37

50 1 8
                                        

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 37

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
Ina AISHATOU?

Bayan kwana biyu da dawowar su Abba aka sanar da Mamie da Abba cewa Shatou na GRA police station Bauchi state, haka suka haɗu har da Sadeeq da Ummi suka je GRA police station.

Wata ce ta fito fuska duk a kumbure ba zaka iya gane asalin fuskar na ta ba, Mamie ta ce officer ina Aishatou ku kira ta mana muna ta jira tun ɗazu.

Ni ce Mamie baki gane ni bako, ta faɗa tana kuka Mamie da Abba suka kama baki suna mamaki, "Shatou kece kika zama haka"
Cewar Sadeeq.

Mamie ta soma zubar da kwalla don har yanzu bawai babu soyayyar Shatou a zuciyar ta bane, kawai dai halayenta ne da suka canja tun tuni shiyasa ta rage nuna mata so.

Abba ya ce,"Dubi halin da kika sanya kanki Aisha, wani irin soyayya ce bamu nuna miki ba, Aisha na ɗauke ki tamkar ƴar ciki na, ban taba banban taki da Sadeeq ba, amma sakayyar da zakiyi min kenan"

Mamie ta ce,"Ko ba komai Shatou ni yar mahaifiyar ki ce mai rasuwa, ta damka min ke hannu biyu, haka na rai ne ki tamkar ƴar dana tsugunna na haife ta, Shatou har yanzu ban yadda kin aikata abubuwan da naji da kunne na kin aikata ba tsabagen soyayya ta dake kenan, meyasa kika zaɓi wannan rayuwar Aisha, kin cuci kan ki indai haka kike son halayen ki to ko kowa ma sai ya guje ki" Mamie ta karasa tana kuka.

Sadeeq bai iya faɗar komai ba, illa mika mata wata farar takarda ya ce,"Kin min asiri na zauna ba uhm ba uhm uhm tsahon shekara biyar Aisha, Alamar ba kya bukata ta kusa da ke a rayuwar ki, ashe ba soyayyar asali kike min ba, ba damuwa na yafe miki dukkan abin da kikamin amma ba zan iya zama da ke ba amatsayin mata, na sake ki saki ɗaya kaman yadda musulunci ya kayyada, wannan sakayyar ki kenan" yana kai wa nan ya ja hannun Ummi ya bar station ɗin dama a motar shi suka zo don haka sun riga su Mamie isa gida.

Tun daga ranar basu kara komawa police station ɗin ba, ashe Abba ya biya kuɗin bellin sannan ya biya kuɗin da ake bin ta,amma kuma sai da suka kusa tafiya Umara sannan suka ɗauko ta, ta dawo gida.

Ashe akwai plan ɗin din da Abba ya keyi jira yake ya dawo daga Umara tukunna.

______________________________________

Duk jirgi ɗaya ya ɗauki ƴan garin gado,Mamie da Abba kuma dasu Zunnu da Sadeeq jirgi ɗaya suka hau, gaba ɗaya family har da su Mairo su kayi landing a ƙasa mai tsarki.

Sun yi ibada sosai, sun ji daɗin kasancewa acikin wannan yanayin har tsahon wata ɗaya. sannan su Baba da kowa ma suka dawo ban da Amare da Angwaye don su wata uku za suyi...daga nan ma Zunnu yace Malaysia zasu je, Sadeeq ya ce muma zamu biku Malaysia ɗin daga Malaysia sai muje London, ko ya kika ce *Salma* ya faɗa yana sha fa kumatunta da suka cika sukayi jazir a ƴan kwanakinnan.

*********

Shatou kullin babu abin da take sai kuka, da nadamar abin da ta aikata, uwa uba kunyar ƴan gidan, su Abba na dawowa daga Umara ta kara basu hakuri, sun hakura amma sun ce basu hana ta yin rayuwa tare da su ba, kawai dai baza a koma kamar da ba, Abba ya bata miliyan talatin ta ja jari.

Ta fara rayuwar ta ita kaɗai a wannan flat ɗin, ba shiri shatou ta koma ga Allah, har islamiyya ta shiga, kullin istigfari ta keyi saboda ta dade tana aikata muna nan abubuwa tun bayan da ta gane basu bane iyayen ta....yanzu kuma ta dawo hanya madaidaiciya, business na atamfofi takeyi anan gida, ga kuma islamiyya da take zuwa kullin safe da yamma.

Babu zato babu tsammani Abba ya kawo mata kati, da mamaki take karanta katin auran, ta daga idanu ta kalli Abba don tana son karin bayani akan hakan.

