35

35 2 5
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 35

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Saura mana kwana biyu mu koma gida sai period ɗina yazo ita kuma Abulle ta fara sallah, wannan ne yasa na yanke wata shawara na tsara yadda zamu fuskanci al'umma da iyayen mu baki ɗaya.....da kyar Abulle ta yadda da shawara ta, sai da na lallaɓe ta na nuna mata ni zan ɗauki duk wani cin kashi da za'ayi mata, in takama korata za'ayi ma zan tafi, duk da tana son Ɗan ta Aarif amma haka ta hakura ta bar min.

Da wannan kaɗai zan iya cewa naga namijin kokarin Abulle, Sannan duk da ni ƴar uwar ta ce kuma ni na kawo shawaran amma sai daga baya na gane wautar ta na sadaukar da Ɗan ta da tayi, saboda babu uwar da ta fara shayar da ɗan ta kuma lokaci guda a raba ta da shi saboda gurmin da mutane za suyi....Abin da ban fahim ta ba shine Abulle ta ɗauke ni tamkar ciki ɗaya muka fito, RELATIONSHIP ɗin mu ya wuce wasa....Yan da take ɗaukar shawarwari na, da yadda take ji dani nima haka nake da ita, Mun yanke shawaran ne ba mu yi tunanin cewa ya gaba zai kasance ba, kawai mu tunanin mu yanda zamu fuskanci iyayen mu.

Na tsagaita ina share wata ƙwallar, na cigaba da cewa bayan mun dawo gida, Gidan Abulle ta biyo ni, bayan kowa yayi mamakin dawowar da mu kayi ga kuma jariri a hannun mu, tambayar farko da a kayi min wacce ita ce tamabayar da naji tsoron ta fiye da tambayoyin da kowa yake min.

Tambayar Baba:

"UMMI INA KUKA TAFI DUK TSAHON WATANNIN DA KUKA ƊAUKA BAKWA MAKARANTA, SANNAN KUN TAFI BABU JARIRI YANZU KUMA KUN DAWO MANA DA ƊA, UMMI KAR DAI ZARGI NA YA ZAMA GASKIYA GAME DA ƊAN DA KUKA ZO MANA DA SHI"

A ranar kuka kawai na keyi na kasa bama Baba amsa, dalilin da yasa suka ga kamar ɗa na ne Mama sun fahimci bana sallah har tsahon kwanaki 6, hakan ya tabbatar musu da cewa Ɗa nane, Baba ya dena kula ni, ya dena hira dani, kullun bai da aiki sai hawaye.

Mama tana iyakar bakin kokarin ta don har wanka take yi ma Aarif, ta goya shi, Mai dawa ma ban fuskanci tsana daga wajan ta ba, sosai take debe min kewa amma ba dai kamar da ba.

Wajan bawa jariri abincin sa,Tun bayan dawowar mu Abulle ke shayar da shi ba tare da sanin kowa ba, amma ni ce mai raino shiyasa yau idan bata kwana a gidan mu ba, gobe zan bita mu kwana a gidan su, dama tun farko mun saba da hakan shiyasa bamu samu matsala ba har Aarif ya fara wayo yayi shekara guda daɗin abin ni da Abulle ya ɗauke mu abu ɗaya saboda duka muna kula da shi dai dai gwagwado sai dai yafi mannuwa da ni ya danganta da irin wasan da nake masa, da kuma kullin yana goye a baya na.

Jita jitan kauyen namu da kuma halin da Baba da Mai Anguwa suka shiga shi ya daɗa tayar min da hankali, cewa sukeyi UMMI ƘWARAS DAGA ZUWA MAKARANTA A DAWO DA ABIN KUNYA, shi ne musabbabin son bari na kauyen, amma daga baya abin ya lafa...tashi ɗaya ko ince lokaci guda na ta shi ina ta haɗa kaya zan bar kauyen , zuciyata ke tafarfasa na kasa gane dalilin son tafiya ta, na samu Abulle na sanar da ita, ta bani shawara akan nayi hakuri na zauna, kuma duk dama a lokacin mun yi waya da Ɗan binni ya tabbatar min da cewa zai zo garin.

Ban san ya a kayi ba, ni dai na wayi gari na ɗauki jakan kaya na na goya Aarif na bar kauyen, kai tsaye Bauchi na tafi....Na fara sabuwar rayuwa ni da Aarif.

