*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 20STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka__GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye______________________________________
LAGOSZaune ya ke saman ɗaya daga cikin fancy chair dake reception na hotel a cikin garin lagos, hannayen sa na rike da wata farar takarda.
Dafa kafaɗar sa da a kayi shi ya dawo da shi daga trance ɗin da ya shiga, ya sauke nannauyen ajiyar zuciya haɗe da sake kishingiɗa ya na kallon wanda ya dafa sa.
"Mike!!!
Mike Ya ce,"Umar what's happening ? Ka kira ni few minutes back, ka ce kana son gani na to gani na zo, faɗamun miye damuwar."
Umar yayi gyaran murya, Ya ce,"Mike an min transfer ne, and the worst part of it shine BAHCHI STATE aka kai ni. Kasan MD dama ya ce hotel ɗin sun buɗe new branch a Bauchi, to cikin wa'in da aka zaba dai ina ciki,in fact nine aka bama MD a wancen hotel ɗin"
Mike Ya ce,"Wow" Ina taya ka murna Umar saboda an kara maka matsayi, but problem din shine an tura ka gari mai nisa, ban san me yasa MD zai saka a ciki ba tare da tamabayar shawaran ka ba, Any way it's another experience, ko ba komai sabon waje zaka babu wan da ya san ka a garin, So I guess ba abin damuwa ba ne.
Umar ya ɗan harare sa na wasa sannan Ya ce,"Baka gane bane ni Lagos ɗin ne bana son na bari, Mike kar ka manta kai ka soma ɗaura ni a hanya, And nayi abin da har yau na kasa komawa Katsina state, kai ne ka bani shawaran na biyo ka Lagos, and yes na bi shawaran ka, ka samamun aiki babba, ka bani wajan kwana kuma duk ba dan bana da shi ba, sai dan abotan dake tsakanin mu, to ga shi yanzu MD ya tura ni, ni kaɗai Bauchi taya kake ganin zan soma wata rayuwar baka kusa dani?
Mike ya dafa kafaɗar sa Ya ce,"Look Umar idan bama gari ɗaya ba shi zai sanya alaqar mu ta yanke ba, zan cigaba da taimakon ka ko baka kusa dani, ni kawai ina so ka kwantar da hankalin ka babu abin da zai faru tun da ba Katsina bane Bauchi ne, kuma na san ku baku da kowa a Bauchi state"
Umar ya gyaɗa kai "Bamu da kowa gaskiya kawai dai su cen basa yin life kaman nan lagos kuma ni da ba dan gari ba zai yi wahala na saba da matan dake cen ka dai gane me nike nufi ai."
"Eh maganan ka akwai abin dubawa mutumina dama na san duk kwana kwanan at the end nan zaka bullu , so ka kwantar da hankalin ka mutumina,akwai wanda zan hada ka da shi, baka da matsala" Umar yayi dariya suka tafa hannu daga nan suka koma wata hirar daban.
Mike abokin Umar ne tun lokacin da su kayi bautar ƙasa su ka haɗu shakuwan su yasa Mike barin Lagos yazo ya zauna da Umar daga baya ne bayan ya tunzura Umar yayi ɓar na, sai Mike ya ɗauke shi suka koma lagos, zaman da su keyi a lagos zama ne na tir Allah wadai, basu ɗauki zina a bakin komai ba. Umar ya biye wa Mike ya koya masa halayen banza wannan kenan.
______________________________________
KATSINA STATE
KAUYEN GARIN GADOMutanen kauyen suna nan kamar dai jiya I yau babu cigaba a tare dasu, sai dai shekaru da suka dan ja,

VOUS LISEZ
UMMI KWARAS ✔
NouvellesLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...