*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 14STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_______________________________________
Tabbas babu shakka jinin daga jikina yake fita, amma na rasa gane shin wannan wani irin abune, tsoron ne ya sa na kara sakin wani ihu yayin da mata biyu ne suka fara shigowa bayin sai Mai dawa ta shigo hankali tashe, ko dana ɗaga ido naga Mai dawa da sauri nayi kanta ina kuka ina nuna mata na ce,"Mai gidan dawa na shiga uku na ji ciwo a kafa kalli yadda jini ke ta zuba na karashe maganar ina nuna mata tiles ɗin bayin"
Tana ganin haka ta janyo ni jikin ta, haɗe da toshe min baki saboda ta ga alamar gaba ɗaya a tsorace nike, sai faman kuka ni keyi, sai data sallami sauran matan, kafin ta jani kuryar ɗakin da aka sauke mu, inda daga ita sai Mairo da Abulle ne suna ta bacci, ta zaunar dani haɗe da cewa,"Kiyi shiru Ummi ba ciwo bane kiyi shiru kinji.
Da kyar na karasa shashshekar da ni keyi na maida hankali na gun Mai gidan dawa ina goge guntun hawayen dake fuska ta, na ce "Ba ciwo ba to menene kenan?
Mai dawa ta ɗan dafe goshin ta, ta rasa yadda za ta fara yi min bayani , ganin duk nabi na tsorata sosai da lamarin, dabara ta faɗo mata, ta kira sunana ahankali.
Aranar Mai gidan dawa ta fahimtar dani komai daya danganci jinin al'ada sosai abin ya mai da ni Ummi mara surutu.Da yamma aka kai Amarya gidanta da yake Shagari, ita kaɗai ce a sabon gidan ta mai ɗauke da parlo biyu ɗaki uku sai dinning, kitchen da store" kowa yana ta taya Mairo murna da kuma Allah ya sanya alkhairi, abin ka da ƴan ƙauye naga gida mai kyau, nayi mamakin wannan gida ko a mafarki ma ban taba ganin irin sa ba, tsabagen kyau da tsaruwa, ba sai na fara cewa ni kam naga wajan zama ba zan koma binni ba. Mai dawa ta ce" Wajan zama a ina, Na ce"Anan mana, ni bazan koma kauyen cen ba"
Mai dawa ta kama salati tana tafa hannu wa, ta ce," Nama isa, ai tare zamu koma ko ina so ko bana so"
Mairo kam tasha kuka nayi matukar tausaya mata amma abin mamaki ni ko ɗigon hawayen kewanta bai sauka a idanuwana ba. Ta na ta rokon Mai dawa wai abarni ni da Abulle muyi mata kwana biyu.
Mai dawa tayi banza damu lokacin tafiya nayi ta kaɗa ƙeyar mu da sanda mutane nata mana dariya.Muka koma gidansu Mansura anan muka kwana washegari muka koma kauyen mu, Da taimakon Mai gidan dawa na san yadda zan tsarkake jikina da kuma abin da yakamata nayi idan abin yazomin. Abulle nata min dariya wai saban shiga, ban kula taba saboda abin yazo min da rashin son yin magana ko surutu bana iya yi, sosai na natsu waje ɗaya saboda gani nike kamar kowa ma kallo na ya keyi da abin.
Bayan sati ɗaya aka koma makaranta, Abulle ta riga ni komawa don ni sai da aka kara wani satin.
Ana gobe zamu tafi,muna zaune ɗakin Mama, ni da Mai dawa , suna ta hira da Mama, ina kwance kafar Mai dawa tana ta faman haɗa min kaya na sai lallami na ta keyi, ban da shagwaɓa babu abin da ni keyi mata, Mama ta ce,"Ja'ira zaki gane shayi ba ruwa bane ai idan kika tafi a yayin da kiga waiga hagu da dama kika ga babu wanda zaki ma shagwaɓa sai muga yadda za kiyi.
![](https://img.wattpad.com/cover/280330340-288-k249707.jpg)
JE LEEST
UMMI KWARAS ✔
Kort verhaalLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...