai dawa?

Mai gidan dawa ta ce,"Uhm uhm kawai ina so na shirya ma tafiyar shalele ne saboda ranar ba karamin tashin hankali zamu gani ba ta karashe maganar tana niyar tashi daga inda take, da alama itama tsakar gidan zata, a yi sanwar da ita.

Na buɗe baki nayi magana da sauti mai kara na ce,"Ahayyyee waya ganni ni Ummi a makarantar kwana, su Mai dawa da Mama da sauran ƴan gidan suna ƙewa ta, ni ko a jiki na *Mahaukaci ya faɗa rijiya yace ni wanka na ni keyi*

Mama ta kalle ni irin ohhhh wannan yarinya sai kace taɓaɓɓiya, ni kam na kanne mata ido ɗaya na cigaba da datsar rake ina lumshe idanuwa ni ala dole zaki na ratsa ni , cen naji Mama ta ce,"Ummi ina ganin sai an fara kai ki asibitin kwakwalwa kafin a kai ki makarantar nan da alama hankali bai gama shiga jikin ki ba har yanzu"

Na zumɓura baki sa'annan na ce," Mama to ni yanzu me nayi na rashin hankalin to wai ? na karashe maganar ina bubbuga kafafuwa, wanda yin hakan yasa su Halilu da Harira fashewa da dariya, saƙon harara na aika musu da shi kafin na kara da wata dakuwar duka hannu biyu kuma yin hakan yayi daidai da shigowar Kawu Shafi'u wanda a take ya fara zazzagamin ruwan masifa " Ke Ummi bana hanaki zagi ba, Ummi me yasa duk abin da a kace ba'aso ki barshi, ke a lokacin kike yin sa, wallahi ki shiga taitayin ki zagi ba abu bane me kyau kina ji na"

Kai kawai na gyaɗa masa ina tura baki gaba, Har ya gaisa dasu Mama ya a jiye musu chefane sannan yayi hanyar ɗaki, ita kuma Maman Halilu ta wani biyoshi har da sauri ta keyi, na harari wajan da gefen ido na guda ɗaya na dawo da kallo na kan Abulle wacce take min dariyar ƙeta, ni fa shiyasa bana son ma ina haɗuwa da shi saboda faɗa, Kawu Shafi'u akwai faɗa sosai"

Na ce," Allah Abulle zamu ɓata yau"
Abulle ta ce waa ban isa ba Ummi ni kuma na ɓata da ƙawalliya ta, ai mana dariya uhm uhm ban isa ba.

Na ce,"To bani haƙuri!!!
Abulle da mamaki ta kalle ni sannan ta ce,"Ni nayi miki laifi ne?

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now