*UMMI ƘWARAS*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
UMMI ƘWARAS
PG 10
STORY, WRITTEN BY FADILA IBRAHIM {dielaibrahim}
_SADAUKARWA_
Wannan littafi sadaukarwa ne ga family na Ibrahim's, Allah ya kara muku tsawon rai mai albarka_
_GARGAD'I_
Ban yarda wani/wata su canja min tsarin labari na ba sai da yarda ta, lallai ku sani aikata hakan babban laifi ne saboda haka a kiyaye_
_____________________________________
*UMMI ƘWARAS*
*RETURN*
*RIGHT FROM WHERE I STOP AT CHAPTER 9*
______________________________________
Suka hau mashin da kayayyakinsu ina ta kallon shi kamar yadda shi ma ya ke kallo na suka tafi ina ɗaga musu hannu sai da na dena hango mashinan nasu.
Baba na kallo na amma bai cemin komai ba suka juya suka barni awajan da kyar na iya ɗaga kafafuna na taka kamar bani da jini a jiki na koma inuwar da muke zama da ɗan guntun hawaye na wallahi"
Ranar dai anan inuwar mu na ƙarasa yini na da kayan makaranta ajiki na, duk da kuruciya na damu na amma na shiga wani yanayi mai wuyar fassarawa, ni Ummi taya zan soma wata rayuwar bayan na saba da rayuwar da mu kayi da *Ɗan binni* Sati biyun da mu kayi da shi shine yake ta yimin yawo a ƙwaƙwalwata.
Sai kusan magriba na koma gida da sanyin jiki na shiga gida haɗe da furta siririyar sallama wacce ta fito daga baki na, bama lalle kowa ya ji sallamar tawa ba, gidan tsit saboda kowa yana ɗaka yana sallah, na shiga ɗakin Mama wanda hasken aci bal bal shi ya karaɗe ɗakin ya kara yin ɗumi duk da na hango tukunyar gaushi agefe"don ɗabi'ar Mama ce ko ana sanyi ko ba'a sanyi sai ta sanya gaushi a ɗaka, a cewar ta wai yana kara lafiya.
"Mama na sallah ita da Mairo sai Mu'azzam dake ta faman wulla kafafu yana kuka a ɗauke shi"
Dama lafiya lafiya ni ba sallan ni keyi ba, balle yanzu da kewar Ɗan binni ya dame ni. Zuwa nayi na ɗauki mu'azzam ina ta faman jijjiga shi kafin su idar da salla, koda suka idar na ma kasa yi musu magana, duk dama naji suna hira don na sako baki amma ni abin bai dame ni ba, Mu'azzam kawai nike ta yiwa wasa kaɗan kaɗan na goye shi yayi bacci nima baccin na soma ji, amma jin ciki na na murɗa min alamar yunwa ce don rabo na da abinci tun ɗumamen tuwon da Mai dawa ta bani naci da safe shima loma biyu nayi na tashi na tafi makaranta" a hankali na kunce Mu'azzam na mikawa Mama sannan nayi mata ƙuri da idanu hakanan lokaci ɗaya ina mutsutsuke ciki da hannu na, cikin nawa ma kuka ya keyi amma atunani na Mama bata gane ba"
"Kallo ɗaya Mama tai min ta gane cewa yunwa ce ke addabata girgiza kai tayi cikin ranta tace na san dama za kiji yunwa Ummi ,Mama tayi mamaki jin duk yinin yau ban dawo gida cin abinci ba, sa'annan ban ambaci ina jin yunwa ba tun bayan dawowata, ni dama yunwar ciki na bai dameni ba indai ina yawo ko wajan wasa babu ruwana da abinci.
Mama ta ce Ummi yunwa halan kike ji? Nayi saurin gyaɗa kai na don Allah yaji ya kuma gani ba zan iya ɓoye mata ba tun da ta tambaye ni.
Mama ta ce,"Buɗe ga kwaryar fura cen a ƙuryar ɗaki kisha, ta ɗan dakata kaɗan tana kallon fuskata kafin ta cigaba da cewa "Tuwon masara miyar kuka akayi kuma na san ba ci ki keyi ba"
Na ɗan marairai ce fuska ina son yin shagwaɓa Mama ta ce,"To ai yanzu tun da ya tafi shikenan kuma jarabar ta dawo, yanzu za'a fara sauke min"
Duk da bani son yin dariya sai da Mama ta sani dariya saboda yadda tayi maganar,
Kuma gaskiyar Mama ne bana cin tuwon masara miyar kuka, na sunne kai kawai na wuce na ɗau kwaryar furar ina buɗewa ko naga yasha nonon kindirmon da Baba ya tatsa a jikin shanuwa jiya da daddare" ai kuwa na kafa kai sai da nasha mai isata kafin na sauke kwaryar na gyara mata zama na rufe sannan na soma kiciniyar canja kayan makaranta ta Allah yasa gobe asabar babu makaranta da ban san yadda zanyi ba"
Ina gamawa nayi kwanciya ta, Ina jin Mairo tana cewa Ummi taho muje dandali mana, amma nace mata A'a taje kawai ni bacci ni keji, Mairo ta tafi dandali abin ta.
KAMU SEDANG MEMBACA
UMMI KWARAS ✔
Cerita PendekLabari mai cike da ban dariya, nishadantarwa gami da fadakarwa, Labarin wata yarinya mai suna UMMI KWARAS, rayuwar Ummi abin dubawa ne,Rayuwarta cike yake da abubuwan ban mamaki da ban al'ajabi moreover Rayuwar ta tana cike da kaddara wacce tai mata...
