Bayan kowa ya waste da dare suka yi Shirin bacci, ya na dakin shi ya kira ta ita kuma suna parlour ita da Aee da Qawwama.
Ta mike ta shiga dakin tare da sallama a bakin ta ya amsa ta karaso tana ce wa "Habibi."
Ya ce "I get a gift to you."
Ta budai baki kafin ta ce "Da gaske, in gan shi."
Ya mika mata bangle din.
Ta amsa cike da farin ciki ta rike dan hannun sannna ta rungumai shi tana ce wa "Thank you habibi na godai sosai thank you so much."
Tayi kissing din shi sannan ta sake shi.
Ya rike hannun ta ya amsa bangels din ya sa mata shi.Ta ce "I like it I love you."
Ya ce 'Wannan shi ne gift din ki na haifar Afreen."Ta ce "Afreen kuma siyama dai."
Ya ce "Duk yada ki ka ce ni dai da afreen zan dinga kiranta. Ta na ina?
Ta ce tayi bacc
i.
Ya ce "Good yanzu kin ga muna da yara biyu."Ta ce "ذEh mana."
Ya ce "Amma ya kamta nima ki min aboki ."Ta dan yi dariya, ta gyara zaman ta a gadon ta na ce wa ay haihuwa ta Allah ce sannan shi ke ba bawan sa jinsa da ya ga dama.
Ya ce "Toh Allah ya bani namiji kin ga Asif yayi namiji yayi mace."
Ta ce "Allah bamu ma su Albarka."
Ya amsa da "Amin" Sannan ya kara da "Allah bar mu tare." Ya rungumaita ta amsa da Amin.Qawwama ta shigo ganin suna rungumai da juna ta turo baki ta ce "Ni kuma fah."
Halimatu ta janye Asim, Asim ya budai hanun shi alamar ta karaso. Ta ruga da gudu ta hayai shi tana rungumar shi. Ya ce Qawwama na dauka kin yi bacci.
Ta ce "No, Abi yace daga yau suna na Yaaya."Asim ya ce "Toh Yaaya babba."
Ta ce "Abi yau ma a nan zan kwana ba wurin Ammi ba."Ya dubi Halimatu kafin ya tambayi Qawwama miyasa?
Ta rada mashi abu a kunnen. Asim yayi dry itama tayi dry. Halimatu ta mike ta ce "Ku dai ku ka sani.
Suka yi dry ta fice.Bayan fitar ta Asim yace yanzu zan kwanta je kiyi fitsari ki zo mu kwnata.
Ta amsa mashi da toh sannan ta sauka ta shiga toilet shi kuma ya kakkafe masu gadon. Bayan ta fito ya kashe fitila suka koma gado suka kwanta.
Ta na rungumai da shi ta ce "Abi wai miyasa Ammi ta fiye zafin rai sai ta ta min shouting kai kuma ba ka min koh."
Ya ce "Ay ke ce baki jin mgn."
Ta ce "Ina ji."Ya ce "Toh ki zama good girl zata dai na maki fada."
Ta ce "Abi bani tatsunniya irin na jiya."
Nan ya fara bata tatsuniya har tayi bacci ya masu addua’a ya kwanta.A bangaren Halimatu ta na fitowa ta ce wa Asee ta shigo da siyama.
Asee ta dauki siyama da ke kwnace saman kujera ta shiga da ita daki ta kwantar da ita a kan gado.
Halimatu ta mika mata dan hannun.
Asee ta amsa tana tambayar "Na ki ne?Halimatu ta daga mata kai kafin ta ce "Yanzu baban su ya bani."
Asee ta dan wara ido tana cewa "AI na san ki, gold ne fah?
Halimatu ta ce "Eh mana."
Asee ta ce "Na taya ki murna nima ki taya ni addu’a in samu irin shi a a matsayin miji."
Halimatu ta ce "Amin, Allah baki na gari ke ma."
Ta amsa da "Amin." Ta hau gadon tana ce wa "Yanzu kun shirya ko?
Ta ce "Eh tin da na haihu komi ya wuce, nima laifi nane na san yana san yara na sa planning amma yanzu ba zan kara sawa ba."
Asee ta ce "Gaskiya kam, amma kin san abinda ke birgeni da shi ko da baku shiri bai nunawa kowa nima dan ina nan zaune."
YOU ARE READING
Halimatus'sadiyah
RomanceLove, crises & hated Ingenous/Naive Halima facing challenges from her in laws being a house maid married into royals family😍😍 HALIMATUS'SADIYAH Hausa novel