18

38 2 3
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 18

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Mu ka yi mata sallama har da kyauta ta bama Aarif, ina komawa gida na fara shirya kayan mu, Aarif ya ishe ni da tambaya, UMMI ina zamu kike haɗa mana kaya kuma?
Na ce Aarif gida zamu canja ka ji.
Haka yayi ta damu na da surutun tambaya daga karshe na ce mi shi ya je ya kwanta yayi bacci gobe akwai "school" Makaranta.

A daren na yi magana da mai adashe na, ta ce gobe da safe na zo na karɓa. ranar da sake-sake na kwana zuwa washe gari.

THE NEXT DAY
~ SABUWAR RAYUWA~

Da asubahi na soma karasa wasu shirye-shirye, nayi wa Aarif wanka na shirya shi na kai shi makaranta na biya masa kuɗin makarantar sa sannan na dawo yau kam ban je asibiti ba, zama nayi na karasa haɗa ƴan kayan mu, na haɗa duk kan abin da na san zamu buƙata na bar wa'insu kayan a cewata dama kuɗin hayan bai kare ba idan ya kare zan zo na kwashe sauran kayan nawa.

Karfe sha biyu na rana an gama shirya min ƴan kayana a karamar J5 ɗinnan motar kwasan kaya da kai na na yi musu jagora, mun fara tsayawa a makarantar su Aarif na ɗauko sa sannan muka je GRA.

Bayan na samu masu aikin gidan wanda suna da yawa ba laifi, Masu aikin waje suna sanya kayan su na gida, masu aikin ciki kuma su uniform suke sanyawa bakin wando da farar riga, kamar dai makaranta, masu aiki a kitchen kuma mata fararen gown suke sanyawa na gansu ne shiyasa na fahimci haka, Sosai masu gadi da ma'aitan suke mamakin irin shirgin kayan da na kwaso, acewar su, komai akwai a gidan wanda ya fi kayan da na ɗebo so dubu miliyan ma, Kasancewar sun san da zuwa na, ba su hanani ɗiban kaya na ba illa ma taya ni shigar da su masaukina wanda ya ke gefen masaukin ma'aikata mata na gidan gaba ɗaya.

Ma Sha Allah nawa masaukin yafi na sauran ma'aikatan haɗuwa sosai domin ciki ne da falon sa, bayi, da karamin kitchen da store, abin mamaki babu abin da babu a ɗakin, ina tsaye kamar wata gunki tsabar na girgiza da yanayin karramawar da Mamie ta yi min, na ji wasu daga cikin ma'aikatan suna gaishe da Mamie.

Da sauri na dukar da kai na ƙasa ina mai isar da gaisuwa na gare ta cikin girmamawa, na rasa dalilin da yasa har yanzu ni ke jin kunyan Mamie bana iya kallon ƙwayar idon ta na yi magana sai dai idan na duƙar da kai na.

Mamie ta amsa min tana mai shafa kan Aarif tana cewa har lokacin tashi yayi kenan?
Na ce "Eh Mamie, ai dama sha biyu na rana suke tashi.
Mamie ta gyaɗa kai kafin ta sauke ajiyar zuciya tana cewa Ummi ga masaukin ki nan, naga kin zo da kaya, ina tunanin komai da kike buƙata akwai shi a ɗakin sai dai abin da ba a rasa ba.

Na ce "Mamie komai yayi fa, wallahi ai ban san akwai komai anan ba, kuma yanzu kam kayana ban san ya zan yi da su ba.

Mamie ta ce "Toh ba damuwa ki zaɓi abin da ki ke so in yaso sauran sai ki yi kyauta da su ko, ga ma'aikata a gidan na san akwai masu buƙata.....Duk abin da kike nema baki samu ba kofa a buɗe take kiyi min magana kin ji.

UMMI KWARAS ✔Where stories live. Discover now