*MAI HAK'URI😰*
(Shi ke da riba)_Na_
*Rahma Kabir✍🏾*
_Page_ *19.*
Suna tafe a hanya Jannat take bashi labarin su Amir, jinjina kai Jalal yayi yace
"Iyen ba kaga 'yar gatan Samari Uku, wato har su duka suka zo duba ki gaskiya kinji dad'inki"D'aure fuska tayi tace
"Nifa ba saurayi na a cikinsu kawai dai na gaya maka ne ko zaka gane meye manufar Brr Junaid dan ban gane maganarsa ba, gwara Yaya Amir nasan shi ya jima yana soma tun ina gida, Yaya Zaid kuma a matsayin k'anwa ya d'aukeni"Dariya sosai Jalal yayi yace
"Little Jan shagwab'ar nan tana k'ara miki kyau in kina yi, to yi hak'uri nima da wasa nayi miki"Ya kuma kira sunan ta "Lil Jan" cikin serious, ta d'ago kai suka had'a ido sun kai kusan minti d'aya a haka kafin yace
"Kinga Amir d'an Uwanki ne kuma yana sonki sosai a yanayin kalamansa, sannan Zaid yana matuk'ar tausayinki hakan yasa ya danne son da yake miki bai bud'e miki zuciyarsa ba saboda ya duba halin da kike ciki, shiyasa ya adana maganar sa sai nan gaba k'ila ya sanar miki, Brr Junaid kuwa ya gaya miki ma kai tsaye sonki yake yi, dan haka gaba d'ayan su suna sonki ne, yanzu ke ce za ki natsu da zuciyarki ki zab'i wanda ya fi kwanta miki a rai".
D'ago kai tayi cikin shagwab'a tace
"Ya Jalal ni zab'ina yana gun Allah Kuma karatu nake so nayi ba ruwana da soyayya, a halin da nake ciki yanzu Yaya Jalal in nace zan sa son wani a raina a kai ma saika min fad'a, da azabar gidan nan zanji koda wahalar soyayya, a wautana a da nake ganin kamar ina son Yaya Amir sai daga baya na gane kawai shak'uwa ce yasa nake jin haka, kuma ni yanzu bazan iya Aurensa ba saboda Abba, shi kuma Zaid na d'auke shi D'an Uwana na jini bazan iya soyayya dashi ba, amma Brri Judaid..."Sai Jalal yayi saurin katseta da cewa
"Shine kike so ko? Dan kalamansa abin dubawa ne"Duka ta kai masa na wasa sai ya goce yana dariya tace
"Nifa bance haka ba"Jalal Yace
"Ke kinga zomu tafi kafin a kama mu anan dan inna biyewa shirmanki zamu iya kwana anan"Tayi masa hararan wasa tace
"To in hakan ya kama mu kwana saimu kwana d'in, ai ni zanfi son haka muna tare dan ba zaka bar wani abu ya cutar dani ba koda kwaro ne""Rufamin asirin kafin kisa Brr Junaid ya d'aure ni"
Duka ta kai masa sai ya matsa da sauri yana tafiya yana dariya, bin bayansa tayi tana shagwab'a
"Allah Yaya Jalal ka bari za muyi fad'a fa"
"To na bari yi hak'uri My Little Jan kema kinsan wasa nake miki, yanzu dai muje ki shiga part d'in ku Nima na tafi, sai da safe Masoyiyar Barrister ko nace mai farin Jinin samari Uku" yana gama fad'a ya tafi da sauri yana murmushi.
Tsayawa tayi tana kallon sa tare da yin kwafa tace
"Zan rama ne tunda mun fara 'yar haka da kai"Juyowa yayi ya mata gwalo yana murmushi, itama murmushi kawai tayi ta shige part d'in su dai-dai lokacin da aka soma koro sauran Mutanan.
Jannat kwance take bisa gadonta tana tunanin abinda ya faru d'azun, zantukan Brr Junaid ne nake ta mata yawo a zuciya, hakanan ta tsinci kanta tana murmushi, a iya saninta bata tab'a jin wannan yanayin ba ga wani D'a Namiji, saita taji ya burgeta, Salonsa a yanda yazo ya bayyana mata sirrin zuciyarsa ya kwanta mata a rai, tunowa tayi da ranar da ya bayyana a kotu yace zai tsaya mata a matsayin lauyanta jaruntarsa ya kayatar da ita, sai ta mirgina tayi kwanciyar rigingine kanta na kallon sama, tsokanar da Yaya Jalal yayi mata shine ya fad'o mata a rai sai tayi murmushi tace a ranta
'Ohhh ko me Yaya Jalal ya gani har yake zargin ina son Brr Junaid oho, ni yanzu bata soyayya nake ba, kawai dai Brr Junaid yana burgeni saboda Jarumtarsa'
YOU ARE READING
MAI HAKURI (shi ke da riba)
RomanceD'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba t...