TO KUNJI LABARIN YADDA ABUBUWA SUKA KASANCE.

Baba sai da ya zubar da kwalla bayan Mamie ta sanar dasu cewa a siri ne Shatou tayi, amma ya jima da karye wa.

Mai anguwa ya ce,"Lallai Ummi na fi ganin kokarin ki na wajan kare ƴar uwar ki akan laifin da dama ba laifin ku bane, Ku shiga halin rayuwa dukkan ku, domin kuwa tun bayan tafiyar ki Abulle ta dena walwala, babu wani gyara, ita ba makaranta ta koma ba, kullin tana ɗakin Baba Sadiyya tana sharɓan hawaye so da dama kamar zatayi yunkurin sanar damu wani al'amari amma sai ta fashe da kuka, mun yi tunanin ko aljanu ne suka fara taɓa ta sai muka fara mata rukiya, anan muka gane babu abin da ke damun ta sai muka zuba ma al'amarin ido, saboda abin yayi mana yawa a lokacin da Ɓatan Ummi za muji ko kuma da abin da Abulle ta keyi.

Hmmmmm Alhamdulillahi zamu ce saboda komai yazo karshe yanzu, Yanzu babu abin da zance sai dai Allah ya kara ma Mijinta hakuri, amma kana da damar da idan kaji ba zaka iya zama da ita ba,to ka faɗa, idan kuma kana son ta har yanzu to sai ka faɗa mana.

Mahaifin Zunnurain ya ce,"Haba sai mu kasance mutanen banza kenan, ai Mai Anguwa ko a labarin nan da yarinyar nan ta bayar na shaida kwarai da halayen Zainabu abu,Zunnu shi ya ganta ya kuma sanar damu yaga mata duk da ma bai san abin da ya faru ba. Ni da Mahafiyar shi bamuyi na'am da maganar ba, sai daga baya saboda yadda mu kaga yana son auran.....A yanzu danaji yadda yaran suka sha gwaggwarmaya a rayuwarsu tausayin su na keji sosai a rai na....sanadiyar abin da ya faru zan biya ma Zunnu da Sadeeq da matayansu Umara ba wai don mazajen basu da kuɗin yin hakan ba, sai don saboda alkhairi, suje suyi honeymoon ɗin su a cen sai sanda sukayi niyar dawowa.

Take wajan ya kaure da Allahu akbar ana ta jin dadi.

Sai Sadeeq ya ce,"Abba in faɗa ko zaka faɗa musu"

Abba ya ce,"Noooo bari na sanar dasu" Na biya ma Mai Anguwa da Mahaifiyar sa da kuma Matan sa Umara" Za'a fara surutun murna sai ya dakatar dasu yana cewa" Ku dakata sannan na biya ma Baba, Mama, Mai dawa, Kawu Shafi'u, da iyalan sa, sai Mu'azzam duk na biya muku Umara gaba ɗayan mu zamu wannan watan zamuje muyi ibada.

Ana ta gode ma Abba, yana cewa "Ku dena gode mun idan ban taimaki talakawa ba ya kuke son nayi da dukiya ta.

Mamie ta ce," Ni dai ku taimaka kh bani Aarif kun ga Ummi ta ɗauke mun Babban Ɗa na, Aarif zai maye min gurbin sa.

Abulle ta ce,"Mamie har sai kin roka ki ɗauka an baki halak malak babu wan da ya isa ya kwace Aarif daga hannun ki.

Mamie ta sake runguman Aarif tana murna, Abba ma dadi yake ji, Allah yasa musu son yara amma basu samu yara da yawa ba sai Sadeeq shi kaɗai.

Mummy mahaifiyar Umar tana ta kuka, ta umar ci mijinta da ya tashi su tafi, tun da basu damu da abin da Abulle tayi wa Umar ba.

Mai Anguwa yace,"Ku ke batawa kanku lokaci, da kun san abin da nayi niyar yiwa Umar wallahi da baki tsaya kina kuka akan wannan abin da akayi masa ba.

Daddy bai ce kala ba, ya ɗauki Umar da yammacin ranar sallah suka kama hanyar katsina sai dai me zai faru mummunar hatsari/accident su kayi a dai dai Kauyen Kuka magamar jibiya, Mummy da Daddy sun riga mu gidan gaskiya, Umar kuma take ambulance ta ɗauke shi sai General hospital.

______________________________________

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM (DielaIbrahim)
COMMENT
VOTE AND SHARE

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now