02

862 54 12
                                    

*MAI HAK'URI*
(Shi ke da riba)

_Na_

*Rahma Kabir✍🏾*

_Page_ *2.*

Ido ya zaro waje yana mamakin k'arfin hali irin na Hajiya Laila, shafe kumatunsa yayi sai yayi yunkurin mik'ewa, sai ta matsa tana hararansa, ko kallonta bai kuma yi ba ya wuce ya bud'e k'ofa ya fice ransa nayi masa suya. Hajiya Laila ta dafe kanta tana zubarda wasu hawaye masu zafi, wayarta ta jawo ta kira wayar k'awarta Hajiya Salma, bugu biyu ta d'aga cikin kuka Laila tace

"Kawata wallahi Yaron nan yana son sanya min hawan jini yak'i yarda da k'udurina"

Hajiya Salma tace
"Haba Laila karki bani kunya mana akan wannan k'aramin Alhakin kike zubda hawaye, Maza nawa kika juya k'arshe kika barsu, sai wannan ne zai baki wuya bacin wasu dabaru ma a wurinki na koya, dan Allah ki dawo cikin hayyacinki ki d'auki mataki kawai"

Cikin shasshek'an kuka tace
"Wallahi Salma ina Sonsa sosai wanda ban tab'a yiwa wani d'an Adam ba, ke kanki da kika fara ganinsa kin yaba dashi, pls kizo ki bani shawara yanda zan shawo Kansa ni wlh burina kawai in had'a shinfid'a dashi ko zan samu kwanciyar hankali, ni Alhaji hoto ne a guma kud'insa yasa nake zaune dashi"

Cikin murmushi Salma tace
"Hajiya Laila kenan wani lokacin kina Abu kamar wata k'aramar Yarinya, ai auren Alhaji wani rufin asiri ne a gunki dan zaki rik'a tsula ciyarki ba tare da wata damuwa ba, sannan ma ai Alhajin bamai zama bane sai yayi wata bai gari"

"Kwarai kuwa, shiyasa nake son amfani da wannan damar dan in ja zuciyar Jalal mu rik'a rayuwa ba tare da kowa ya kawo wani zargi ba"

"To K'awata karki damu zanzo zuwa anjima akwai shawaran da zan baki" Da wannan maganar ne suka yi sallama suka aje wayar.

Yaya Amir ya bar Asibiti ya tafi police station, ya musu dukkan bayanin abinda ya faru, nan take ASP Jafar da muk'arrabansa suka d'unguma zuwa gidan Alhaji Sani Buba.

Suna shiga Unguwar jiniyar motansu ke tashi, Mutanan dake hada-hada domin fita aiki da Yara masu zuwa makaranta sai abin ya zame musu abin mamaki ganin motocin 'Yan Sanda da sassafe, k'ofar gidan Mai Gadi ya wangale suka shiga tare da yin parking, suka fito gaba d'aya kusan su takwas, ko wanna da bindiga a hanninsa, ASP ne kawai babu a hannunsa, cikin falon suka shiga direct d'akin Jannat suka shiga, sun sameta ta rakub'e a gefen bango jikinta na kakkarwar sanyi, idon nan nata ya kod'e saboda azabar kuka da tasha, d'aya daga cikin 'Yan Sandan Mace ta daka mata tsawa ta mik'e jiki na rawa, Istigafari take ambato a zuciyarta, domin yau tasan Rayuwarta ya gama amfani a Duniya, burinta mutuwa ta d'auketa cikin salama taje ta iske abin da ta aikata.

Hotuna sukaita d'auka da inda jinin Abba ya zuba, da inda ta jefar da wukan tare da Hoton hannunta, ASP Jafar ya ciro hankacif ya d'auka wuk'ar aka d'auka hoton wuk'ar, 'Yar Sandar ta sanyawa Jannat Ankwa a hannu ta tasa k'eyarta tace
"Mu tafi munafuka kamar mutumiyar kirki"

Haka suka ratsa falon Ma'aikatan gidan suna kuka, Jannat ta tsaya ta juyo tana bin cikin falon da kallo har takai kallonta kan Family pictures d'insu, ta kurawa hoton ido a sannane hawaye mai rad'ad'i ya sauka a kuncinta, taja majinan hancinta, saita maida kallonta gun Ma'aikatan gidan su uku, Baba Inde, Indo, Tabawa, hannunta ta had'a biyu ta nuna musu alaman su yafe nata, kana ta cigaba da tafiya a hankali kamar wanda kwai ya fashe mata a ciki.

Sun fito haraban Gidan, Mak'ocinsu Alhaji Ahmad Abokin Abba ya shigo gidan cikin sauri, "Subhanallahi" yake fad'a ya kalli Amir yace
"Amir me zan gani haka? meye yake faruwa?"

Cikin damuwa Yaya Amir ya labarta masa komai, tsananin tashin hankali Alhaji Ahmad ya shiga ya matsa gaban Jannat ya d'ago hab'arta, sai ta rufe ido domin tana kunyar had'a ido dashi, yace

MAI HAKURI (shi ke da riba)Where stories live. Discover now