19

47 7 25
                                    

*UMMI ƘWARAS*


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/

*UMMI ƘWARAS*
PG 19

STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}

_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_

_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_

______________________________________

RIGHT FROM WHERE I STOPPED

Da karfe huɗu 4:00pm na ji hayaniyar dawowar Mai gidan harda jiniyar motocin ƴan sanda, da kyar na iya ta shi na fita ta baya don kwaso kayan Aarif dana wanke da safe, yayin da nike kwashe kayan naji wasu masu aiki mata suna gulma, duk dama ban damu na saurara ba amma kunne na ya jiyo min wasu abubuwa in da suke cewa,

"Wannan karan fa mai gidan da ƴar gaban goshin sa ya dawo"

Wata ta capke tana cewa "Wai wannan ƴar gaban goshin ta mance mijin ta ba shi da lafiya ne amma a ko da yaushe cikin tafiya ta keyi kasashe zuwa kasashe bata taɓa kula da shi ko da ta dawo ma bata wani kwana a ɗakin da yake kuma bata jimawa take komawa London"cewar ɗaya daga cikin masu gulman, yayin da wata ta sake cafkewa da cewa "To ai ni ina ganin kaman auran dama bai dame ta ba, su kuma masu gidan suna kallon abin da ta ke yi amma basa tsawatar mata, ni a yanda na ji ma yanzu ita ke kula da komai na harkokin kasuwancin Mai gidan dana Mijin na ta"

Buɗar bakin wata ta ce,"Ni fa na tsani wannan Shatou ne sunan ta ko Aisha, ba ta burge ni ko kaɗan, ga wulakanta ɗan adam, kwata kwata mu ma'aikata ba ma da daraja a idanunta"

Wata ta sake cafkewa da cewa "Hmm to bari kuji, ku shirya tsaf saboda wannan karan zata jima a garin sosai saboda na ji kishin kishin wai tana da juna biyu" cewar indo ɗaya daga cikin masu aikin kitchen (irin mikon kaza, ɗauko wan cen, da sauran su).

"Dallah ke indo wa ya faɗa miki, karyar banza, ke da iya kar ki miko wan cen, aje wannan, sai jera kayan abinci, A ina ki ka ji wannan labarin? Indo Ta ce,To in baku yadda ba shikenan ni kam nayi kitchen"

Dama ai a kitchen ɗin kikafi auki, cewar Shamsiyya ɗaya daga cikin masu wanke wanke.

Kunnuwa na sun gaji da jiye min gulmace gulmacen nasu hakan yasa bayan na gama linke kayan na yi hanyar ɗaki na ina tunani a cikin zuciya ta sosai ni ke mamaki in dai abin da suka faɗa gaskiya ne to ai ya kamata Mamie ta tsawatar mata ta zauna ta kula da mijinta, uhmmmm ni Ummi bari dai nayi shiru wannan ba hurumi na ba ne, da sauri na yi watsi da zan cen na su, na kama har kar gaba ta.

______________________________________
CIGABAN LABARI~ CONTINUATION

Kwana ki na ta tafiya, tsahon mako huɗu kenan mu na zaune a gidan Mamie ni da Aarif ɗina, ba na shiga sabgar kowa, aikin da ya kawo ni shi ni keyi, ba ruwa na da shige-shige a gidan Mamie, aikin asibtin ma na dena zuwa, Kullin aikin bangaren Mamie ni keyi, Sai dai a ɗan kwanakin da na yi bayan dawowar shatou, na fahimci surukar Mamie mai suna Shatou kamar yadda na ji masu aikin gidan su na faɗa,
Shatou na yawan samun saɓani da Mamie akan Ɗan Mamie mara lafiya.

UMMI KWARAS ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang