03

60 6 0
                                    

*UMMI ƘWARAS*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

UMMI ƘWARAS
PG 3

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

Ranar dai Ummi haƙura tayi da fitar amma rigima babu wanda ba ta yi ba da neman tsokana sai aka ci sa'a ranar
babu wanda ya kula ta har lokacin da Baba ya dawo tana jin muryar shi ta duro daga saman gadon shillon ta amma me zai faru ganin Mama tayi ta ɗauko dorina ta ce," Ummi wallahi kul kar ki yarda ki soma fitinar ta ki don wallahi ba zan iya ɗauka ba.

Ummi ta zumɓure baki ta haɗe rai ta koma ta haye gadon ta kwan ta, tana jin Baba ya shigo suna ta damuwan su har ya na ta tambayar, "Shalelen sa ya akayi ta yi bacci da wuri yau ?
Buɗar bakin Mama sai ta washe baki tace ai yau babu rigima fa cewa tayi za ta kwanta da wuri shi ne fa har tayi bacci ma.
Baba yace, "Ahhh Masha Allahu haka ake so to ni na tafi ɗaki sai da safen ku, Ummi ta ji wani abu ya to kare mata zuciya ai bata san lokacin data saki kuka ba Mama suna jin ta amma basu rarrashe ta ba har dai tayi mai isar ta bacci yai a won gaba da ita"

______________________________________

Wasa wasa dai Ummi ta zama ƴar kulle ko da yaushe tana gida kusa da Mama hankalin Mama ya kwanta sosai ganin kamar Ummi ta fara natsuwa "To dama an sanya ta makarantar Allo inda Baba yake koyarwa don Mairo ma cen ta ke zuwa"
Ummi dai idan ta tafi makaranta ba ta shi ga aji nan kofar makarantar ta ke zama duk yaron daya zo latti sai ta ci ƙaniyan sa kafin yake wuce wa aji, ko kuma idan kazo da ƴar tallar ka sai ta kaɓar ya zube ko ta rabar wa yara sannan ta kora yaro gida ta ce ai ba talla a ke yi a makarantar ba, tun iyayan yara na zuwa kawo ƙorafi ana hukun ta Ummi kuma hakan bai sa ta dena ba sai ma abin da ya karu" Ana yawan ka wa Baba ƙorafi akanta kuma shi ma yana iya bakin ƙoƙarin shi na ganin ta dena amma Ummi ba a iya juya ta shiyasa ya hana ta zuwa makarantar kwana biyu yara yara su ka huta ta fitinar ta.

Sai yau Ummi ta fito cikin shirin ta da sassafe ta ɗau kwaras ɗin Mairo ɓoye a bayan ta, sa'annan ta samu Mama da Mai gidan dawa da Maman halilu suna dakan fura Mama ita ke cuccura wa tana zuba dawon a cikin ruwan zafi har sai ya dahu kafin ta sauke ta tsame su sannan sai ta baiwa Mai gidan dawa ita ke dakawa"

Kamar dai munafuka haka ta rinka  sanɗa dama fita za tayi ba tare da sanin su ba sai kuma ta dawo wajan Mama ta tsugunna ta ce,"Mama sannun ku da aiki!
Mama ta ce, "Yauwa Ummi ina zuwa haka? Ummi ta ce,"Mama gidan su Abulle zani  na gaido Baba Sa'adiya!
Mama bata ɗago ta kalle ta ba amma sai tace *Ummi* daga gidan bance kiyi ko ina ba kina ji na" Ummi tsabagen murna yasa ta rungumar Mama har ta ku san tunƙuɗe ta Mai gidan dawa ce ta tare tana cewa hankali Ummi....hankali dai"

Ummi ina ma ta tsaya sauraron su tafiyar ta tayi abun ta tana tsalle tsalle tana zuwa ƙofar gida ta sanya ƙwaras ƙwaras ɗin ta fara tafiya kamar wata hawainiya kowa ya ganta sai ya tanka mata ace Ummi sai yau ake ganin ki ita kuma sai ta yi banza da su don Ummi ta iya miskilanci idan bata ga damar kula ka ba aradu ko kai waye, ko zaka mutu kana yi mata magana ba za ta kula ka ba sai in tayi niya" kai tsaye gidan su Abulle ta wuce suna ta murnar ganin Ummi Baba Sa'adiya kakar Abulle ce *Umma* kuma ita ce *Maman Abulle* Abulle dai ita ce ƴa ta biyar acikin jerin ƴaƴan Mai Anguwa
Mai Anguwa gaba daya ƴaƴan sa suna karatu maza" yaran sa shidda
Ibrahim, *Mahmud*, Sale , Jummai , Sharifa , *Zainabu Abulle" sai autan su Hamisu" Mazan manya manyan suna Jahar Katsina gidan wan sa daga nan suke tafiya makaranta" Jummai da Sharifa sunyi aure a nan Garin gado sai Abulle da yanzu ta fara karatun a Government Girl's Secondary Jibiya *G.G. S JIBIYA* Tana J.S.S 1 wanda bata jima da fara zuwa ba"
Sanda za'a tafi da Abulle an so su tafi tare da ɗaya daga cikin yaran Mal. Muhammadu sai aka samu takardar admission ƙwalli ɗaya wacce gwamnati ce ke bayar wa ko wani kauye mutun ɗaya ake dauka a shekara, to sai a ka ce idan wata shekarar ta zagayo za'a baiwa Mal. Muhammadu shima ɗaya daga cikin yaran sa suje makaranta"

UMMI KWARAS ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora