Chapter 64

4 2 0
                                    

Har a ka sha ruwa Qawwama bata saki ba. Asim ya tambayi Asee mi halimatu ta mata.

Asee ta dubi halimatu kafin ta dubi Asim ta ce "Laifi ta mata ta duke ta."

Asim ya dubi Halimatu ya ce "Ni na sani haka nan princess di na ba zata yi silent ba."

Ya koma kusa da Qawwama yace zan ra ma maki. Maza ki ci abincin.
A hankali ta ce "Na koshi."

Halimatu ta ce "Ba zaki ci ba ki ka sa a ka zuba maki."

Asim ya ce "Dan allah ya isa haka." Ya dauki awarar ya kai mata a baki.
Ta girgiza mashi kai.

Ya dauki plate din ya dauki Qawwama ya wuce dakin shi.

Suna shiga Asee ta ce "Gaskiya kina takurawa Qawwama gashi kuma halin ku daya."

Halimatu ta Harare ta kafin ta ce "Ban gane ba?

Ta ce "Kin manta idan Umma ta maki fada kin dinga fushi da kowa."

Tayi murmishi ta ce "Ni daban ita daban in ban yi da gaske ba zai sangarta ta ne."
Asee ta ce "Yanzu in ta fadi mahsi abin da tayi."

Halimatu ta ce "Ba zata fadi mashi ba."

A daki Asim yayi yayi Qawwama ta fada mashi mi tayi ta ki fadi mi shi sai ma kukan da ta ke a hankali wanda hakan ya bata mashi rai. Da kar ya samu ya lallashe ta ta ci abici. Karshe ma bacci tayi a dakin.

Ko da zai fita sallah ya ce kar ta tada ta.
Bayan ya dawo yace ta samai shi a daki.
Ya na shiga ba jimawa ta shigo.

Rai bace ya tambaye ta "Mi tayi ki ka duke ta."

Halimatu tayi murmishi kafin ta ce "Sbd haka ka bata rai."

A hassale ya ce "Tambayar ki na ke, wai ke wacce irin uwa ce ki dinga sawa yarinyar ki tsoro, baki san duka lalalta yaro yake ba."

Halimatu ta ce "Sai kuma na bar yarinya ta dinga yin abin da ta ga dama icce tin yana karami ake dankwafar da shi ba wai sai ya girma ba."

Ya ce "Mi ta maki? Duk abin da tayi ba zaki iya mata fada ba. Toh bari ki ji tin da na maki mgn kin ki ji daga yau ki ka kara dukan ta Allah sai ranki ya baci."

Ta ce "Ka saurare ni ka ji miya faru?

Ya zauan kan gado ya ce "Duk abin da tayi bai kai na ki duke ta ba."

Ta zauna saman gadon ta ce "Fada min  da cewa ne ta dinga rungumai namiji duk namijin da ya zo sai ta rungumai shi wannan tarbiya ce?
Na mata mgn na mata fadan ta ki ji dole na duke ta na san yanzu ba zata kara ba.

Asim ya ce "Ohh shiyasa yau ta ki min welcoming hug din da ta ke min in na dawo."

Ta ce "Azizi ba zai yu ba dukkan mu mu yi sanya a kan su dole in wani yayi zafi wani yayi sanyi."

Ya ce "Na ji amma duk abin da zata yi kar ki kara dukan ta."

Ta amsa shi da toh wadda kullun da haka ta ke bin shi.

Ya mike ya koma wurin Qwwama yana ce wa dauko mata kayan baccin ta.

Halimatu ta mike ta fita ta koma dayan dakin ta dauko mata rigar baccin ta ta dawo ta sa mata shi kuma yana lissafin kayan shagon sa. Ta gama sama ta ta fice.

Tin da ga ranar duk namijin da ya zo gidan ko da ta san shi sosai, iya kar ta da shi gaisuwa.

Tin da a ka yi suna komi ya dawo daidai tsakanin halimatu da Asim. Asee ta cigaba da zama a gidan har sai da akayi sallah da kwana uku sanann ta koma gida halimatu ta cigaba da hidimar gidan ta.

*****

Da dare Asim ya samu Alh inuwa a parlourn shi yana mamakin kiran da ya masa. Yayi sallama ya shigo ya gaishe shi kafin ya zauna.

Halimatus'sadiyah Where stories live. Discover now