*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 28STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
KATSINA STATE
JIBIYA, Garin gadoMamie ta fara faɗa, wai Ummi miye haka ne, ban san iskanci fa, ba zaki fito ba ne?
Abba ya ce,"Uhm Uhm Mamie bi ta a hankali ta jima bata gida abin dole ya zame mata sabo yau"
Mamie tace,"Uhmm kai Abba ka iya sangarta yaro ai, shiyasa ka sangarta Shatou, yanzu miye abin jin kunya anan ka gani fa wallahi taki fitowa Abba.
S.Chubaɗo dariya yayi musu sannan ya leka yace,"Gimbiya saurautar mata, takawarki lafiya matar Sadeeq ƴar gidan Abba"
Kirarin nan ne ya sa ni murmushi mai ƙayatarwa bayan hawayen da suke ta fita daga idanuwa na, na ɗan share hawayen sannan na dubi Yaya Sadeeq nace"Yaya ba zan iya shiga ba, kunyan su Mama nike ji wallahi"
S.Chubaɗo yace"Da gaske ashe kin gane kinyi laifi kenan, dama na zuba miki idanu ne, gwara da kika gane barin iyaye ba abu bane mai kyau, komin halin da ka shiga bai kamata ka bar iyayen ka ba, ka tafi uwa duniya, amma na miki uzuri saboda ba da son zuciyar ki kika tafi ba.
Na ɗanyi pouting baki na, na fashe da wani sabon kukan wannan kara da sauti kukan yake fita......S.Chubaɗo ya kama baki, yana cewa"Salma ya dai anya lafiyan ki kalau kuwa" ya cire hular zannan shi yana dago kai daga jikin window ɗin motar yana cewa Mamie ina ga dole sai kin zo fa Salma da gaske takeyi wollah"
Abba ne ya zo ya lallaɓa ni da kyar na fito da kafata ɗaya waje ina shirin fitowa ne naga ƴan gidan mu, Mu'azzam,Halilu, Harira, da yaran Aunty mairo, na guje gujen fitowa suna cewa"Yara makaryata ina kuka ga UMMI ƘWARAS ɗin.
Na fito na taka kasar haihuwa ta, wallahi wani iska ne mai dadi ya ratsa ni ya shiga jikina, Ina tsaye ina kare wa karamin kauyen namu kallo,Ina kare wa gidan mu kallo yana nan yanda yake babu abin da ya canja, Yayin da naji wasu daga cikin ƴan matan kauyen wanda suka sanni suna ta wakar UMMI ƘWARAS ta dawo kasancewar talle sukeyi a kofar gidan mu, wasu sunyi aure wasu kuma suna nan.
Lahhh ashe da gaske ne cewar Halilu, na fara takawa ne sai ga Aunty Mairo da gudu tazo ta rungume ni kamar me, ban san lokacin da kuka ya kubce min ba ita ta jani muka shiga gidan yayinda ni kuma na kankame ta a kunne na sanar da ita ina tare da baki ta musu iso da gidan.
Mama na rungume ina kuka, Mama ma duk da dauriya irin na ta na uwa sai data zubda hawaye.
Mai dawa ta taso daga kuryar barandar ta tana cewa da gaske jikalle ta dawo, ku gwada min ita in ganta.
Da gudu na saki Mama na ruga na rungume ta tsam wani sabon kukan mu keyi daga ni har Mai dawa, bayan kaman mintuna goma sha biyar da faruwar hakan, har an bawa su Abba masauki.
Gaba ɗaya har da su Abba suna zazzaune a barandar Mai dawa, an kawo musu abinci da fura, Mama na rike da Aarif yana ta lilo da kayan ta.
Ni dubi Aunty Mairo nace,"Aunty yaran ki kenan, tubarkallah Ma Sha Allah, Kun jima ne anan?
VOCÊ ESTÁ LENDO
UMMI KWARAS ✔
ContoLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...