23

48 3 0
                                        

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 23

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
BAUCHI STATE
GRA
MORNING

Ina idar da Sallah na yi azkar ɗin dana saba yi, nayi karatun alqur'ani na akalla minti arba'in sannan na ta shi Aarif yana ta magagin bacci a haka nayi masa wanka na shirya shi na haɗa masa tea ya sha, alokacin karfe bakwai dai dai, Don haka nima shiryawa nayi muka fita tare sai da na fara sauke shi a school sannan ni kuma na tafi nawa school ɗin, kasancewar exam/jarabawa a keyi ba mu wani jima ba da ni da shi a school ɗin.

___12:30pm______
ABUBAKAR SADEEQ CHUBAƊO

Misalin karfe biyu muka dawo gida naci karo da Abba, Mamie da sauran ma'aikatan gidan da alama Abba tafiya zai yi saboda yadda naji anata Alhaji Allah ya sauke ku lafiya. Na durkusa har ƙasa na gaishe su, Karo na farko da naga fara'ar Abba, ban taɓa tsammanin haka halayan sa yake ba sai yau.
Ya kirani da hannu yana cewa,"Zo nan yar albarka, Mamie tamin murmushi tana cewa,"Ya kinan Ummi, Abba na kiranki.

Na taho ina murmusawa, Abba ya ce,"Mamie ta yi min bayanin ki Ummi, ban da isasshen lokaci yanzu saboda ina da appointment a london, but In Sha Allah idan na dawo zamu zauna ni dake kinji.

Na gyaɗa kai ina cewa,"To Abba Allah ya kiyaye ya kuma sauke ku lafiya.

Amin ya rabbal alamin cewar Abba yayin da yake yi ma wani sallama a cen bayana, waigawan da zan yi shine fa idanuwa na suka sauka akan kyakkyawan halittan nan mai suna ABUBAKAR SADEEEQ CHUBAƊO.

Tsaye yake, yana sanye da shadda ruwan toka da hula da agogo ya sanya takalma baki sau ciki, yayi matukar kyau, duk da ya sha jinya amma hakan bai sa fatar jikin sa ta canja ba, hakan bai sa shi yayi muni ba,tsahon shekarun da ya ɗauka bai ma san in da kan shi yake ba yana kunshe a cikin ɗaki kuma bugu da kari Mamie na iyakar bakin kokarin ta wajan kula da ɗan ta.

Yana yi wa Abba waving da hannu,at the same time yana masa murmushi, har Abba ya bar compound ɗin kowani ma'aikaci ya koma wajan aikin sa, Mamie ta shiga palour ta sannan ni kuma ina tsaye kamar wata kungi don har wannan lokacin idanuwana suna kan Ɗan binni. haka zalika shima.

Ya zura mata idanuwa kaman me nazarin wani abu,kallo yake ta bin ta da shi, Ummi ce ta canja haka, ya sake bin jikin ta da kallo, Sanye take da kayan makaranta, farin riga mai dogon hannu, sai buje/skirt shima fari amma yana da layi layin baki da ash iyakar sa gwiwa ya sha flitting, ta sanya karamin hijab wanda yayi matukar amsar kyakkywar round face din ta, abin da ya birge shi ganin ta sanya safa mai wando ta rufe duk illahirin jikin ta shigar uniform ɗin yayi mata kyau. Lallai Ummi ta waye da zaman da tayi a Birni.
Ya tuna wasu lokuta cen baya takan ce mishi, *Yaya ɗan binni yaushe zaka kai ni binni? Ni ina son zuwa binni in rayuwa a cen, wata zuciyar ta ce da shi yau gaki a binni Ummi*

Sai yayi murmushi ya sake kallon gefen ta yayin da yayi tozali da kyakkyawan yaro, yaron da kallon da yayi masa sai yaga kamar fuskar wacce ya sani amma ya kasa tuna in da ya santa, To fuskar wacece wannan yaron ya ɗauko?

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now