*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 6STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
Ba tare da tunanin komai ba na ce, "To bari na ajiye ruwan na sanar da su"
Ya ce," To.Babu wani sallama kutsa kaina kawai nayi cikin gidan ina waƙe kaina da kirarin *UMMI ƘWARAS* hakan yai matukar janyo hankalin ma su zuwa barka ya yin da ni kuma nike ta harkar gaba ta, bayan na sauke tulun na rufe saman tulun da kyalle sannan na nufi ɗakin Mama kai tsaye ba tare da na gaishe da baƙin dake cikin ɗakin ba na hau zance abi na,"Mama ga ɗan binni zai shigo ya gaishe ki wai"
" Ni dai ban ga abin mamaki ko abin kallo acikin maganar tawa ba amma yadda naga kowa ya ƙura min idanu wa shine dai abin mamaki agare ni" na kyafta idanu wa na na sake buɗe wa sannan na mai da kallo na izuwa ga Mama na ce," Mama na ce mishi ya shigo babba ne fa!Cikin za fin ciwo Mama ta gyaɗa min kai kawai, na fita ina murna ina zuwa kofar gida na same shi zaune a teburin Mal.Habu suna datsar rake shi kuma yana ta faman taya su surutu da alama santin rake yake nayi murmishi, kai tsaye na same shi na ce," Wai ta ce ka shigo, Ya tashi yana kakkaɓe kayan jikin sa sai da ya cire gilashin fuskar sa sannan muka shiga gidan, duk wanda ɗan binni ya gani sai ya duƙa yayi gaisuwa abin har ya soma burge ni na kaishi har ɗakin Mama suka gaisa cikin mutunci da girmama wa har ya ɗauki jaririn mu yana masa wasa, a take awajan nai masa iso wajan Mai gidan dawa da Maman Halilu sai su Halilu da suke ta faman wasa a tsakar gida, daga bisani yai ma kowa sallama da fatan Allah ya karawa Mama lafiya shi kuma yaron Allah ya raya shi" Mama tai masa godiya sosai sa'annan ya fita na bi bayan sa, sai ga shi mun yi kachiɓus da Mairo ta dawo da ga aika dama ita kaɗai ce ba su gaisa ba na matsa dai-dai kunnen ta na ce,' Mairo hinn ɗan binni nan wanda nai ta miki taɗin shi jiya" Mairo ta murmusa ta gaishe shi cikin girmama wa da fara'ar ta sannan ta shiga cikin gida.
Ya dube ni ya ce," yanzu na san Baba, na san Mama, Mai gidan dawa,Maman Halilu da kuma ke, saura kuma wa?
Na yi murmushi na ce," sai kawu na kanin Baba shi baya nan ne yana gona "
Ya jinjina kai sannan ya ce uhmm to ni zan koma wajan abokanai na, ki koma gida kinji.
Na gyaɗa kai ina ce wa," To sai gobe kenan" Ya ce," Eh, amma karki manta gobe ranar tafiya makaranta ce saboda haka ki tabbar kin je school kina ji na" yayi magana ya na ɗan kama kunnen sa na hagu alamar kashedi yake yimin na taɓe baki duk dama cikin zuciya ta akwai abinda nike aiyana wa akan zuwa makarantar a fili kuma na amsa masa da "Toh" yai min sallama yana mai yi min murmushin da na kasa gane shin wani iri ne! ya tafi ya barni da tunani barkatai acikin zuciya ta.Da daddare ma ina zaune shi nike tunawa, har Mairo tai min tayin zuwa dandali amma nayi banza da ita, tasan yadda nike matukar son takalmi mai ƘWARAS ma'ana takalmi mai tsini don haka sai ta ce," Ummi har ƙwaras ɗina fa zan baki ki sanya"
shima baki so ba za kije ba ko shikenan ni kinga tafiya ta" har ta kusa kaiwa bakin ƙofa na biyo ta da gudun gaske wallahi zaka ɗauka ko biyoni akayi ina haƙi ina tambayar ta," Ina....Ina...Ina takalmin yake zan je dandalin" tsoki tayi mun sannan tayi gaba abin ta, sannan ta juyo kaɗan ta ce," suna bayan ƙofa kuma kiyi sauri ina jiran ki"
* Mairo na kenan ban taɓa yi muku sharhi akan Mairo ba ko" Mairo dai yarinya ce nutsastsiya mai hankali, ta fini haske da jiki kadan amma mutane da yawa suna ce wa na fita kyau duk dama ni baka ce, tana da saukin kai haka zalika bata son raini ko kaɗan, akwai ta da son girma da kuma nuna ita babba ce amma duk da hakan tana zama tayi hira dani taji damuwa ta amatsayin ta na ya agare ni shiyasa nike matukar son ta kamar yadda nima take nuna mun kulawa * na ɗauko takalman na biyo ta muka jera da ƙawayen ta ina ji suna ce wa," Ke Mairo kullin sai kanwar ki Ummi ƙwaras ta biyo ki, shin ita bata san hanyar dandalin bane ko bata da ƙawaye ne, mu kam bamu son muna jera wa da ita"
Kai tsaye Mairo ta ce," Saboda me?
"Saboda mun girme ta mana Mairo ke baki gani ne!

VOUS LISEZ
UMMI KWARAS ✔
NouvellesLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...