24

36 2 0
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 24

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
BAUCHI STATE
GRA

Shatou tayi tsaki ta juya tana kallo na, Ta ce,"Na sanya ki a cikin duhu ko to bari kiji wallahi sai na ɗau babban mataki a kanki, na san duk abin da kikeyi da sannu zaki gane kuranki ta faɗa tana huci, ta bar wajan, ta bar ni tsaye ina mamakin ta....Shin me ta aikata min?
Dama ta sanni ne tun shekarun baya?
Gashi kuma ta ambaci sunana Salamatu, Shin me Shatou ta keyi ne?

A daddafe na koma ɗaki na zauna saboda wani azababben ciwon kai da ya kamani lokaci guda, samun waje nayi na kwanta wanda tuni bacci ya ɗauke ni.

Bayan wata ɗaya
___One month later _________________

Bari mu leka su Baba
___KATSINA STATE___________________
Barhim Estate

Tsaye na hango kyakkyawar mace mai cikar kamala, kamannin su ya bace da Ummi ƙwaras sai dai ta ɗara Ummi haske, ban gane ko wacece ba sai da wani kyakkyawan mutum ya fito, anan naji yana faɗin Mairo kin ɗauko flask in ruwan jinka na ya faɗa da zolaya.....anan na gane Yaya mahmud na koma kallon Mairo na ce lallai fa ashe Mairo ta canja wallahi ta kara kyau ta goge sosai.

Yaran ta uku kyawawasun samu hutun makaranta shiyasa zasu tafi gaba ɗaya suyi hutun su a kauye.

____Garin gado______________________

Tafiyar awa guda sukayi kafin suka iso Garin gado sai da ya sauke su a gidan Mai Anguwa, wanda yasha gyara kamar ba a a kauye ba, ginin bulo akayi da kwanun zinc gidan ya gyaru sosai, Mahmud ne ya gyara.

Mairo suka shiga suna gaggaisawa da mutan gidan,bayan sun huta ne, Mairo ta samu Abulle a ɗakin Baba Sa'adiya.

Zaune take tana ta karatun alqur'ani mai girma, don bata ma san da zuwan su Mairo ba.

Ta kai aya sannan ta rufe tana ɗan murmusawa wannan karan ta ɗanyi fasali ba kamar lokutan baya ba, kasancewar Mairo na yawan zuwa ta bata shawara akan rayuwa, asalima ita Mairo tayi niyan Abulle ta dawo birni da zama, amma ita Abulle tana tuna abin da ya faru da su shekarun baya shiyasa ko da wasa ba ta kara gigin cewa zata gidan Yaya Mahmud ba.
"Ina kwana Aunty Mairo"
Lafiya lau Mairo ta amsa, tana murmusawa ta ce,"Eh Lallai naga canji sosai Abulle, yanzu dai sauri nikeyi zanje na ga su Baba, ga waɗannan kayan ta mika mata manya manyan ledojo cike da kayan sawa da abubuwan bukatu na rayuwar ƴa mace.

Anjima ki same ni gidan mu sai muyi hira kinji ƴar kanwata.
Abulle ta rungume Mairo tana kuka mai tsuma zuciya tana cewa,"Aunty Mairo na gode sosai, kina debe min kewar Ummi.

Mairo ta ce,"Ya isa hakanan Abulle yi shiru kinji.
Abulle ta ce Aunty ba laifin Ummi bane Laifi nane, me yasa Ummi ta kasa dawowa cibiyar ta, ta wanke kanta daga wannan al'amarin.

Mairo ta yi saurin rufe mata baki tana cewa,"Shiiiiiiiiii Abulle yi a hankali mana, na ce kiyi shiru ki bar wa Allah komai ko, tun da Ummi har yanzu Allah bai dawo da ita ba, watakil tana raye, wata kil kuma ta rasu, mu dai muti ta Addu'a kinji.

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now