Abba ya ce,"Har yanzu ina matsayin Uban ki ne Aisha ina da damar ɗaura miki aure ga duk wanda ya kwanta min a rai, Aishatou kiyi fatan Allah ya baku zaman lafiya da shi kuma zan yi miki nasiha a matsayi na na mahaifin ki, Aisha kibi mijinki sau da kafa, aljannar ki tana tafin kafar sa, sai kin kyautata masa kafin zaki ga mai kyau a rayuwar ki"

Aishatou na hawaye ta kalli Mamie.

"Mamie ta ce,"Allah ya baku zaman lafiya" Ki tashi ki shirya ƴan uwan sa zasu zo ɗaukar ki, suna hanya.

Tana kuka tana haɗa kayan ta, ta shirya tsab, ta sani Su Mamie sun nuna mata gata fiye da kowacce ƴa mace a duniya, ta sani ta musu laifi ne  shiyasa take ganin sakayya, dukkan abin da zai faru da ita yanzu zata rungume shi hannu bibbiyu.

Masu ɗaukan ta suka zo, tana kuka ta shiga mota, Mamie dai daurewa kawai take yi tana ɗaga musu hannu har suka bar compound ɗin.

*****************
Abulle sunyi wata uku a saudiya suka sake yin wata biyar a Malaysia, sannan suka dawo Nigeria tana da tsohon cikin wata shidda 6month pregnancy....Zunnu duk ya ruɗe yana so ta dawo ta haihu kusa da Maman shi don ya san Maman shi zata bata kulawa sosai.

Allah cikin ikon sa ta haifo ɗa namiji, yaron kyakkyawa yaso yayi kama da Aarif amma shima yana da kyau sosai. Ɗa yaci sunan Mahaifin Zunnu wato Abdullah ana kiran sa *Shaheed*.

Su Aunty Mairo, da Baba Sa'adiyya da Mama, da Maman halilu har da zuwa suna akayi shagali sosai. kwanan su biyar suka koma Katsina.

______________________________________
KATSINA STATE
Labarin gaske

Garin gado dai ya bar tarihi sosai sanadiyar UMMI ƘWARAS.

Bayan dawowar su Mai Anguwa daga saudiya sai kauyen Garin gado da makotansu suka fara samun barazana daga bandits, kidnappers Barayin da suke shigowa da daddare su kakkashe mutane ko su tafi da mutane ko su tafi da dukiyoyi.

Amma abin da ke faruwa a Garin gadon sai ya zama kamar barazana don basa kashe kowa amma suna harba bindiga, kuma idan suka nemi abu ba'a basu ba su kan tafi da mutun walau su dawo da shi, walau kuma ya tafi kenan.

Gidan Malam Muhammadu ma an shiga sun tsorata su sosai wanda har sun yi niyar kashe Mama da Mai dawa amma Baba ya basu shanaye har biyu da buhunan shinkafa sanadiyar da yasa suka rabu da su, amma sun shai da musu cewa hakan ba shi zai hana su sake dawowa ba.

Haka zalika aka shiga gidan Mai Anguwa shima same abin da ya faru da shi, yanda su kayi ma Malam Muhammadu haka suka mi shi.

Dalilin da yasa mutane da yawa suka fara barin garin, a hankali ahankali suka rinka komawa Garin jibiya, wasu kuma su koma kauyukan da ke makota da kauyen garin gado.

Ana haka Yaya Mahmud da sauran yayan sa, da sauran ƴan uwansa suka haɗa kuɗi suka siya ma Mai Anguwa fili a garin Jibiya, su kayi gini cikin wata uku an gama don ba wani mai wahala sukayi masa ba amma ba laifi Babban gida ne sosai kuma ginin zamani ne.

Gefen Gidan Mai Anguwa Filin Malam Muhammadu ne wanda daga baya Abba ya tura ma Mahmud kuɗi aka siya masa, sannan shima aka tada gini.

Allah cikin ikon sa har aka gama gini kidnappers basu kara shiga gidajen su ba, suka kwashe ƴan kayansu gaba ɗaya suka kulle gidajen su, suka koma Garin Jibiya da zama.

Musabbabin barin su garin kenan wanda a yanzu haka idan kuka tambaya garin bawai labari bane babu wanda zaku samu kowa yayi kaura ya tashi a yanzu haka, wasu suna katsina, wasu suna Jibiya, ba haka aka so ba amma ya za'ayi.

Garin jibiyan ma a yanzu haka shima wani lokaci suna tsayawa a hanya zuwa katsina amma In Sha Allah, Allah shine mai tsare wa, kuma shine mai komai.

______________________________________
TAMBAYA
*Waye mijin Aishatou?*

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE

UMMI KWARAS ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang