25

41 1 0
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 25

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________
BAUCHI STATE
GRA

Shatou ta ce,"Ina ai hakan ma zai kasance da yardar Allah komai yazo karshe, Boka yayi mata tsawa ya ce,"Kin san da Allah ne kike zuwa wajan mu don biyan bukatar ki,Karki yarda ki sake kira mana Allah,  ba aikin Allah mukeyi ba, ki ta shi za'a mai dake wajan motar ki.

Tashi tayi a tsorace ta rufe idanuwan ta kamar yanda ta saba, ko second ɗaya ba'ayi ba ta ganta cikin motar ta hakan yasa tayi ajiyar zuciya ta kunna motar ta bar wajan.

Gudu take ta faman yi a hanya, ta iso Bauchi ana ta ruwan sama amma bame karfi ba.

Bayan ta isa gida, tana Allah Allah, Allah yasa ta samu Yaya Sadeeq a gida, dama tana da pills na bacci, wanda take ɗan sha idan mood ɗinta ya baci, sai da tayi wanka ta shirya tsab sannan ta fita ta haɗa abin  sha zobo drink, ta san Yaya Sadeeq baya ganin zobo ya share ta zuba pills uku ta jijjiga.

Da kyar ta iya fita saboda wannan lokacin ruwan saman yayi karfi, har sai da ya ɗan jika mata kaya.

Kai tsaye flat ɗin shi ta nufa, sai dai kash wayam babu kowa hakan yasa ta fara neman shi,flat ɗin Mamie taje nan ma bayanan, abin mamaki cen ta jiyo muryoyin su ta bayan flat ɗin Mamie, zuciyar ta na huci ta nufi waja  n da sauri, samun su tayi a ɗakin Ummi, Sadeeq na tsaye yana wasa da Aarif, Mamie na zaune saman sofa, yayin da Ummi ke kokarin sauka daga kan matakalar corridor don da zai sada ka da kitchen ɗin su....Tana tafiya kamar wata hawainiya hannun ta na ɗauke da tray, Har shatou ta kau da kan ta gefe sai ta sake juyawa taga ashe glass jug ɗin zobo ne da cups guda hudu, ta dire shi a gaban Mamie tana kokarin zubawa kowa wanda kanshin cucumber da mint shine ya karaɗe ɗakin, Ummi na ta zubawa tana cewa"Mamie ga zobo, Yaya Sadeeq, Aarif, or na manta ma ban ɗauko Meat pie da Samosa ba, Ummi ta tashi ta ɗauko daidai lokacin suka lura ashe Shatou na tsaye bakin kofa.

Mamie tace,"Shatou karaso mana,Inaaaa ai tuni Shatou ta bar ɗakin tayi gidan ta da sauri tana huci,
haushi ya sa ta kafa kai ta shanye soborodon ta, Tama manta akwai pills a ciki, haka ta yini a ɗaki ranar ran ta ya baci saboda abin da ta gani without her knowledge tayi bacci babu sallah babu salati, ba ita ta tashi ba sai misalin karfe goma sha biyu.

Ta tashi tana ta layin bacci duba agogo sai taga dare yayi sosai kuma ta san Yaya Sadeeq ya kwanta by now, tsaki tayi ta zare layar, ta shiga ban ɗaki ta watsa ruwa, bayan ta fito tayi shirin bacci sannan ta nemi lafiyan gado.

Kun ga tayi missing rana ɗaya, The next day, Rana ta biyu ta tashi late tana ta lissafin yadda zatayi ya kusance ta,Taje  flat ɗin shi ta duba shi baya nan, ta tambayi Mamie ko ina yake?
Mamie tace,"Sadeeq ya tafi Dass, ya je gaishe da dangin mahaifin sa, saboda suna ta tambayar sa......Shatou ta dafe kai abin ya bata mata rai amma sai ta basar ta wuce ba tare da tayi wa Mamie magana ba.......karo mukayi daidai lokacin da nike shigowa ita kuma tana kokarin fita ta bankaɗe ni haɗe da tsaki ta wuce ko magana ba ta mun ba......ban san lokacin dana jawo ta da baya sannan na tsinka mata zazzafan mari,na kankara mata warning "Daga yau kar ki kuskura ki sake gigin bankaɗe ni, tsaki kuma in kin ga dama kiyi so miliyan miliyan mara mutunci" na faɗa ina ban ka mata harara na wuce na bar ta tana dafe kuncin ta, Na ɗan tsaya nace mata "Kaɗan ma kika gani wallahi dan na yi sanyi ne da duka zaki sha billahillazi, jibe ki kamar kazar mayu don Allah" ina faɗa ina dariya naa wuce falon Mamie.

UMMI KWARAS ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang