*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 12STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
************************************
KATSINA STATE
JIBIYA,KAUYEN GARIN GADOShirye Shirye ya kankama yau saura kwana uku kacal a ɗaura aure ranar juma'a.
Yau laraba tun safe muke ta kokarin ganin mun shirya yadda gaɗa zai kasance a ranar Alhamis da yamma.
Ni, Abulle da kawayen Mairo guda huɗu muka samu Ango a kofar gidan Mai Anguwa muna tattaunawa a kan kuɗin da zai bayar na ƴan mata.Yaya Mahmud mu da abokanan ka ma za muyi magana na fahimci Yayan namu kunya ya keji" na faɗa ina dariya.
Ya ɗan harare ni da wasa sannan Ya ce,"Bari na kira muku su dama duk sun iso ku suke jira, kun ga sai kuyi shawaran dasu ko ya ku kace?
Duk muka haɗa baki muna cewa,"Eh gaskiya da yafi"Yana shi ga soron gidansu kai tsaye ɗakinsu ya shiga, jim kaɗan sai gasu sun fara fitowa ɗaya bayan ɗaya dukkan su ƴan gayu ne saboda gaba ɗayansu kaf sanye suke da manyan kaya wato shadda wanda yai matukar yi musu kyau suka fito suna raha atsakanin su,
ƴan mata ya a kayi ne muna ciki muna hutawa kun sa anyi kiran mu!
Tun da suka fara magana nayi shiru ina nazarin me zamu ce musu sai naji Nadiya (Babbar ƙawar Mairo) ta ce,"Kuyi haƙuri dama maganar kuɗin ƴan mata mu kazo a bamu saboda gobe muna da gaɗa da yamma.
Sai ɗaya daga cikin su Ya ce,"To kuma nawane kuɗin da kuke buƙata?
"A'a Abdul barsu dan Allah kawai mu basu kuɗin da zai ishe su har na ranar biki ma ka ga kada gobe suzo su dame mu da maganar kuɗi" ya fada yana ɗan dariya a lokacin da yake kokarin ciro kuɗi a aljihun wandonsa na ɗaga kai ina kare masa kallo dan na san irin maganar da zan watsa masa amma ganin *Yaya Umar Faruk* ne shiyasa nayi shiru a zuciya na ce Allah ya taimake ka, ina ɗan hararan shi har ya bamu bandir ɗin ƴan dubu ɗaya ɗaya har guda biyu Ya ce ga dubu ashirin nan ina fatan zata ishe ku kuyi gaɗa kuyi walima ranar ɗaurin aure?Kut! ai gaba ɗayan mu ɗauke wuta mu kayi saboda duk tunanin mu kuɗin da zamu karɓa bai wuci naira ɗari takwas zuwa dubu ɗaya ba amma wai sai gashi ana miko mana bandir ɗin dubu ashirin ni UMMI ina na taɓa rike irin wannan zunzurutun kuɗin!!!!
Da kyar na bari Abulle ta amshi kuɗin bayan mun koma gida ne muka nunawa Mama kuɗin, ita ma cewa tayi a mayar sun yi yawa amma Mai gidan dawa tace kar mu yarda mu mayar acewar ta ai hakkin ƴan mata ne.
Da daddare ni da Abulle mu kayi wa Mairo kunshin gargajiya mai kyau.Washe gari muka soma shirya amarya inda a kayi mata bakin lalle, sannan muka wanke mata kai da ganyen karkashi da sauran man wanke gashi da muka ɗauka a cikin akwati
Amarya tasha atamfar ta super riga da zani, ta sanya sarka fari mai adon duwatsu da warwaro kai har da agogo, kuma duk shirin Abulle ne saboda ta fimu sanin kayan binni, muka yafa mata farin gyale babba mai kaman leshi sai takalminta na ƙwaras wanda yayi mata kyau sosai ina ta kallon kafarta saboda a duniya babu abin da nike muradi kamar ƘWARAS.
ESTÁS LEYENDO
UMMI KWARAS ✔
Historia CortaLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...